Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 On the third day, a wedding took place in Cana of Galilee; Jesus's mother was there. A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can,
2 Jesus and his disciples were also invited to the wedding. aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren.
3 When the wine ran out, the mother of Jesus said to him, "They have no wine." Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”
4 "Woman, why are you bringing me into this?" Jesus replied. "My hour has not yet come." Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.”
5 His mother said to the servants, "Do whatever he tells you." Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.”
6 Six stone water jars stood there, used for Jewish purification, each holding twenty to thirty gallons. Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.
7 Jesus said to them, "Fill the jars with water," so they filled them to the brim. Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.
8 He told them, "Draw some out now, and take it to the head steward." So they did. Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.” Suka yi haka.
9 The master of the banquet tasted the water now wine, not knowing its source—though the servants who drew it knew. So he called the bridegroom aside, Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya
10 and said, "Everyone serves the good wine first, then the lesser once guests are drunk. But you've kept the good wine till now." ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”
11 Jesus performed this first sign at Cana in Galilee. He revealed his glory, and his disciples believed in him. Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.
12 After this he went down to Capernaum with his mother, brothers, and disciples, and stayed there a few days. Bayan wannan sai ya tafi Kafarnahum tare da mahaifiyarsa da ’yan’uwansa da kuma almajiransa. A can suka zauna ’yan kwanaki.
13 When the Jewish Passover was near, Jesus went up to Jerusalem. Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima.
14 In the temple courts he found sellers of cattle, sheep, and doves, and others sitting at tables exchanging money. A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi.
15 He made a whip of cords and drove them all out of the temple courts, sheep and cattle alike, poured out the money-changers' coins, and overturned their tables. Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu.
16 To the dove sellers he said, "Take these out of here! Don't make my Father's house a marketplace." Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!”
17 His disciples remembered that it is written: "Zeal for your house will consume me." Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.”
18 So the Jews asked, "What sign will you show us for doing these things?" Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?”
19 Jesus answered them, "Destroy this temple, and in three days I will raise it up." Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”
20 They replied, "This temple took forty-six years to build, and will you raise it in three days?" Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?”
21 But the temple he had spoken of was his body. Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne.
22 After he rose from the dead, his disciples remembered he had said this, and believed the Scripture and the word Jesus had spoken. Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.
23 While he was in Jerusalem at the Passover, many saw the signs he did and trusted in his name. To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa.
24 But Jesus would not entrust himself to them, for he knew all people. Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane.
25 He didn't need anyone's testimony about people—he knew what was in each one. Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]