Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Genesis 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 So the heavens and the earth were completed in all their vast array. Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.
2 By the seventh day our Father had completed his work, and he rested on the seventh day from everything he had made. Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa.
3 And our Father blessed the seventh day, making it holy, because on it he rested from all the work of creation he had done. Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
4 This is the history of the heavens and the earth when they were created, when our Father made earth and heavens. Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su. Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai,
5 No shrub of the field yet existed on the earth, no plant of the field had yet sprouted, for our Father had not sent rain on the earth, and there was no man to work the ground, babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar,
6 but springs came up from the earth and watered the whole surface of the ground. amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa.
7 Then our Father formed the man from dust of the ground, breathed into his nostrils the breath of life, and the man became a living person. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
8 Then our Father planted a garden in Eden, in the east, and put there the man he had formed. To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi.
9 From the ground our Father grew every tree lovely to see and good to eat, with the tree of life in the garden's center and the tree of knowing good and evil. Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.
10 A river flowed from Eden to water the garden; from there it divided into four rivers. Akwai wani kogi mai ba da ruwa ga lambun wanda ya gangaro daga Eden, daga nan ya rarrabu, ya zama koguna huɗu.
11 The first is named Pishon; it flows around all the land of Havilah, where gold is found. Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.
12 The gold of that land is good; aromatic resin and onyx are also there. (Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.)
13 The name of the second river is the Gihon; it winds through the entire land of Cush. Sunan kogi na biyu, Gihon. Shi ne ya malala kewaye da ƙasar Kush.
14 The third river's name is Tigris, flowing east of Assyria. The fourth river is the Euphrates. Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites.
15 Our Father took the man and set him in the garden of Eden to work it and guard it. Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.
16 And our Father commanded the man, "You are free to eat from any tree in the garden; Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun,
17 but you must not eat from the tree of knowledge of good and evil, for you will surely die the day you eat from it." amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”
18 Then our Father said, "It is not good for the man to be alone. I will make a helper matching him." Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
19 From the ground our Father formed every field animal and every sky bird, then brought each to the man to see what he'd name it. Whatever the man named each living creature, that was its name. To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan.
20 The man named all livestock, birds of the sky, and all wild animals, but for Adam no helper matching him was found. Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye. Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba.
21 So our Father made the man fall into a deep sleep, and while he slept, took one of his ribs and closed the flesh over it. Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama.
22 Then our Father built a woman from the rib he took from the man, and brought her to the man. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
23 The man said, "At last! This is bone of my bones and flesh of my flesh; she will be called 'woman,' for she was taken out of man." Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”
24 So a man leaves his father and mother, joins his wife, and they become one flesh. Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.
25 The man and his wife were both naked, and they were not ashamed. Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]