Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Genesis 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In the beginning, our Heavenly Father created the heavens and the earth. A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa.
2 The earth was formless and empty; darkness lay over the deep's surface, and the Spirit of our Father was hovering over the waters' surface. To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
3 Then our Father said, "Let there be light," and there was light. Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske.
4 He saw that the light was good, and he separated the light from the darkness. Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu.
5 He called the light "day" and called the darkness "night." There was evening, and there was morning—the first day. Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.
6 And our Father said, "Let there be an expanse between the waters to separate water from water." Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.”
7 He made the expanse and separated the water under it from the water above it. And it was so. Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance.
8 He called the expanse "sky." So there was evening, and there was morning—the second day. Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.
9 Then our Father said, "Let the water under the sky be gathered to one place, and let dry ground appear." And it was so. Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance.
10 He named the dry ground "land," the gathered waters "seas." And he saw it was good. Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
11 Then he said, "Let the land grow vegetation: seed-bearing plants, fruit trees bearing fruit with seed in it, after its kind." And it was so. Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.
12 The land produced vegetation—seed-bearing plants by kind, and trees bearing seed-bearing fruit by kind—and our Father saw that it was good. Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau.
13 And there was evening, and there was morning—the third day. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.
14 And our Father said, "Let there be lights in the sky's expanse to separate day from night, and serve as signs to mark seasons, days, and years, Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru,
15 and let them be lights in the sky's expanse, to give light on the earth." And it was so. bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance.
16 Our Father made two great lights—the greater light to rule the day, the lesser light to rule the night. He also made the stars. Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari.
17 He set them in the expanse of the sky to give light on the earth, Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya,
18 to rule the day and the night, and to separate light from darkness. He saw it was good. su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
19 So there was evening, and there was morning—the fourth day. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.
20 Then our Father said, "Let the water swarm with living creatures, and let birds fly above the earth, across the sky's expanse." Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.”
21 So he created the great sea creatures, every living creature that moves and swarms in the water by its kind, and every winged bird by its kind. And he saw it was good. Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
22 Our Father blessed them and said, "Be fruitful, multiply, fill the waters in the seas, and let birds multiply on earth." Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.”
23 And there was evening, and there was morning—the fifth day. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.
24 And our Father said, "Let the land produce living creatures by kind: livestock, crawling creatures, and wild animals, each by kind." And it was so. Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance.
25 He made wild animals by their kind, livestock by their kind, and every creature crawling the ground by its kind. And he saw that it was good. Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
26 Then our Father said, "Let us make humanity in our image, in our likeness, to rule the fish of the sea, the birds of the sky, the livestock, all the earth, and every creature crawling on the ground." Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”
27 So our Father created humanity in his own image; in the image of God he created them; male and female he created them. Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su.
28 Our Father blessed them and said to them, "Be fruitful, multiply, fill the earth and subdue it. Rule the fish of the sea, the birds of the sky, and every living creature that moves on the earth." Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”
29 Then he said, "I give you every seed-bearing plant across the whole earth, and every tree with seed-bearing fruit—they will be your food. Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku.
30 To every animal of the earth, every bird of the sky, everything crawling on the ground with breath of life, I give every green plant for food." And so it happened. Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.
31 Our Father saw all he had made, and it was very good. So there was evening, and there was morning—the sixth day. Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]