Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Genesis 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The serpent was shrewder than any field animal our Father had made. He asked the woman, "Did God really say, 'You must not eat from any tree in the garden'?" To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
2 The woman said to the serpent, "We may eat the fruit from the trees in the garden, Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun,
3 but God said, 'Don't eat the tree's fruit in the garden's middle, or touch it, or you'll die.'" amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”
4 But the serpent said to the woman, "You will certainly not die. Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba.
5 God knows that when you eat from it, your eyes will open and you'll be like God, knowing good and evil." Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”
6 The woman saw the tree was good for food, delightful to the eyes, and desirable for wisdom. She took its fruit, ate, gave some to her husband with her, and he ate. Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.
7 Then the eyes of both of them were opened, and they knew they were naked; they sewed fig leaves together and made themselves coverings. Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.
8 They heard the sound of our Father walking in the garden in the cool of the day, and the man and his wife hid from his presence among the garden's trees. Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.
9 But our Father called to the man and said to him, "Where are you?" Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
10 The man said, "I heard you in the garden and was afraid, for I was naked, so I hid." Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”
11 Our Father said, "Who told you you're naked? Did you eat from the tree I forbade you to eat from?" Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
12 The man said, "The woman you put with me gave me fruit from the tree, and I ate." Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”
13 Then our Father asked the woman, "What have you done?" She said, "The serpent deceived me, and I ate." Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
14 So our Father said to the serpent, "Because you have done this, cursed are you above all livestock and above all wild animals; on your belly you will go, and dust you will eat all the days of your life. Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.
15 And I will put enmity between you and the woman, and between your offspring and her offspring; he will crush your head, and you will strike his heel." Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
16 To the woman he said, "I will greatly increase your pain in childbirth; in pain you will give birth to children. Your desire will be for your husband, and he will rule over you." Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.”
17 And to Adam he said, "Because you listened to your wife and ate from the tree that I commanded you, saying, 'You must not eat from it,' cursed is the ground because of you; through painful toil you will eat from it all the days of your life. Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
18 It will produce thorns and thistles for you, and you will eat the plants of the field. Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona.
19 By the sweat of your brow you will eat your bread until you return to the ground, since from it you were taken; for dust you are, and to dust you will return." Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.”
20 The man named his wife Eve, because she would become the mother of all the living. Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.
21 Our Father made garments of skin for Adam and his wife, and he clothed them. Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura.
22 Then our Father said, "Look, the man has become like one of us, knowing good and evil. Now, so he doesn't reach out, take from the tree of life too, eat, and live forever…" Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.”
23 So our Father sent him out of the garden of Eden to work the ground he was taken from. Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi.
24 He drove out the man and placed cherubim and a whirling, flaming sword east of Eden's garden, guarding the way to the tree of life. Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]