Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Acts 9 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 But Saul, still breathing threats and murder against the Lord's disciples, went to the high priest, Ana cikin haka, Shawulu ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist
2 and asked him for letters to Damascus's synagogues, so that if he found any of the Way, men or women, he could bring them bound to Jerusalem. ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majami’un Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yă kama su a matsayin ’yan kurkuku yă kai Urushalima.
3 As he traveled and was approaching Damascus, suddenly a light from heaven flashed around him. Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.
4 He fell to the ground and heard a voice saying, "Saul, Saul, why are you persecuting me?" Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”
5 He said, "Who are you, Lord?" And he said, "I am Jesus, whom you are persecuting. Shawulu ya yi tambaya ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.
6 But rise and enter the city, and you will be told what you must do." Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”
7 The men traveling with him stood speechless, hearing the voice but seeing no one. Mutanen da suke tafiya tare da Shawulu suka rasa bakin magana; sun ji muryar amma ba su ga kowa ba.
8 Saul got up from the ground, but with eyes open he saw nothing; they led him by the hand and brought him into Damascus. Shawulu ya tashi daga ƙasa, amma sa’ad da ya buɗe idanunsa bai iya ganin wani abu ba. Saboda haka aka kama hannunsa aka yi masa jagora zuwa cikin Damaskus.
9 He was blind for three days and neither ate nor drank. Kwana uku yana a makance, bai ci ba bai kuma sha kome ba.
10 A disciple named Ananias lived in Damascus. In a vision the Lord said, "Ananias." He answered, "Here I am, Lord." A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”
11 The Lord said to him, "Get up, go to the street called Straight, and look in Judas's house for a man from Tarsus named Saul—he is praying, Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a.
12 and in a vision has seen a man named Ananias come in and place his hands on him so he may see again." Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don yă sāke samun ganin gari.”
13 Ananias replied, "Lord, many have told me about this man—the harm he's done your holy ones in Jerusalem. Ananiyas ya amsa ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.
14 And here he has authority from the chief priests to bind all who call on your name." Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don yă kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.”
15 But the Lord said to him, "Go, for this man is my chosen instrument to carry my name before nations, kings, and Israel's people. Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don yă kai sunana a gaban Al’ummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Isra’ila.
16 For I will show him how much he must suffer for the sake of my name." Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”
17 Ananias went and entered the house. He laid hands on Saul and said, "Brother Saul, the Lord Jesus—who appeared to you on the road you traveled—sent me so you may see again and be filled with the Holy Spirit." Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”
18 Immediately something like scales fell from his eyes, and he could see again. He got up and was baptized, Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawulu, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma,
19 and after eating, he regained his strength. For some days he was with the disciples in Damascus, bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi. Shawulu ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus.
20 and immediately he began proclaiming Jesus in the synagogues, that he is the Son of our Father. Nan take ya fara wa’azi cikin majami’u cewa Yesu Ɗan Allah ne.
21 All who heard were amazed and said, "Isn't this the man who caused such havoc in Jerusalem among those calling on this name? And hasn't he come here for this: to bring them bound before the chief priests?" Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki suka ce, “Ba shi ne mutumin da ya tā-da-na-zaune-tsaye a kan masu kira bisa ga wannan sunan a Urushalima ba? Ba ya zo nan ne don yă kai su a matsayin ’yan kurkuku ga manyan firistoci ba?”
22 But Saul grew stronger still, bewildering the Jews living in Damascus by proving this one is the Christ. Duk da haka Shawulu ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi.
23 After many days had passed, the Jews plotted to kill him, Bayan kwanaki masu yawa, sai Yahudawa suka haɗa baki su kashe shi,
24 but Saul learned of their plot; they watched the gates day and night to kill him, amma Shawulu ya sami labarin shirinsu. Dare da rana suka yi fakonsa a ƙofofin birnin don su kashe shi.
25 but at night his disciples lowered him through the wall in a basket. Amma almajiransa suka ɗauke shi da dare suka saukar da shi a cikin kwando ta taga a katanga.
26 Arriving in Jerusalem, he tried to join the disciples, but all feared him, not believing he was a disciple. Da ya zo Urushalima, ya yi ƙoƙarin shiga cikin almajiran amma dukansu suka ji tsoronsa, ba su gaskata cewa tabbatacce shi almajiri ba ne.
27 But Barnabas took him to the apostles and explained how Saul had seen the Lord on the road, who spoke to him, and how in Damascus he had spoken boldly in Jesus' name. Amma Barnabas ya ɗauke shi ya kawo shi wurin manzanni. Ya gaya musu yadda Shawulu a kan hanyarsa ya ga Ubangiji kuma cewa Ubangiji ya yi magana da shi, da yadda a Damaskus ya yi wa’azi ba tsoro a cikin sunan Yesu.
28 So he was with them, moving freely about Jerusalem, speaking boldly in the name of the Lord. Saboda haka Shawulu ya zauna tare da su yana kai da kawowa a sake a cikin Urushalima, yana magana gabagadi a cikin sunan Ubangiji.
29 He spoke and debated with the Hellenists, but they were seeking to kill him. Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Hellenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi.
30 When the brothers learned this, they brought him down to Caesarea and sent him off to Tarsus. Sa’ad da ’yan’uwa suka sami labarin wannan, sai suka ɗauke shi zuwa Kaisariya suka aika da shi Tarshish.
31 So the church throughout Judea, Galilee, and Samaria had peace and was strengthened; walking in the fear of the Lord and comforted by the Holy Spirit, it multiplied in number. Sa’an nan ikkilisiya ko’ina a Yahudiya, Galili da kuma Samariya ta sami salama. Ta yi ƙarfi; ta kuma ƙarfafa ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ta ƙaru sosai tana rayuwa cikin tsoron Ubangiji.
32 As Peter traveled among all the believers, he also went down to the holy ones living in Lydda. Da Bitrus yake zazzaga ƙasar, sai ya je ya ziyarci tsarkakan da suke a Lidda.
33 There he found a man named Aeneas, bedridden for eight years, who was paralyzed. A can ya tarar da wani mutum mai suna Eniyas, shanyayye wanda yake kwance kan gado shekara takwas.
34 Peter said to him, "Aeneas, Jesus Christ heals you. Get up, make your bed." He got up at once. Sai Bitrus ya ce masa, “Eniyas, Yesu Kiristi ya warkar da kai. Tashi ka naɗe tabarmarka.” Nan da nan Eniyas ya tashi.
35 And all who lived in Lydda and Sharon saw him, and they turned to the Lord. Duk waɗanda suke zama a Lidda da Sharon suka gan shi suka kuma juyo ga Ubangiji.
36 In Joppa lived a disciple named Tabitha, meaning Dorcas. She was full of good works and help for the poor. A Yoffa akwai wata almajira mai suna Tabita (a harshen Girik sunanta shi ne Dokas); ita mai aikin alheri ce kullum, tana kuma taimakon matalauta.
37 In those days she got sick and died; they washed her and laid her in an upstairs room. A lokacin nan ta yi rashin lafiya ta mutu, aka kuma yi wa gawarta wanka aka ajiye a wani ɗaki a gidan sama.
38 Since Lydda was near Joppa, disciples who heard Peter was there sent two men to him, urging, "Don't delay coming to us." Lidda yana kusa da Yoffa; saboda haka sa’ad da almajirai suka ji cewa Bitrus yana a Lidda, sai suka aiki mutum biyu wurinsa su roƙe shi cewa, “In ka yarda ka zo nan da nan!”
39 So Peter got up and went with them. When he arrived, they brought him to the upper room. All the widows stood beside him crying, showing the tunics and cloaks Dorcas had made while with them. Sai Bitrus ya tafi tare da su, sa’ad da ya iso sai aka kai shi ɗakin saman. Duka gwauraye suka tsaya kewaye da shi, suna kuka suna nunnuna masa riguna da kuma waɗansu tufafin da Dokas ta yi yayinda take tare da su.
40 Peter sent everyone out, knelt, and prayed. Turning to the body, he said, "Tabitha, get up." She opened her eyes, saw Peter, and sat up. Bitrus ya fitar da su duka daga ɗakin; sa’an nan ya durƙusa ya yi addu’a. Da ya juya wajen matacciyar, sai ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe idanunta, ta ga Bitrus sai ta tashi zaune.
41 Giving her his hand, he raised her up. Calling the holy ones and the widows, he presented her alive. Ya kama ta a hannu ya taimake ta ta tsaya a ƙafafunta. Sa’an nan ya kira masu bi da kuma gwaurayen ya miƙa musu ita da rai.
42 And it became known throughout all Joppa, and many believed in the Lord. Wannan ya zama sananne ko’ina a Yoffa, mutane da yawa kuma suka gaskata da Ubangiji.
43 And he stayed in Joppa for many days with a man named Simon, a tanner. Bitrus ya zauna a Yoffa na ɗan lokaci tare da wani mai aikin fatu mai suna Siman.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]