Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Acts 8 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Saul approved of Stephen's killing. That day a great persecution erupted against the Jerusalem church, scattering everyone except the apostles through Judea and Samaria. Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.
2 Devout men buried Stephen and mourned loudly over him. Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.
3 But Saul was destroying the church, entering house after house, dragging off men and women, throwing them in prison. Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.
4 So those scattered went everywhere, proclaiming the good news of the word. Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi.
5 Philip went down to the city of Samaria and proclaimed Christ to them. Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can.
6 The crowds paid attention together to Philip's words, hearing and seeing the signs he did. Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa.
7 Unclean spirits came out of many who were possessed, screaming loudly, and many paralyzed and lame were healed. Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa.
8 So there was great joy in that city. Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.
9 A man named Simon had already practiced magic in that city, amazing Samaria's people and claiming to be someone great. To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne,
10 Everyone, from least to greatest, listened to him, saying, "This man is God's power, called Great." dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma”
11 They paid attention to him because for a long time he had amazed them with his magic. Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa.
12 But when they believed Philip's good news about the kingdom of our Father and the name of Jesus Christ, men and women were baptized. Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata.
13 Simon himself believed, was baptized, and stayed close to Philip, amazed at the signs and great miracles he saw. Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.
14 When the apostles in Jerusalem heard Samaria had received our Father's word, they sent Peter and John to them. Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna.
15 When they arrived, they prayed for them that they might receive the Holy Spirit, Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki,
16 for the Holy Spirit had not yet fallen on any of them; they were only baptized into the name of the Lord Jesus. domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu.
17 Then they laid their hands on them, and they received the Holy Spirit. Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.
18 When Simon saw the Spirit given through the apostles' laying on of hands, he offered them money, Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi,
19 saying, "Give me this power too, so whoever I lay hands on receives the Holy Spirit." ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”
20 Peter said to him, "May your silver perish with you, since you thought you could buy our Father's gift with money! Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!
21 You have no part or share in this matter, for your heart is not right before our Father. Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba.
22 So turn from this evil, and pray to our Father that, if possible, your heart's intent may be forgiven you. Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka.
23 I see you poisoned by bitterness and bound by evil." Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.”
24 Simon answered, "Pray to God for me, that nothing you have said may come upon me." Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”
25 So, having testified and spoken our Lord Jesus's word, they returned to Jerusalem, preaching the good news in many Samaritan villages. Sa’ad da suka yi shaidar suka kuma yi shelar maganar Ubangiji, sai Bitrus da Yohanna suka koma Urushalima, suna wa’azin bishara a ƙauyukan Samariya masu yawa.
26 Then an angel of our Father told Philip, "Get up and go south to the road going down from Jerusalem to Gaza"—a desert road. To wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar, hanyar hamada, da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.”
27 He got up and went. There was an Ethiopian eunuch, a court official of Candace, queen of the Ethiopians, in charge of all her treasury, who had come to Jerusalem to worship, Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan ma’ajin Kandas (wanda yake nufin “sarauniyar mutanen Itiyofiya”). Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada,
28 and was returning, seated in his chariot and reading the prophet Isaiah. a kan hanyarsa ta komawa gida kuwa yana zaune bisan keken yaƙinsa yana karatun littafin annabin Ishaya.
29 And the Holy Spirit said to Philip, "Go over and catch up with that chariot." Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa wurin kekunan yaƙin nan ka yi kusa da ita.”
30 Philip ran up, heard him reading the prophet Isaiah, and asked, "Do you understand what you're reading?" Sai Filibus ya ruga zuwa wajen keken yaƙin ya kuma ji mutumin yana karatun littafin annabin Ishaya. Filibus ya yi tambaya ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”
31 He said, "How can I, unless someone guides me?" and invited Philip up to sit with him. Sai ya ce, “Ina fa zan iya, in ba dai wani ya fassara mini ba?” Saboda haka sai ya gayyaci Filibus yă hau yă zauna tare da shi.
32 Now the passage of Scripture he was reading was this: "Like a sheep he was led to the slaughter, and like a lamb silent before its shearer, so he did not open his mouth. Bābān yana karanta wannan Nassin, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.
33 In his humiliation justice was denied him. Who can describe his generation? For his life is taken away from the earth." A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya. Wa zai iya yin zancen zuriyarsa? Gama an ɗauke ransa daga duniya.”
34 The eunuch said to Philip, "Tell me, of whom does the prophet say this—himself, or someone else?" Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, “Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?”
35 Philip opened his mouth and, starting from this Scripture, told him the good news about Jesus. Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu.
36 Traveling the road, they reached water, and the eunuch said, "Look, water! What stops me from being baptized?" Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?”
38 He ordered the chariot to stop; both went down into the water, Philip and the eunuch, and Philip baptized him. Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma.
39 When they came up out of the water, the Spirit of our Father snatched Philip away; the eunuch never saw him again, but went on his way rejoicing. Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.
40 Philip found himself at Azotus. He traveled through, announcing the good news in every town until he reached Caesarea. Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana wa’azin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]