Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Acts 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Then the high priest asked, "Are these things true?" Sai babban firist ya tambaye shi ya ce, “Waɗannan zargen gaskiya ne?”
2 Stephen said, "Brothers and fathers, listen: Our Father of glory appeared to our father Abraham in Mesopotamia, before he lived in Haran, Game da wannan ya amsa ya ce, “’Yan’uwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran.
3 and told him, 'Leave your land and relatives, and go to the land I'll show you.' Allah ya ce, ‘Ka bar ƙasarka da kuma mutanenka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.’
4 He left the Babylonians' land and settled in Haran. After his father died, our Father moved him from there into this land you now live in. “Saboda haka ya bar ƙasar Kaldiyawa ya kuma yi zama a Haran. Bayan mutuwar mahaifinsa, Allah ya aika da shi wannan ƙasar da yanzu kuke zama.
5 He gave him no inheritance in it, not even a foot of ground—yet promised it to him and his descendants after him as a possession, though he had no child. Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro.
6 And our Father said his offspring would be foreigners in a land not their own, enslaved and mistreated 400 years. Allah ya yi magana da shi ta haka, ‘Shekara ɗari huɗu, zuriyarka za tă yi baƙunci a wata ƙasar da ba tasu ba, za su yi bauta su kuma sha wulaƙanci.
7 'I will judge the nation they serve,' our Father said, 'and after, they will come out and worship me in this place.' Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘Kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’
8 He gave him the covenant of circumcision. Abraham fathered Isaac and circumcised him on the eighth day; Isaac fathered Jacob, and Jacob the twelve ancestors. Sa’an nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan.
9 The ancestors, jealous of Joseph, sold him into Egypt, but our Father was with him, “Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi
10 and rescued him from all his troubles, gave him favor and wisdom before Pharaoh king of Egypt, who made him ruler over Egypt and Pharaoh's whole household. ya kuma cece shi daga dukan wahalolinsa. Ya ba wa Yusuf hikima ya kuma sa ya sami farin jini a wurin Fir’auna, sarkin Masar; saboda haka ya mai da shi mai mulki a kan Masar da kuma dukan fadarsa.
11 A famine and great suffering struck all Egypt and Canaan, and our fathers found no food. “Sai yunwa ta auko wa dukan Masar da Kan’ana, ta kawo wahala mai tsanani, kakanninmu ba su iya samun abinci ba.
12 Hearing there was grain in Egypt, Jacob sent our fathers there first. Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa akwai hatsi a Masar, sai ya aiki kakanninmu ziyararsu ta farko.
13 On the second visit, Joseph made himself known to his brothers, and Pharaoh learned of Joseph's family. A ziyararsu ta biyu, Yusuf ya faɗa wa ’yan’uwansa wane ne shi, Fir’auna kuwa ya sami sani game da iyalin Yusuf.
14 And Joseph sent for his father Jacob and all his relatives, seventy-five persons in all. Bayan wannan, Yusuf ya aika a zo da mahaifinsa Yaƙub da dukan iyalinsa, gaba ɗaya dai mutum saba’in da biyar ne.
15 And Jacob went down into Egypt, and he died, he and our fathers. Sai Yaƙub ya gangara zuwa Masar, inda shi da kuma kakanninmu suka mutu.
16 They were taken back to Shechem, and buried in the tomb Abraham had bought for silver from Hamor's sons in Shechem. Aka dawo da gawawwakinsu Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya daga wurin ’ya’yan Hamor da waɗansu kuɗi a Shekem.
17 As the time of the promise our Father gave Abraham neared, the people grew and multiplied in Egypt, “Da lokaci ya yi kusa da Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim, sai yawan mutanenmu da suke a Masar ya ƙaru ƙwarai.
18 until there arose over Egypt another king who did not know Joseph. Sa’an nan wani sarki, wanda bai san kome game da Yusuf ba, ya zama mai mulkin Masar.
19 This king exploited our people and mistreated our fathers, forcing them to abandon their infants to die. Ya kuwa wulaƙanta mutanenmu sosai, ya kuma gwada wa kakanni-kakanninmu azaba ta wurin tilasta su su zubar da sababbin jariransu, don su mutu.
20 At that time Moses was born, beautiful in our Father's sight. He was raised three months in his father's house. “A lokacin nan aka haifi Musa, shi kuwa ba kamar sauran jarirai ba ne. Wata uku aka yi renonsa a gidan mahaifinsa.
21 And when he was abandoned, Pharaoh's daughter adopted him and brought him up as her own son. Sa’ad da aka ajiye shi a waje, diyar Fir’auna ta ɗauke shi ta kuma rene shi kamar ɗanta.
22 Moses was trained in all Egyptian wisdom, and was strong in speech and action. Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka.
23 When he was forty years old, he decided to visit his brothers, the sons of Israel. “Da Musa ya cika shekara arba’in da haihuwa, sai ya yanke shawara yă ziyarci ’yan’uwansa Isra’ilawa.
24 Seeing one of them wronged, he defended the oppressed man and avenged him by striking down the Egyptian. Ya ga ɗayansu yana shan wulaƙanci a hannun wani mutumin Masar, sai ya je ya kāre shi, ya rama masa ta wurin kashe mutumin Masar ɗin.
25 He thought his brothers would understand our Father was giving them salvation through his hand, but they didn't understand. Musa ya yi tsammani mutanensa za su gane cewa, Allah yana amfani da shi don yă cece su, amma ba su gane ba.
26 The next day he came upon them as they were fighting and tried to reconcile them, saying, 'Men, you are brothers. Why do you wrong each other?' Kashegari, Musa ya sadu da Isra’ilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku ’yan’uwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’
27 But the man wronging his neighbor shoved Moses aside, saying, 'Who made you ruler and judge over us? “Amma mutumin da yake wulaƙanta ɗayan, ya tura Musa a gefe ya ce, ‘Wa ya mai da kai mai mulki, da alƙali a kanmu?
28 Do you want to kill me as you killed the Egyptian yesterday?' Kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan na jiya?’
29 At this word, Moses fled and lived as a foreigner in the land of Midian, where he fathered two sons. Sa’ad da Musa ya ji haka, sai ya gudu zuwa ƙasar Midiyan, inda ya yi baƙunci, ya kuma haifi ’ya’ya biyu maza.
30 Forty years later, an angel appeared to him in the wilderness of Mount Sinai, in a burning bush's flame. “Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai.
31 Moses saw it and was amazed; as he approached to look closer, our Father's voice came: Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,
32 'I am the God of your fathers—the God of Abraham, Isaac, and Jacob.' Moses trembled, not daring to look. ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.
33 Then our Father told him, 'Take the sandals off your feet, for the place you're standing on is holy ground.' “Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne.
34 I have indeed seen my people's suffering in Egypt, heard their groaning, and come down to rescue them. Now go—I'm sending you to Egypt. Tabbatacce na ga wulaƙancin da ake yi wa mutanena a Masar. Na ji nishinsu na kuma sauka domin in ’yantar da su. Yanzu ka zo, zan aike ka ka koma Masar.’
35 This Moses, whom they rejected, saying, 'Who made you ruler and judge?'—this is the one our Father sent as both ruler and redeemer, through the hand of the angel who appeared to him in the bush. “Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin mala’ikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yă zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu.
36 This man led them out, doing wonders and signs in the land of Egypt, at the Red Sea, and in the wilderness for forty years. Ya fitar da su daga Masar ya kuma yi ayyukan da abubuwan banmamaki a Masar, a Jan Teku, da kuma cikin hamada har shekara arba’in.
37 This is the Moses who told Israel's sons, 'Our Father will raise up a prophet like me for you, from your brothers.' “Wannan Musa ne ya ce Isra’ilawa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’
38 This is the one who was in the wilderness assembly with the angel speaking to him at Mount Sinai, and with our fathers—he received living words to give us. Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da mala’ikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don yă miƙa mana.
39 Our fathers refused to obey him; they rejected him and in their hearts turned back to Egypt, “Amma kakanninmu suka ƙi yin masa biyayya. A maimakon haka, sai suka ƙi shi a cikin zuciyarsu kuwa suka koma Masar.
40 telling Aaron, 'Make us gods to go ahead of us. As for this Moses who led us out of the land of Egypt, we don't know what happened to him.' Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba!’
41 They made a calf in those days, offered a sacrifice to the idol, and celebrated what their hands had made. A lokacin ne suka ƙera gunki mai siffar ɗan maraƙi. Suka kawo masa hadayu suka kuma yi bikin girmama abin da suka ƙera da hannuwansu.
42 But our Father turned away, giving them over to worship the host of heaven, as written in the prophets' book: 'Did you bring me slaughtered animals and sacrifices for forty years in the wilderness, house of Israel? Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa, “ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila?
43 You carried Moloch's tent and your god Rephan's star, the idols you fashioned to worship them; so I will banish you far beyond Babylon.' Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek, da tauraron allahnku Refan, gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada. Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.
44 Our ancestors had the tent of witness in the wilderness, as he who spoke to Moses directed him to make it, matching the pattern he'd seen. “Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani.
45 Our fathers in turn brought it in with Joshua when they dispossessed the nations that our Father drove out before them. So it was until the days of David, Bayan sun gāji tabanakul nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga al’umman da Allah ya kora a idanunsu. Tabanakul ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda,
46 who found favor with our Father and asked to find a dwelling place for our Father. wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yă yi wa Allah na Yaƙub wurin zama.
47 But it was Solomon who built a house for him. Amma Solomon ne ya gina masa gida.
48 Yet the Most High does not live in houses made by human hands, as the prophet says: “Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa,
49 'Heaven is my throne, and the earth is my footstool. What kind of house will you build for me, says our Father, or what is the place of my rest? “ ‘Sama ne kursiyina, duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata. Wane irin gida za ka gina mini? Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance? In ji Ubangiji.
50 Did not my hand make all these things?' Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’
51 "You stubborn people, uncircumcised in heart and ears, always resist the Holy Spirit—like your fathers, so do you. “Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki!
52 Which of the prophets did your fathers not persecute? They killed those who announced beforehand the Righteous One's coming—whom you have now betrayed and murdered. An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi
53 You who received the law through angels and yet did not keep it." ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin mala’iku amma ba ku yi biyayya da ita ba.”
54 Now when they heard these things they were enraged, and they ground their teeth at him. Da membobin Sanhedrin suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu.
55 But Stephen, full of the Holy Spirit, looked into heaven, saw the glory of our Father, and Jesus standing at the right hand of our Father. Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah.
56 And he said, "Look, I see the heavens opened and the Son of Man standing at our Father's right hand." Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”
57 But they cried out with a loud voice, covered their ears, and rushed at him. Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya.
58 They threw him out of the city and stoned him. The witnesses laid their coats at the feet of a young man named Saul. Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.
59 And as they were stoning him, Stephen called out, "Lord Jesus, receive my spirit." Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”
60 Kneeling, he cried out loudly, "Lord, do not hold this sin against them." Then he fell asleep. Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]