Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Acts 6 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In those days, as the disciples multiplied, the Greek-speaking Jews grumbled against the Hebrews because their widows were overlooked in the daily distribution of food. A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.
2 So the Twelve called all the disciples together and said, "It's not right for us to neglect our Father's word to serve tables. Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba.
3 So, brothers, pick seven men among you, well-respected, full of the Holy Spirit and wisdom, whom we'll appoint to this task. ’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki
4 But we will devote ourselves to prayer and to the ministry of the word." mu kuwa mu mai da halinmu ga yin addu’a da kuma hidimar maganar Allah.”
5 The whole assembly approved, and chose Stephen—full of faith and the Holy Spirit—along with Philip, Prochorus, Nicanor, Timon, Parmenas, and Nicolaus, a convert from Antioch. Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.
6 They presented these men to the apostles, who prayed and laid their hands on them. Suka gabatar da waɗannan mutane wa manzanni, waɗanda kuwa suka yi addu’a, suka ɗibiya hannuwansu a kansu.
7 The word of our Father spread, and disciples in Jerusalem multiplied greatly; a great number of priests became obedient to the faith. Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya.
8 Now Stephen, full of grace and power, was performing great wonders and signs among the people. To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane.
9 Some from the so-called Synagogue of the Freedmen—Cyrenians, Alexandrians, and men from Cilicia and Asia—rose up to argue with Stephen. Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus,
10 Yet they could not stand up against the wisdom and the Spirit with which he was speaking. amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba.
11 Then they secretly instructed men to say, "We heard him speak blasphemous words against Moses and God." Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”
12 They stirred up the people, elders, and scribes; came upon him, seized him, and brought him before the council. Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa.
13 They brought in false witnesses, saying, "This man never stops speaking against this holy place and the law. Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka.
14 For we heard him say this Jesus of Nazareth will destroy this place and change the customs Moses handed down to us." Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.”
15 Everyone sitting in the council stared at him and saw his face was like an angel's face. Dukan waɗanda suke zaune a Majalisar suka kafa wa Istifanus ido, suka kuma ga fuskarsa ta yi kama da ta mala’ika.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]