Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Timothy 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 But understand this: in the last days there will come times of difficulty. Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe.
2 For people will be self-lovers, money-lovers, boastful, arrogant, abusive, disobedient to parents, ungrateful, unholy. Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki,
3 Heartless, unforgiving, slanderous, without self-control, brutal, hating what is good, marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta,
4 treacherous, reckless, swollen with conceit, lovers of pleasure rather than lovers of our Father. masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah
5 They keep the shape of devotion to God but deny its power—turn from them. suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.
6 For among these are those who slip into homes and trap weak women weighed down with sins, driven by various desires. Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu,
7 Always learning but never able to come to a knowledge of the truth. kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya.
8 As Jannes and Jambres opposed Moses, these also oppose the truth—minds corrupted, disqualified regarding the faith. Kamar dai yadda Yannes da Yamberes suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya, mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki.
9 But they won't get far, for their foolishness will be clear to all, as with those two men. Sai dai ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.
10 You, however, have followed my teaching, conduct, purpose, faith, patience, love, endurance, Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri,
11 my persecutions and suffering—at Antioch, at Iconium, at Lystra, what persecutions I endured! Yet the Lord rescued me from them all. tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu.
12 Indeed, all who desire to live a godly life in Christ Jesus will be persecuted, Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.
13 while evil people and impostors will go on from bad to worse, deceiving and being deceived. Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.
14 But you—stay with what you learned and became convinced of, knowing from whom you learned it, Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su,
15 and that from infancy you have known the sacred writings, able to make you wise for salvation through faith in Christ Jesus. da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
16 All Scripture is breathed out by our Father—useful for teaching, exposing wrong, correcting, and training in right living, Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci,
17 so that the person of our Father may be complete, equipped for every good work. domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]