Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Timothy 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 So then, my child, draw your strength from the grace that is in Christ Jesus. Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu.
2 And what you heard from me in the presence of many witnesses, entrust to faithful people able to teach others too. Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu.
3 Take your share of suffering like a good soldier of Christ Jesus. Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.
4 No soldier on duty gets tangled in civilian affairs—he wants to please the one who enlisted him. Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja.
5 And an athlete is not crowned unless he competes according to the rules. Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki.
6 The hard-working farmer ought to be the first to receive a share of the crops. Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona.
7 Think over what I am saying, for the Lord will give you understanding in everything. Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan.
8 Remember Jesus Christ, risen from the dead, a descendant of David, as told in my gospel, Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata,
9 for which I suffer, chained like a criminal. But the word of our Father is not chained! wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba.
10 So I endure everything for the sake of the chosen, so they too may gain the salvation in Christ Jesus, with eternal glory. Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.
11 This saying is trustworthy: If we have died with him, we will also live with him; Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi;
12 if we endure, we will also reign with him; if we disown him, he also will disown us; in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;
13 if we are faithless, he remains faithful, for he cannot disown himself. in ba mu da aminci, shi dai mai aminci ne, domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”
14 Remind them of these things, and warn them before our Father not to quarrel over words—useless, and ruins those who listen. Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.
15 Do your best to present yourself to our Father approved, a worker unashamed, rightly handling the word of truth. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.
16 But avoid empty, godless chatter; it leads people further into wickedness, Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah.
17 and their talk will spread like gangrene. Among them are Hymenaeus and Philetus, Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus,
18 who wandered away from the truth, claiming the resurrection already happened, and are undermining some people's faith. waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu.
19 Yet our Father's firm foundation stands, sealed: "He knows those who are his," and "Let all who name his name turn from evil." Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.”
20 In a large house there are vessels not only of gold and silver, but also of wood and clay—some for honor, some for dishonor. A babban gida akwai kayayyakin da ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma har da na katako da na yumɓu ma; waɗansu domin hidima mai daraja waɗansu kuwa domin hidima marar daraja.
21 So if anyone purifies himself from these, he becomes a vessel of honor: holy, useful to the Master, ready for every good work. In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.
22 Flee youthful cravings; pursue righteousness, faith, love, and peace with those who call on the Lord from a pure heart. Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.
23 Have nothing to do with foolish, ignorant controversies; you know they breed quarrels. Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa.
24 The Lord's servant must not be quarrelsome, but be gentle to all, able to teach, patient when wronged. Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma.
25 Gently correcting those who oppose him. Perhaps our Father will grant them repentance to know the truth, Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya,
26 and they may sober up, escaping the devil's trap where he has held them captive to do his will. su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]