Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 John 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The elder, to the chosen lady and her children, whom I love in truth—not only I, but all who know the truth, Dattijon nan, Zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya da kuma ’ya’yanta, waɗanda nake ƙauna ƙwarai da gaske kuma ba ni kaɗai ba, amma har da dukan waɗanda suka san gaskiya.
2 because of the truth that lives in us and will be with us forever. Muna ƙaunarku saboda gaskiyan nan, wadda take cikinmu za tă kuma kasance tare da mu har abada.
3 Grace, mercy, and peace will be with us from our Father and from Jesus Christ, our Father's Son, in truth and love. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da kuma Yesu Kiristi, Ɗan Uba, su kasance tare da mu cikin gaskiya da ƙauna.
4 I was overjoyed to find some of your children walking in truth, as our Father commanded us. Na yi farin ciki ƙwarai, da na sami waɗansu ’ya’yanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda Uba ya umarce mu.
5 Now I ask you, dear lady: not a new command, but one we've had from the start—love one another. Yanzu kuma, uwargida ƙaunatacciya, ba sabon umarni nake rubuta miki ba sai dai wanda muke da shi tun farko. Ina roƙo cewa mu ƙaunaci juna.
6 This is love: that we walk by his commands. This is the command, as you heard from the beginning: that you walk in love. Ƙauna, ita ce mu yi biyayya ga umarnansa. Kamar yadda kuka ji tun da fari, umarninsa shi ne ku yi zaman ƙauna.
7 For many deceivers have gone out into the world, denying that Jesus Christ came in the flesh. This is the deceiver and the antichrist. Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi.
8 Watch yourselves, so that you don't lose what we have worked for, but receive a full reward. Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada.
9 Anyone who oversteps, not remaining in Christ's teaching, lacks our Father; whoever remains in the teaching has both our Father and the Son. Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan.
10 If someone comes to you without this teaching, don't welcome them into your home or greet them, Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi.
11 for whoever greets him shares in his evil deeds. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.
12 I have much to write, but I'd rather not use paper and ink. I hope to come and speak with you face to face, so our joy may be complete. Ina da abubuwa da dama da zan rubuta muku, sai dai ba na so in yi amfani da takarda da inki in rubuta. A maimako, ina fata in ziyarce ku in kuma yi magana da ku fuska da fuska, domin farin cikinmu yă zama cikakke.
13 The children of your chosen sister greet you. ’Ya’yan ’yar’uwarki wadda Allah ya keɓe, suna gaishe ku.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]