Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

3 John 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The elder, to the beloved Gaius, whom I love in truth. Dattijon nan, Zuwa ga ƙaunataccen abokina Gayus, wanda nake ƙauna ƙwarai da gaske.
2 Beloved, I pray you prosper in every way and stay healthy, as your soul prospers. Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.
3 I rejoiced greatly when brothers arrived and testified about your faithfulness to the truth—for you truly are walking in it. Na yi farin ciki ƙwarai sa’ad da waɗansu ’yan’uwa suka zo suka yi zance game da yadda kake da aminci ga gaskiyan nan da kuma yadda kake cin gaba cikin gaskiyan nan.
4 I have no greater joy than this: to hear that my children are walking in the truth. Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.
5 Beloved, you act faithfully in all you do for the brothers, even strangers. Abokina ƙaunatacce, kana da aminci cikin abin da kake yi wa ’yan’uwa, ko da yake su baƙi ne a gare ka.
6 They testified to your love before the church. Send them on in a way worthy of our Father. Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah.
7 For they went out for the sake of the Name, accepting nothing from the Gentiles. Saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa karɓan wani taimako daga waɗanda ba masu bi ba.
8 Therefore we ought to support such people, so that we may be fellow workers for the truth. Saboda haka ya kamata mu nuna halin karɓan baƙi ga irin mutanen nan domin mu yi aiki tare saboda gaskiyan nan.
9 I wrote something to the church, but Diotrephes, who loves being first among them, does not receive us. Na rubuta wa ikkilisiya, amma Diyotirefes, wanda yake son zama na farko, ya ƙi yă yi hulɗa da mu.
10 So if I come, I'll expose what he's doing—slandering us with malicious words. Not satisfied with that, he refuses to welcome the brothers, stops those who want to, and throws them out of the church. Saboda haka in na zo, zan tone abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har yana ƙin marabtar ’yan’uwa. Yana hana waɗanda suke so yin haka, yana ma korinsu daga ikkilisiya.
11 Beloved, don't imitate evil, but good. Whoever does good is from our Father; whoever does evil hasn't seen our Father. Abokina ƙaunatacce, kada ka yi koyi da abin da yake mugu sai dai abin da yake nagari. Duk mai yin abin da yake nagari daga Allah yake. Duk mai yin abin da yake mugu bai taɓa sanin Allah ba.
12 All speak well of Demetrius, and so does the truth. We testify too, and you know our testimony is true. Demetiriyus yana da shaida mai kyau daga wurin kowa, har gaskiya kanta ma ta shaide shi. Mu ma muna ba da shaida mai kyau a kansa, ka kuma san cewa shaidarmu gaskiya ce.
13 I had much to write to you, but I would rather not write with pen and ink. Ina da abubuwa da dama da zan rubuta maka, sai dai ba na so in yi amfani da alƙalami da inki in rubuta su.
14 I hope to see you soon, and we will talk face to face. Ina fata in gan ka nan ba da daɗewa ba, za mu kuwa yi magana fuska da fuska.
15 Peace to you. The friends send their greetings. Greet each of the friends by name. Salama gare ka. Abokai a nan suna gaishe ka. Ka gai da abokai a can da sunansu.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]