Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 8 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 After twenty years, in which Solomon built the house of our Father and his own palace, A ƙarshen shekaru ashirin, a lokacin da Solomon ya gina haikalin Ubangiji da nasa fadan,
2 Solomon rebuilt the cities that Huram had given him, and settled the people of Israel in them. Solomon ya sāke gina ƙauyukan da Hiram ya ba shi, ya kuma zaunar da Isra’ilawa a cikinsu.
3 Then Solomon marched against Hamath-zobah and overpowered it. Sa’an nan Solomon ya tafi Hamat-Zoba ya ci ta da yaƙi.
4 He built Tadmor in the wilderness, along with all the storage cities he built in Hamath. Ya kuma gina Tadmor a hamada da kuma dukan biranen ajiyar da ya gina a Hamat.
5 He also rebuilt Upper Beth-horon and Lower Beth-horon as fortified cities, with walls, gates, and bars, Ya sāke gina Bet-Horon na Bisa da kuma Bet-Horon na Ƙasa a matsayin birane masu katanga, da bangaye da ƙofofi da kuma ƙyamare,
6 Baalath, all Solomon's supply cities, his chariot and horsemen cities, and all he desired to build in Jerusalem, Lebanon, and his whole realm. haka kuma Ba’alat da dukan biranen ajiyarsa, da kuma dukan birane domin keken yaƙinsa da dawakansa, duk abin da ya so yă gina a Urushalima, a Lebanon da kuma dukan yankin da ya yi mulki, ya gina shi.
7 There were still people left from the Hittites, Amorites, Perizzites, Hivites, and Jebusites, who were not Israelites. Dukan mutanen da suka rage daga Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa (waɗannan mutane ba Isra’ilawa ba ne),
8 Their descendants still living in the land, whom Israel had not destroyed, Solomon conscripted for forced labor, as they still are today. wato, zuriyarsu da suka ragu a ƙasar, wadda Isra’ilawa ba su hallaka ba, waɗannan ne Solomon ya mai da su bayinsa na aikin dole, kamar yadda yake har wa yau.
9 Solomon enslaved no Israelites for his work; they were soldiers, commanders of his officers, and commanders of his chariots and horsemen. Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi don aikinsa ba; su ne mayaƙansa, shugabannin hafsoshinsa, da shugabannin keken yaƙinsa da kuma mahayan keken yaƙinsa.
10 These were King Solomon's chief officers: 250 who supervised the people. Su ne kuma manyan ma’aikatan Sarki Solomon, manyan mutane ɗari biyu da hamsin masu lura da mutane.
11 Solomon brought Pharaoh's daughter from the City of David to the house he built her, saying, "No wife of mine will live in David king of Israel's house, for holy is wherever our Father's ark has entered." Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”
12 Then Solomon offered burnt offerings to our Father on the altar he built before the portico, A kan bagaden Ubangiji da ya gina a gaban shirayi, Solomon ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji,
13 daily as required, by Moses' command: Sabbaths, New Moons, and three yearly festivals—the Feast of Unleavened Bread, the Feast of Weeks, and the Feast of Tabernacles. bisa ga bukace-bukace na kullum don hadayun da Musa ya umarta don Asabbatai, Sabon Wata da kuma bukukkuwa uku na shekara, Bikin Burodi Marar Yisti, Bikin Makoni da Bikin Tabanakul.
14 Following his father David's rules, he set priestly divisions for service, Levite divisions to praise and serve before the priests as each day required, and gatekeeper divisions at each gate, for David the man of our Father had commanded it. Bisa ga farillar mahaifinsa Dawuda, ya naɗa ɓangarori na firistoci don ayyukansu da Lawiyawa don su jagoranci yabo su kuma taimaki firistoci bisa ga bukace-bukacen kowace rana. Ya kuma naɗa matsara ƙofofi ɓangarori, ɓangarori don ƙofofi dabam-dabam domin abin da Dawuda mutumin Allah ya umarta ke nan.
15 They followed the king's orders to the priests and Levites exactly, down to the storerooms. Ba a kuwa yi rashin biyayya ba game da abin da sarki ya umarta game da firistoci ko Lawiyawa a kan kayan haikalin ba.
16 All Solomon's work was finished, from the day our Father's house was founded until its completion; our Father's house was complete. An yi dukan ayyukan Solomon, daga ranar kafa tushen haikalin Ubangiji har gamawarsa. Ta haka aka gama haikalin Ubangiji.
17 Then Solomon went to Ezion-geber and Eloth on the seacoast in the land of Edom. Sa’an nan Solomon ya tafi Eziyon Geber da Elot a bakin tekun Edom.
18 Huram sent him ships by his servants, with sailors who knew the sea; they sailed with Solomon's servants to Ophir, took about seventeen tons of gold, and brought it to King Solomon. Sai Hiram ya aika masa jiragen ruwan da masu tuƙinsu waɗanda suka san teku sosai. Ma’aikatan Hiram suka tafi da na Solomon zuwa Ofir suka dawo da talentin zinariya ɗari huɗu da hamsin wa Sarki Solomon.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]