Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 9 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Hearing Solomon's fame, the queen of Sheba came to Jerusalem to test him with hard questions—a huge retinue, camels bearing spices, much gold, precious stones. Reaching Solomon, she told him all on her mind. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta.
2 Solomon answered all her questions; nothing was too hard for him to explain to her. Solomon ya amsa dukan tambayoyinta; babu wani abin da ya yi masa wuya yă bayyana mata.
3 When the queen of Sheba had seen the wisdom of Solomon, and the palace he had built, Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ga hikimar Solomon da kuma fadan da ya gina,
4 the food on his table, his officials seated, his servants attending, their clothing, his cupbearers and theirs, and the burnt offerings at the house of our Father—it took her breath away. ta ga abincin da yake teburinsa, ta ga zaman fadawansa, bayi masu yin masa hidima cikin rigunansu, ta ga masu riƙe kwaf cikin rigunansu da kuma hadayun ƙonawar da ya yi a haikalin Ubangiji, sai mamaki ya kama ta.
5 She told the king, "The report I heard in my own land about your words and your wisdom was true. Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da nasarorinka da hikimarka, gaskiya ne.
6 I didn't believe the reports until I came and saw for myself. Not half the greatness of your wisdom was told me; you surpass the report I heard. Amma ban gaskata abin da suka faɗa ba sai da na zo na kuma gani da idanuna. Tabbatacce, ko rabin girman hikimarka ba a faɗa mini ba, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba.
7 How happy your people! How happy these servants who stand before you always, hearing your wisdom! Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka!
8 Blessed be the LORD your God, who delighted in you and set you on his throne as king for the LORD your God! Because your God loved Israel, establishing them forever, he made you king to do justice and righteousness." Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.”
9 She gave the king about 9,000 pounds of gold, great quantities of spices, and precious stones. No spice ever matched what the queen of Sheba gave King Solomon. Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba.
10 Huram's and Solomon's servants, who brought gold from Ophir, also brought sandalwood and precious stones. (Mutanen Hiram da mutanen Solomon suka kawo zinariya daga Ofir, suka kuma kawo gungumen algum da duwatsu masu daraja.
11 From the sandalwood the king made steps for our Father's house and his palace, and lyres and harps for the singers—none like them ever seen in Judah. Sarki ya yi amfani da gungumen algum don matakalan haikalin Ubangiji da kuma na fadan sarki, ya kuma yi garayu da molaye don mawaƙa. Ba a taɓa gani irinsu a Yahuda ba.)
12 King Solomon gave the queen of Sheba all she desired, whatever she asked, more than she had brought him. Then she returned to her own land with her servants. Sarki Solomon ya ba sarauniyar Sheba duk abin da take so da kuma ta nema; ya ba ta fiye da abin da ta kawo masa. Sa’an nan ta tashi ta koma ƙasarta tare da masu rufe mata baya.
13 The weight of gold that came to Solomon in a single year was about twenty-five tons, Nauyin zinariyar da Solomon yake karɓa shekara-shekara talenti 666 ne,
14 besides what traders and merchants brought; all the kings of Arabia and governors of the land brought gold and silver to Solomon. ban da harajin da fatakai da ’yan kasuwa suke biya. Haka kuma dukan sarakunan Arabiya da gwamnonin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa wa Solomon.
15 King Solomon made 200 large shields of hammered gold, each with about fifteen pounds of gold. Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu da zinariya; an yi kowane garkuwa da bekas ɗari shida na zinariya.
16 He made 300 smaller shields of hammered gold, about seven and a half pounds each. The king put them in the House of the Forest of Lebanon. Ya kuma yi ƙanana garkuwoyi zinariya ɗari uku, da bekas ɗari uku na zinariya a kowanne. Sarki ya sa su a cikin Fadan da ake kira Kurmin Lebanon.
17 The king made a large ivory throne and covered it with pure gold. Sai sarki ya yi wata kujerar sarauta mai girma da aka shafe ta da hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla.
18 The throne had six steps with a gold footstool attached to it; armrests flanked the seat, with two lions standing beside them, Kujerar tana da matakalai shida, da wurin sa ƙafa na zinariya haɗe da ita. A kowane gefen wurin zama, akwai wurin ajiye hannu, da zaki tsaye kusa da kowannensu.
19 and twelve lions stood there, one at either end of each of the six steps. Nothing like it was ever made for any kingdom. Zakoki goma sha biyu sun tsaya a kan matakalai shida, ɗaya a ƙarshen matakala guda. Ba a taɓa yin irin wannan abu don wata masarauta ba.
20 All King Solomon's cups were gold, and every vessel of the House of the Forest of Lebanon was pure gold. Silver counted as nothing in Solomon's days, Dukan kwaf na Sarki Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon zinariya ne zalla. Ba a yi wani abu da azurfa ba, domin ba a ɗauki azurfa a zamanin Solomon a bakin kome ba.
21 for the king's ships sailed to Tarshish with Huram's servants; every three years the Tarshish ships returned with gold, silver, ivory, apes, and peacocks. Sarki yana da jerin jiragen ruwa na kasuwanci waɗanda mutanen Hiram ne suke kula da su. Sau ɗaya kowace shekara uku sukan dawo ɗauke da zinariya, azurfa, hauren giwa, gogo da kuma birai.
22 So King Solomon surpassed all the kings of the earth in riches and wisdom. Sarki Solomon ya fi arziki da hikima in aka kwatanta da dukan sauran sarakunan duniya.
23 All the kings of the earth sought Solomon's presence to hear the wisdom our Father put in his heart. Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa.
24 Each brought his gift—silver and gold articles, garments, weapons, spices, horses, and mules—year after year. Shekara, shekara, duk wanda ya zo wurinsa yakan kawo kyauta, kayayyakin azurfa da na zinariya, da riguna, makamai da kayan yaji, da dawakai da kuma alfadarai.
25 Solomon had 4,000 horse-and-chariot stalls and 12,000 horsemen, kept in the chariot cities and with the king in Jerusalem. Solomon ya kasance da wuraren ajiye dawakai dubu huɗu don dawakai da kekunan yaƙi, yana da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi da kuma tare da shi a Urushalima.
26 He ruled all the kings from the Euphrates to the land of the Philistines, to Egypt's border. Ya yi mulki bisa dukan sarakuna daga Kogi Yuferites zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar.
27 The king made silver in Jerusalem like stones, and cedar as plentiful as foothill sycamore-figs. Sarki ya sa azurfa ta zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka.
28 Horses were imported for Solomon from Egypt and from all the lands. An sayo dawakan Solomon daga Masar da kuma daga dukan sauran ƙasashe.
29 Solomon's other deeds, first to last—aren't they recorded in the words of Nathan the prophet, Ahijah of Shiloh's prophecy, and the visions of Iddo the seer about Jeroboam son of Nebat? Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin annabi Natan, cikin annabcin Ahiya mutumin Shilo da kuma cikin wahayin Iddo mai gani game da Yerobowam ɗan Nebat.
30 Solomon reigned in Jerusalem over all Israel forty years. Solomon ya yi mulki a Urushalima a bisa dukan Isra’ila shekaru arba’in.
31 Solomon rested with his ancestors, buried in the city of David his father. His son Rehoboam reigned in his place. Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi cikin birnin Dawuda mahaifinsa. Rehobowam ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]