Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 When Solomon finished praying, fire fell from heaven and consumed the burnt offering and sacrifices, and our Father's glory filled the house. Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.
2 The priests couldn't enter our Father's house, because our Father's glory filled it. Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi.
3 When all the Israelites saw the fire fall and our Father's glory on the house, they knelt, faces to the ground on the pavement, worshiping and thanking our Father: "He is good; his faithful love endures forever." Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa, “Ubangiji mai alheri ne, ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”
4 Then the king and all the people offered sacrifices before our Father. Sai sarki da dukan mutanen suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji.
5 King Solomon sacrificed 22,000 oxen and 120,000 sheep; the king and all the people dedicated the house of our Father. Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah.
6 The priests stood at their posts; the Levites stood with the musical instruments for our Father that King David made for giving thanks to our Father—"for his faithful love endures forever"—whenever David praised through the instruments. Opposite them the priests blew the trumpets, and all Israel stood. Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.
7 Solomon dedicated the courtyard's middle, in front of our Father's house, for there he offered the burnt offerings and fat of the peace offerings, since the bronze altar he had made could not hold the burnt offering, grain offering, and fat. Solomon ya tsarkake sashen tsakiya na filin da yake gaban haikalin Ubangiji, a can ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayun salama domin bagaden tagullar da ya yi ba zai iya ɗaukan hadayun ƙonawa, hadayun hatsi da kuma ɓangarori na kitsen ba.
8 At that time Solomon kept the feast seven days, and all Israel with him—a vast assembly—from Lebo-hamath to the Brook of Egypt. Ta haka Solomon ya kiyaye bikin a wannan lokaci har kwana bakwai, dukan Isra’ila kuwa tare da shi, babban taro, mutane daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar.
9 On the eighth day they held a closing assembly, having kept the altar's dedication seven days and the feast seven days. A rana ta takwas sai suka yi taro, gama sun yi bikin keɓewar bagade na kwana bakwai da kuma biki na ƙarin kwana bakwai.
10 On the twenty-third day of the seventh month, he sent the people home, joyful and glad at heart for the goodness our Father showed to David, to Solomon, and to Israel his people. A rana ta ashirin da uku na watan bakwai sai ya sallami mutane su tafi gidajensu da farin ciki da kuma murna a zuciya saboda abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi domin Dawuda da Solomon da kuma domin mutanensa Isra’ila.
11 Solomon finished the house of our Father and the royal palace. Everything Solomon set his heart to do in the house of our Father and his own house, he did successfully. Sa’ad da Solomon ya gama haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki ya kuma yi nasara a yin dukan abin da yake a zuciyarsa da zai yi a haikalin Ubangiji da kuma a fadarsa,
12 Then our Father appeared to Solomon at night and said to him: "I have heard your prayer and chosen this place for myself as a house of sacrifice. sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.
13 "If I shut the skies so no rain falls, or command locusts to devour the land, or send a plague among my children, “Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena,
14 if my children—who bear my name—humble themselves, pray, seek my face, and turn from their evil ways, I will hear from heaven, forgive their sin, and heal their land. in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.
15 Now my eyes will be open and my ears attentive to the prayer offered in this place. Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri.
16 Now I have chosen and dedicated this house, so my name remains there forever; my eyes and heart will be there always. Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.
17 As for you—if you walk before me as David your father walked, doing all I commanded you and keeping my statutes and judgments, “Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina,
18 then I will confirm your kingdom's throne, as I covenanted with David your father: "A man of yours will always rule over Israel." zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’
19 But if you turn away, abandon my statutes and commands I set before you, and go serve other gods and worship them, “Amma in ka juya daga gare ni ka yashe ƙa’idodi da umarnan da na ba ka, ka yi gaban kanka don ka bauta wa waɗansu alloli ka kuma yi musu sujada,
20 then I will uproot Israel from my land I gave them, cast from my sight this temple I set apart for my name, and make it an example and taunt among all peoples. zan tumɓuke Isra’ila daga ƙasata, wadda na ba su, zan kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Zan mai da shi abin karin magana da abin ba’a cikin dukan mutane.
21 This house, once so exalted, will leave everyone who passes by appalled, saying, "Why did the LORD do this to this land and this house? Ko da yake wannan haikali yanzu mai girma ne, dukan wanda ya wuce zai kaɗa kai yă ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi irin wannan abu ga wannan ƙasa da kuma ga wannan haikali?’
22 They will answer, "Because they abandoned the LORD, God of their ancestors, who brought them out of the land of Egypt, and clung to other gods, bowing and serving them—that's why he brought all this disaster on them." Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’ ”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]