Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 6 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Then Solomon said, "Our Father has said that he would dwell in thick darkness. Sa’an nan Solomon ya ce, “Ubangiji ya faɗa cewa zai zauna cikin duhun girgije;
2 But I have built you an exalted house, a place for you to dwell in forever." na gina ƙasaitaccen haikali dominka, wuri domin ka zauna har abada.”
3 Then the king turned and blessed the whole assembly of Israel as they all stood. Yayinda dukan taron Isra’ila suke tsaye a can, sai sarki ya juya ya albarkace su.
4 He said, "Praise our Father, the God of Israel, whose hand has fulfilled what his mouth promised my father David, saying, Sa’an nan ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannuwansa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce,
5 'Since the day I brought my people out of Egypt, I chose no city from all the tribes of Israel to build a house for my name to be there, nor any man to rule my people Israel. ‘Tun ranar na da fitar da mutanena daga Masar, ban zaɓi wani birni a wata kabilar Isra’ila don a gina haikali domin Sunana ya kasance a can ba, ba kuwa zaɓi wani yă zama shugaba a bisa jama’ata Isra’ila ba.
6 But I chose Jerusalem for my name to be there, and I chose David to lead my people Israel.' Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’
7 David my father had it in his heart to build a house for the name of our Father, the God of Israel. “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a zuciyarsa yă gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.
8 But our Father told David my father, 'Because building a house for my name was in your heart, you did well to intend this. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Domin yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka kasance da wannan a zuciyarka.
9 But you will not build the house; your son, from your own body—he will build the house for my name.' Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikalin, amma ɗanka wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’
10 Now our Father has fulfilled the word he spoke: I have succeeded David my father and sit on Israel's throne, as he promised, and I have built the house for the name of our Father, the God of Israel. “Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina yanzu kuwa na zauna a kan kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.
11 There I placed the ark, holding the covenant our Father made with the people of Israel." A can na ajiye akwatin alkawari, inda alkawarin Ubangiji da ya yi da mutanen Isra’ila yake.”
12 Then Solomon stood before our Father's altar in the presence of the whole assembly of Israel and spread out his hands. Sa’an nan Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa sama.
13 Solomon had made a bronze platform about seven and a half feet long, seven and a half feet wide, four and a half feet high, and set it in the middle of the court. He stood on it, knelt before the whole assembly of Israel, and spread his hands toward heaven. Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama.
14 He said, O my Father, God of Israel, no Father is like you in heaven or on earth, keeping covenant and showing loyal love to your servants who walk before you wholeheartedly. Ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama da kuma ƙasa, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna tare da bayinka waɗanda suke cin gaba da zuciya ɗaya a hanyarka.
15 You kept your promise to your servant David my father; what you spoke with your mouth you fulfilled with your hand today. Ka kiyaye alkawarinka ga bawanka Dawuda mahaifina; da bakinka ka yi alkawari kuma da hannunka ka cika shi, yadda yake a yau.
16 So now, my Father, God of Israel, keep for your servant David my father what you promised: "You will never lack a man before me on Israel's throne, if only your sons watch their way to walk in my law, as you have walked before me." “Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’
17 And now, my Father, God of Israel, let the word you spoke to your servant David be confirmed. Yanzu kuwa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi alkawarta wa bawanka Dawuda yă cika.
18 But will our Father really live with people on earth? The heavens and highest heavens can't hold you—how much less this house I built. “Amma tabbatacce Allah zai zauna a duniya tare da mutane? Sammai, har ma da saman sammai, ba za su iya riƙe ka ba. Balle wannan haikalin da na gina!
19 Yet hear the prayer of your servant and his plea, O my Father, and hear the cry and prayer your servant prays before you. Duk da haka ka mai da hankali ga addu’ar bawanka da kuma roƙo don jinƙai, ya Ubangiji, Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka.
20 May your eyes be open toward this house day and night, toward the place where you said you'd put your name, to hear the prayer your servant prays toward this place. Bari idanunka su buɗu ta wajen wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce za ka sa Sunanka a can. Bari ka ji addu’ar da bawanka ke yi ta wajen wannan wuri.
21 Hear your servant's and your people Israel's pleas when they pray toward this place. Hear from heaven, your dwelling; and when you hear, forgive. Ka ji roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a suna duban wajen wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka; kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta.
22 If a man sins against his neighbor and must swear an oath, and he comes and swears his oath before your altar in this house, “Sa’ad da mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi aka kuma bukaci ya yi rantsuwa, ya kuma zo ya rantse a gaban bagadenka a cikin wannan haikali,
23 then hear from heaven and act. Judge your servants: pay back the guilty for their deeds, and clear the righteous, rewarding them by their righteousness. sai ka ji daga sama ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, kana sāka wa mai laifi ta wurin kawo a kansa hakkin abin da ya yi. Ka nuna cewa marar laifi ba shi da laifi, ta haka a fiffita rashin laifinsa.
24 If your people Israel, defeated by enemies for sinning against you, turn back to praise your name, pray, and plead with you in this house, “Sa’ad da an ci mutanenka Isra’ila a yaƙi ta wurin abokin gāba domin sun yi maka zunubi kuma sa’ad da suka juya suka furta sunanka, suna addu’a suka kuma yin roƙe-roƙe a gabanka a wannan haikali,
25 then hear from heaven, forgive the sin of your people Israel, and bring them back to the land you gave to them and their ancestors. sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin mutanenka Isra’ila ka kuma dawo da su zuwa ƙasar da ka ba su da kuma kakanninsu.
26 When the sky is shut with no rain because they sinned against you, if they pray toward this place, praise your name, and turn from their sin when you make them suffer, “Sa’ad da sammai suka rufu ba kuwa ruwan sama saboda mutanenka sun yi maka zunubi, sa’ad da kuwa suka yi addu’a suna duban waje wannan wuri suka kuma furta sunanka suka juye daga zunubinsu domin ka azabta su,
27 then hear from heaven, forgive your servants' sin, your people Israel, when you teach them the good path to walk, and send rain on your land, which you gave your people as their inheritance. sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace da za su yi zama, ka kuma aika ruwan sama a ƙasar da ka ba mutanenka gādo.
28 If famine, plague, blight, mildew, locust, or caterpillar strikes the land; if enemies besiege them in their towns—whatever plague or sickness comes, “Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko wahala ko fumfuna, ko fāra ko fāra ɗango, ko sa’ad da abokan gāba sun yi musu ƙawanya a kowane daga biranensu, dukan wata masifa ko cutar da za tă zo,
29 whatever prayer or plea anyone or all your people Israel makes, each knowing his own suffering and pain and spreading his hands toward this house, sa’ad da kuwa wani cikin mutanenka Isra’ila ya yi wata addu’a ko roƙo, kowa yana sane a azabarsa da kuma zafinsa, yana buɗe hannuwansa yana duban wajen wannan haikali,
30 then hear from heaven, your home, and forgive, and repay each according to all his ways, since you know his heart—for you alone know every human heart, sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi da kowane mutum gwargwadon duk abin da yake yi, da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan mutane),
31 so they may fear you and walk in your ways as long as they live on the land you gave our ancestors. don su ji tsoronka su kuma yi tafiya a hanyoyinka a kowane lokacin da suke zama a ƙasar da ka ba wa kakanninsu.
32 Also, when a foreigner not of your people Israel comes from a distant land for your great name, your mighty hand, and your outstretched arm—when they come and pray toward this house, “Game da baƙo wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba kuwa amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka mai girma da kuma hannunka mai iko da hannunka mai ƙarfi, sa’ad da ya zo ya yi addu’a yana duban wannan haikali,
33 then hear from heaven where you live, and do all the foreigner asks, so all the earth's peoples may know your name and fear you, as your people Israel do, and know this house I built bears your name. sai ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi duk abin da baƙon ya nemi ka yi, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, su kuma san cewa wannan gidan da na gina na Sunanka ne.
34 If your people go to war against their enemies wherever you send them, and pray to you toward this city you have chosen and the house I built for your name, “Sa’ad da mutanenka suka je yaƙi da abokan gābansu, ko’ina ka kai su, kuma sa’ad da suka yi addu’a gare ka suna duban wannan birnin da ka zaɓa da haikalin nan da na gina domin Sunanka,
35 then hear from heaven their prayer and their plea, and uphold their cause. sai ka ji addu’arsu da kuma roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatarsu.
36 If they sin against you—for no one is without sin—and you are angry with them and hand them to an enemy who takes them captive to a land far or near, “Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wani wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su ka miƙa su ga abokin gāba, wanda ya kai su zaman bauta a ƙasa mai nisa ko kuwa kusa;
37 yet if in the land of their captivity they take it to heart, and turn back and plead with you there, saying, "We have sinned, we did wrong, we acted evilly," Kuma in suka canja zuciya a cikin ƙasar da suke zaman bauta, suka tuba suka roƙe ka a ƙasar zaman bautarsu suka kuma ce, ‘Mun yi zunubi, mu yi abin da ba daidai ba, mu kuwa yi mugunta’;
38 if they turn back to you with all their heart and soul in the land of their captivity where they were taken, and pray toward their land you gave their ancestors, the city you chose, and the house I built for your name, in kuma sun juye gare ka da dukan zuciyarsu da ransu a ƙasar zaman bautarsu inda aka kai su, suka kuma dubi wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, wajen birnin da ka zaɓa da kuma wajen haikalin da na gina domin Sunanka;
39 then hear from heaven, your dwelling place, their prayer and pleas, uphold their cause, and forgive your people who sinned against you. to, daga sama, mazauninka, sai ka ji addu’arsu da kuma roƙe-roƙensu, ka kuwa biya musu bukatunsu. Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi.
40 Now, my Father, let your eyes be open and your ears attentive to the prayer of this place. “Yanzu, Allahna, bari idanunka su buɗu kunnuwanka kuma su saurara ga addu’o’in da ake miƙa a wannan wuri.
41 And now arise, my Father, and come to your resting place, you and the ark of your might. Let your priests, my Father, be clothed with salvation, and let your faithful ones rejoice in your goodness. “Yanzu ka tashi, ya Ubangiji Allah, ka zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka. Bari firistocinka, ya Ubangiji Allah, su sanye ceto, bari tsarkakanka su yi farin ciki cikin alherinka.
42 My Father, do not reject your anointed one. Remember your covenant love for David your servant. Ya Ubangiji Allah, kada ka ƙyale shafaffenka. Ka tuna da ƙauna mai girma da ka alkawarta wa Dawuda bawanka.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]