Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 32 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 After these things and these acts of faithfulness, Sennacherib, Assyria's king, invaded Judah, besieged its fortified cities, meaning to break into them for himself. Bayan dukan abin da Hezekiya ya yi cikin aminci, sai Sennakerib sarkin Assuriya ya zo ya yaƙi Yahuda. Ya yi kwanto wa biranen katanga, yana zato zai ci su da yaƙi wa kansa.
2 When Hezekiah saw that Sennacherib had come, intent on making war against Jerusalem, Sa’ad da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo yana kuma niyya yă yaƙi Urushalima,
3 he consulted his officials and warriors about blocking the springs outside the city, and they helped him. sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi.
4 Many people gathered and blocked all the springs and the stream flowing through the land, asking, "Why should Assyria's kings come and find abundant water?" Sai babban taro suka haɗu suka datse dukan maɓulɓulai da rafuffukan da suke gudu cikin ƙasar. Suka ce “Me zai sa sarakunan Assuriya su zo su sami ruwa barkatai?”
5 He worked hard to rebuild all the broken sections of the wall, raised towers on it, built another wall outside, strengthened the Millo of the city of David, and made abundant weapons and shields. Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.
6 He set war commanders over the people, gathered them at the city gate square, and encouraged them: Ya naɗa manyan hafsoshi a kan mutane, ya tattara su a gabansa a fili a ƙofar birni, ya kuma ƙarfafa su da waɗannan kalmomi.
7 "Be strong and brave. Don't fear or dread Assyria's king and all his horde, for more are with us than with him. “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Assuriya, da mayaƙan nan masu yawa da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.
8 With him is only an arm of flesh; with us is our Father, to help us and fight our battles." The people relied on Hezekiah king of Judah's words. Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.
9 After this, while besieging Lachish with all his forces, Sennacherib king of Assyria sent his servants to Jerusalem, to Hezekiah king of Judah and all Judah there, saying: Daga baya, sa’ad da Sennakerib sarkin Assuriya da dukan mayaƙansa suke kwanto wa Lakish, sai ya aiki hafsoshinsa da wannan saƙo wa Hezekiya sarkin Yahuda da kuma wa dukan mutanen Yahuda waɗanda suke can cewa,
10 "This is what Sennacherib king of Assyria says: On what are you trusting, staying under siege in Jerusalem? “Ga abin da Sennakerib sarkin Assuriya ya ce ga me kake dogara, har da ka dāge cikin Urushalima da aka yi mata kwanto?
11 Isn't Hezekiah deceiving you, surrendering you to die by famine and thirst, when he says, 'The LORD our God will save us from the hand of the king of Assyria'? Ai, Hezekiya, ruɗinku yake yi, don yă sa ku mutu da yunwa da ƙishirwa sa’ad da yake ce muku, ‘Ubangiji Allahnmu zai cece mu daga hannun sarkin Assuriya.’
12 Wasn't it Hezekiah who removed his high places and altars, telling Judah and Jerusalem to worship at one altar and burn offerings there? Hezekiya kansa bai rushe waɗannan masujadan kan tudu da bagadai, yana ce wa Yahuda da Urushalima, ‘Dole ku yi sujada a gaban bagade guda ku kuma ƙone hadayu a kansa ba’?
13 Don't you know what I and my fathers did to all peoples of other lands? Could their nations' gods rescue their lands from my hand? “Ba ku san abin da ni da kuma kakannina suka yi wa dukan mutanen sauran ƙasashe ba? Allolin ƙasashen nan sun taɓa iya ceton ƙasarsu daga hannuna ne?
14 What god of nations my fathers devoted to destruction could save his people from my hand? How then can your God save you from my hand? Wanne a cikin dukan allolin waɗannan ƙasashe da kakannina suka hallaka ya taɓa iya ceton mutanensa daga gare ni? To, yaya Allahnku zai iya cetonku daga hannuna?
15 Don't let Hezekiah deceive or mislead you like this, and don't believe him: no god of any nation or kingdom could rescue his people from my hand or my fathers'—much less will your God rescue you from my hand!" Yanzu fa, kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku yă kuma ɓad da ku haka. Kada ku gaskata shi, gama babu allahn wata ƙasa ko masarautar da ya taɓa iya ceton mutanensa daga hannuna ko kuwa hannun kakannina. Balle har Allahnku yă cece ku daga hannuna!”
16 And his servants spoke still more against our Father and against his servant Hezekiah. Hafsoshin Sennakerib suka ci gaba da maganar banza wa Ubangiji Allah da kuma a kan bawansa Hezekiya.
17 Sennacherib also wrote letters insulting our Father, the God of Israel, speaking against him: "The nations' gods did not rescue their people from my hand; neither will Hezekiah's God rescue his people from my hand." Sarki ya kuma rubuta wasiƙu yana zagin Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana faɗin wannan a kansa, “Kamar yadda sauran allolin mutanen sauran ƙasashe ba su iya kuɓutar da mutane daga hannuna ba, haka Allahn Hezekiya ba zai kuɓutar da mutanensa daga hannuna ba.”
18 They shouted loudly in Judah's language to Jerusalem's people on the wall, to frighten and terrify them, to seize the city. Sa’an nan suka yi magana da ƙarfi cikin Yahudanci wa mutanen Urushalima waɗanda suke kan katanga, don su firgita su, su kuma sa su ji tsoro don su iya cin birnin.
19 They spoke of Jerusalem's God like the gods of earth's peoples, the work of human hands. Suka yi magana game da Allah na Urushalima yadda suka yi game da allolin sauran mutanen duniya, aikin hannuwan mutane.
20 Then King Hezekiah and the prophet Isaiah son of Amoz prayed about this, crying out to heaven. Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz suka yi kuka cikin addu’a ga sama game da wannan.
21 So our Father sent an angel who killed every mighty warrior, commander, and officer in the Assyrian king's camp. Sennacherib returned home in disgrace, and when he entered his god's temple, some of his own sons killed him there with the sword. Sai Ubangiji ya aiki mala’ika, wanda ya karkashe dukan jarumawa da shugabanni da kuma hafsoshi a sansanin sarkin Assuriyawa. Saboda haka sai sarkin Assuriya ya janye zuwa ƙasarsa da kunya. Da ya shiga haikalin Allahnsa, sai waɗansu a cikin ’ya’yansa maza suka yanka shi da takobi.
22 So our Father saved Hezekiah and Jerusalem's people from the hand of Sennacherib king of Assyria and all others, and he cared for them on every side. Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mutanen Urushalima daga hannun Sennakerib sarkin Assuriya da kuma daga hannun dukan sauran. Ya magance su a kowane gefe.
23 Many brought gifts to our Father in Jerusalem, and treasures to Hezekiah king of Judah; afterward all nations honored Hezekiah highly. Yawanci mutane suka kawo hadayun ƙonawa zuwa Urushalima wa Ubangiji da kuma kyautai masu daraja wa Hezekiya sarkin Yahuda. Daga lokacin zuwa gaba dukan ƙasashe suka girmama shi.
24 In those days Hezekiah grew sick to death; he prayed to our Father, who answered, giving him a sign. A kwanakin nan Hezekiya ya yi ciwo, ya yi kusan mutuwa. Sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wanda ya amsa masa ya kuma ba shi alama.
25 But Hezekiah didn't repay the good done him; his heart grew proud, so anger came on him and on Judah and Jerusalem. Amma zuciyar Hezekiya ta yi girman kai, bai kuwa yi amfani da alherin da aka nuna masa ba, saboda haka fushin Ubangiji ya sauko a kansa da kuma a kan Yahuda da Urushalima.
26 Hezekiah humbled himself for his proud heart, he and Jerusalem's people, so our Father's wrath didn't reach them in Hezekiah's days. Sai Hezekiya ya tuba daga girma kan zuciyarsa, haka ma mutanen Urushalima; saboda haka fushin Ubangiji bai zo a kansu a kwanakin Hezekiya ba.
27 Hezekiah had great wealth and honor. He built storerooms for silver, gold, gems, spices, shields, and other valuables, Hezekiya mai arziki da girma ne ƙwarai, ya kuma yi baitulmali domin azurfa da zinariyarsa da kuma domin duwatsu masu daraja, kayan yaji, garkuwoyi da kuma domin dukan kayayyaki masu daraja nasa.
28 storerooms for the harvest of grain, new wine, and oil; stalls for all kinds of livestock; pens for flocks. Ya kuma yi gine-gine domin ajiyar hatsi, sabon ruwa inabi da mai; ya kuma yi wuraren ajiyar kowane irin shanu dabam-dabam, da kuma turke domin tumaki.
29 He built cities for himself and gained huge flocks and herds, for our Father gave him very great wealth. Ya gina ƙauyuka ya kuma samo shanu da garkuna masu yawa, gama Allah ya ba shi arziki mai yawa sosai.
30 Hezekiah stopped Gihon's upper outlet and directed the water down the west side of David's city. He succeeded in all he did. Hezekiya ne ya datse ruwan bisa na maɓulɓular Gihon, ya sa ruwan ya gangara zuwa gefe yamma na Birnin Dawuda. Ya yi nasara a kome da ya yi.
31 When Babylon's rulers sent envoys to him asking about the land's sign, our Father left him to himself, to test him and to know all in his heart. Amma da masu mulkin Babilon suka aika da jakadu su tambaye shi game alamar da ta faru a ƙasar, Allah ya rabu da shi don yă gwada shi don yă kuma san kome da yake cikin zuciyarsa.
32 Hezekiah's remaining acts and faithful deeds are written in the vision of Isaiah the prophet, son of Amoz, in the Book of the Kings of Judah and Israel. Sauran ayyukan mulkin Hezekiya da kuma kyawawa ayyukansa, suna a rubuce a cikin wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.
33 Hezekiah slept with his ancestors, buried in the upper tombs of David's sons. All Judah and Jerusalem's residents honored him at death. His son Manasseh succeeded him. Hezekiya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a kan tudu inda makabartan zuriyar Dawuda suke. Dukan Yahuda da kuma mutanen Urushalima suka girmama shi sa’ad da ya mutu. Sai Manasse ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]