Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 31 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 When this ended, all Israel present went out to the towns of Judah, smashed the sacred pillars, cut down the Asherah poles, and tore down the high places and altars throughout Judah, Benjamin, Ephraim, and Manasseh, destroying them completely. Then all Israel returned to their towns, each to his own property. Sa’ad da aka gama dukan wannan, sai Isra’ilawan da suke can suka fita zuwa garuruwan Yahuda, suka rurrushe keɓaɓɓun duwatsu suka kuma farfashe ginshiƙan Ashera. Suka rurrushe masujadan kan tudu da bagadai, ko’ina a Yahuda da Benyamin da kuma cikin Efraim da Manasse. Bayan sun rurrushe dukansu, sai Isra’ilawa suka koma garuruwansu, kowanne zuwa mahallinsa.
2 Hezekiah assigned the priests and Levites to their divisions, each by his service, priests and Levites alike, for burnt offerings and peace offerings, to serve, give thanks, and praise in the gates of our Father's camps. Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi-kashi, kowanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima, su yi godiya, su kuma rera yabai a ƙofofin mazaunin Ubangiji.
3 The king gave from his own wealth for the burnt offerings—morning and evening burnt offerings, and those for Sabbaths, new moons, and appointed feasts—as written in our Father's law. Sarki ya ba da taimako daga mallakarsa domin hadayun ƙonawa, safe da yamma da kuma don hadayun ƙonawa a Asabbatai, Sabon Wata da kuma ƙayyadaddun bukukkuwa kamar yadda yake a rubuce a cikin Dokar Ubangiji.
4 He told Jerusalem's residents to give the priests' and Levites' portion, so they could devote themselves to our Father's law. Ya umarci mutanen da suke zama a Urushalima su ba da rabon da yake na firistoci da Lawiyawa, don su ƙwallafa ransu ga Dokar Ubangiji.
5 As soon as the order spread, Israelites abundantly gave firstfruits of grain, new wine, oil, honey, and all the field's produce, and brought in the tenth of everything abundantly. Nan da nan aka baza umarnin, sai Isra’ilawa suka bayar ’ya’yan farin hatsinsu, sabon ruwan inabi, mai da kuma zuma da dukan abin da gona ta bayar, hannu sake. Suka kawo zakan kowane abu da yawa.
6 The Israelites and Judahites living in Judah's towns also brought the tenth of cattle and sheep, and the tenth of what was dedicated to our Father, piling them in heaps. Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi.
7 They began piling the heaps in the third month, finishing in the seventh. Sun fara yin haka a wata na uku, suka kuma gama a wata na bakwai.
8 Hezekiah and the officials came, saw the heaps, and blessed our Father and his people Israel. Sa’ad da Hezekiya da fadawansa suka zo suka ga tsibin, sai suka yabi Ubangiji, suka kuma albarkace mutanensa Isra’ila.
9 Hezekiah asked the priests and Levites about the heaps. Hezekiya ya tambayi firistoci da Lawiyawa game da tsibin;
10 Azariah the chief priest, of Zadok's house, answered him, "Since people began bringing contributions into our Father's house, we've eaten well with plenty remaining, for our Father blessed his people, leaving this large surplus." sai Azariya babban firist, daga iyalin Zadok ya amsa, “Tun daga lokacin da mutane suka fara kawo taimakonsu ga haikalin Ubangiji, muna da isashe don abinci da kuma da yawa da za mu rage, domin Ubangiji ya albarkaci mutanensa, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”
11 Then Hezekiah ordered them to prepare storerooms in the house of our Father, and they prepared them. Hezekiya ya ba da umarni a shirya ɗakunan ajiya a haikalin Ubangiji, aka kuwa yi haka.
12 They faithfully brought in the contributions, the tenth, and dedicated gifts. Conaniah the Levite led them; Shimei his brother was second. Sa’an nan cikin aminci suka kawo taimako, zakka da keɓaɓɓun kyautai. Konaniya, wani Balawe, shi ne ke lura da waɗannan abubuwa, kuma ɗan’uwansa Shimeyi shi ne na biye da shi.
13 Jehiel, Azaziah, Nahath, Asahel, Jerimoth, Jozabad, Eliel, Ismachiah, Mahath, and Benaiah oversaw, under Conaniah and his brother Shimei, appointed by King Hezekiah and Azariah, chief officer of our Father's house. Yehiyel, Azaziya, Nahat, Asahel, Yerimot, Yozabad, Eliyel, Ismakiya, Mahat da Benahiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimeyi ɗan’uwansa, waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban haikalin Allah suka naɗa.
14 Kore son of Imnah, the Levite gatekeeper toward the east, oversaw the voluntary offerings to our Father, distributing our Father's contributions and the most holy gifts. Kore ɗan Imna Balawe, mai tsaron Ƙofar Gabas, shi ne yake lura da baikon yardan ran da aka yi wa Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.
15 Under him, Eden, Miniamin, Jeshua, Shemaiah, Amariah, and Shecaniah served faithfully in the priestly towns, distributing to fellow priests by divisions, great and small alike, Eden, Miniyamin, Yeshuwa, Shemahiya, Amariya da Shekaniya sun taimake shi da aminci a cikin garuruwan firistoci, suna ba da rabo wa ’yan’uwansu firistoci bisa ga sassansu, tsofaffi da yara.
16 besides giving to those registered by genealogy, males three and up—all entering the house of our Father for daily duty—for their service by office and division. Bugu da ƙari, suka ba da rabo ga maza ’yan shekaru uku ko fiye waɗanda sunayensu suna a tarihin zuriya, dukan waɗanda ba za su iya shiga haikalin Ubangiji su yi ayyukansu na kullum ba, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.
17 Priests were registered by clans; Levites twenty and up, by duty and division. Suka kuma ba da rabo ga firistocin da aka rubuta ta iyalansu cikin tarihin zuriya, haka kuma ga Lawiyawa masu shekara ashirin ko fiye, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.
18 They were registered with all their little ones, wives, sons, and daughters—the whole community—for they faithfully dedicated themselves in holiness. Suka haɗa da dukan ƙanana ’ya’yansu, mata, da kuma ’ya’ya maza da ’ya’ya mata, al’umma gaba ɗaya da aka jera a waɗannan tarihin zuriya. Gama sun yi aminci cikin tsarkake kansu.
19 For Aaron's priestly descendants living in the pasture-fields around their towns, men were named in each and every town to give shares to every male priest and all Levites listed by genealogy. Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa ’ya’yan Haruna, firist, maza, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namijin da aka rubuta na Lawiyawa, rabonsa.
20 Hezekiah did this throughout all Judah. He did what was good, right, and faithful before our Father. Abin da Hezekiya ya yi ke nan ko’ina a Yahuda, yana yin abin da yake da kyau, daidai da kuma mai aminci a gaban Ubangiji Allahnsa.
21 In all he undertook—serving the house of our Father, keeping the law and command, seeking our Father—he gave his whole heart, and thrived. Cikin kome da ya yi cikin hidimar haikalin Allah, cikin biyayya kuma ga doka da umarnai, ya nemi Allahnsa, ya kuma yi aiki gabagadi. Ta haka kuwa ya yi nasara.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]