Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 30 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Hezekiah sent word to all Israel and Judah, and wrote letters to Ephraim and Manasseh, to come to the house of our Father in Jerusalem to keep the Passover to our Father, the God of Israel. Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
2 The king, his officials, and the whole assembly in Jerusalem had decided to keep the Passover in the second month, Sarki da fadawansa da dukan taro a Urushalima suka yanke shawara su yi Bikin Ƙetarewa a wata na biyu.
3 since they could not keep it then, because too few priests had made themselves holy and the people had not gathered at Jerusalem. Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.
4 The plan seemed right to the king and to all the assembly, Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron.
5 so they sent a proclamation throughout Israel, from Beersheba to Dan, that the people should come to Jerusalem to keep the Passover to our Father, the God of Israel; for they had not kept it together in great numbers as written. Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.
6 The couriers went through all Israel and Judah with letters from the king and his officials, ordered by the king: "Children of Israel, return to our Father, the God of Abraham, Isaac, and Israel, so he may return to the remnant of you who survived and escaped the power of the kings of Assyria. Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.
7 Do not be like your fathers and brothers, who were unfaithful to our Father, the God of their fathers, so he made them a desolation, as you see. Kada ku zama kamar iyayenku da ’yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani.
8 Don't be stubborn like your fathers; give yourselves to our Father and come to his sanctuary, which he dedicated forever, and serve your Father, so his fierce anger turns from you. Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi yă juye daga gare ku.
9 For if you return to our Father, your brothers and your children will find compassion from their captors and return to this land. For your Father is gracious and merciful; he will not turn his face from you if you return to him." In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama ’yan’uwanku da ’ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi.”
10 The couriers went from city to city through Ephraim and Manasseh to Zebulun, but the people laughed at them and mocked them. ’Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a.
11 Even so, some from Asher, Manasseh, and Zebulun humbled themselves and came to Jerusalem. Duk da haka, waɗansu mutanen Asher, Manasse da Zebulun suka ƙasƙantar da kansu suka tafi Urushalima.
12 The hand of our Father was also on Judah, giving them one heart to do what the king and officials commanded by the word of our Father. Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don yă ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji.
13 A very large assembly gathered at Jerusalem to keep the Feast of Bread Without Yeast in the second month. Taron mutane mai girma ya haɗu a Urushalima don Bikin Burodi Marar Yisti a wata na biyu.
14 They set to work and removed the altars in Jerusalem, and they took away all the incense altars, throwing them into the Kidron Valley. Suka kawar da bagadai a Urushalima suka fid da bagadan turare suka zubar da su a Kwarin Kidron.
15 They slaughtered the Passover lamb on the fourteenth of the second month. The priests and Levites were ashamed, so they dedicated themselves and brought burnt offerings to the house of our Father. Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.
16 They stood at their posts by custom, as the Law of Moses the man of God requires; the priests sprinkled the blood the Levites handed them. Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su.
17 Many in the assembly had not dedicated themselves, so the Levites were in charge of killing the Passover lambs for everyone unclean, to dedicate them to our Father. Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka ’yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba.
18 A large number of the people, many from Ephraim, Manasseh, Issachar, and Zebulun, had not purified themselves, yet ate the Passover, though not as written. But Hezekiah prayed for them: "May our good Father pardon everyone, Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, “Bari Ubangiji, wanda yake nagari, yă gafarta wa kowa
19 who sets his heart to seek our Father, the God of his fathers, though not clean by the sanctuary's rules." wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki.”
20 And our Father listened to Hezekiah and healed the people. Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya ya kuma warkar da mutane.
21 The Israelites in Jerusalem kept the Feast of Bread Without Yeast seven days with great joy, and day by day the Levites and priests praised our Father with loud instruments resounding to him. Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.
22 Hezekiah spoke encouragingly to all the Levites skilled in serving our Father. For seven days they ate their festival share, offering peace offerings and giving thanks to our Father, the God of their fathers. Hezekiya ya yi magana mai ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna ganewar fasaha a hidimar Ubangiji. Kwana bakwai suka ci rabonsu da aka tsara, suka miƙa hadayun salama, suka kuma yabi Ubangiji Allah na kakanninsu.
23 Then the whole assembly agreed to keep the feast another seven days, and they kept it seven more days with joy. Dukan mutanen suka yarda su ƙara kwana bakwai kuma, sai suka ci gaba da bikin cikin farin ciki har waɗansu kwana bakwai kuma.
24 Hezekiah king of Judah gave the assembly 1,000 bulls and 7,000 sheep, and the officials gave 1,000 bulls and 10,000 sheep, and many priests dedicated themselves. Hezekiya sarkin Yahuda ya tanada bijimai dubu ɗaya da tumaki da kuma awaki dubu bakwai wa taron, fadawa kuma suka tanada musu bijimai dubu da kuma tumaki da awaki dubu goma. Firistoci masu yawa suka tsarkake kansu.
25 All Judah's assembly rejoiced, with the priests, the Levites, the whole assembly that came from Israel, and the foreigners from Israel's land and those living in Judah. Taron gaba ɗaya na Yahuda suka yi farin ciki, tare da firistoci da kuma Lawiyawa da dukan waɗanda suka taru daga Isra’ila, har ma da baƙi waɗanda suka zo daga Isra’ila da waɗanda suke zama a Yahuda.
26 Great joy filled Jerusalem, for nothing like this had happened there since the days of Solomon son of David, king of Israel. Aka yi farin ciki mai girma a Urushalima, gama tun zamanin Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila, ba a taɓa yin wani abu kamar haka a Urushalima ba.
27 The priests and Levites rose to bless the people, and their voice was heard; their prayer reached his holy home in heaven. Firistoci da Lawiyawa suka tsaya suka albarkace mutane, Allah kuma ya ji su, gama addu’arsu ya kai sama, mazauninsa mai tsarki.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]