Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 33 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Manasseh was twelve years old when he became king, and he reigned fifty-five years in Jerusalem. Manasse yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyar.
2 He did evil in our Father's sight, like the detestable things of the nations our Father drove out before the Israelites. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji, yana bin ayyukan banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.
3 He rebuilt the high places his father Hezekiah had torn down, built altars to the Baals, made Asherah poles, and he bowed down to all the forces of heaven and worshiped them. Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada.
4 He built altars in our Father's house, where our Father said, "In Jerusalem my name remains forever." Ya gina bagadai cikin haikalin Ubangiji, waɗanda Ubangiji ya ce, “Sunana zai kasance cikin Urushalima har abada.”
5 He built altars to all heaven's forces in both courts of the house of our Father. Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari.
6 In the Valley of Ben-Hinnom he sacrificed his sons in the fire, practiced fortune-telling, omens, and witchcraft, and consulted mediums and spiritists. He did great evil before our Father, provoking his anger. Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.
7 He set the carved image he made in the house of our Father, of which our Father said to David and his son Solomon, "In this house and in Jerusalem, which I chose from all the tribes of Israel, I will put my name forever. Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon, “Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.
8 I will never again remove Israel from the land I gave your ancestors, if only they carefully keep all I commanded them—the whole law, decrees, and rules through Moses." Ba zan ƙara bari ƙafafun Isra’ilawa su bar ƙasar da na ba wa kakanninku ba, in dai suka yi hankali ga yin kome da na umarce su game da duka dokoki, ƙa’idodi da kuma farillai da na bayar ta wurin Musa.”
9 But Manasseh led Judah and Jerusalem's people astray, doing more evil than the nations our Father destroyed before Israel. Amma Manasse ya sa Yahuda da mutanen Urushalima suka kauce, har suka aikata mugunta fiye da al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.
10 Our Father spoke to Manasseh and his people, but they would not listen. Ubangiji ya yi magana da Manasse da mutanensa, amma ba su kula ba.
11 So our Father brought the army commanders of Assyria's king against them; they captured Manasseh with hooks, bound him in bronze shackles, and took him to Babylon. Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon.
12 Distressed, he sought our Father's favor, humbling himself deeply before the God of his fathers. Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.
13 He prayed to him, and our Father, moved by his plea, heard his cry for mercy, brought him back to Jerusalem, to his kingdom. Then Manasseh knew that our Father is God. Da ya yi addu’a gare shi, sai Ubangiji ya taɓu da tubansa, ya kuma saurari roƙonsa; saboda haka ya dawo da shi Urushalima da kuma zuwa mulkinsa. Sa’an nan Manasse ya san cewa Ubangiji shi ne Allah.
14 Afterward he rebuilt the City of David's outer wall, west of Gihon in the valley to the Fish Gate entrance, around the Ophel, raising it very high. He posted army commanders in all Judah's fortified cities. Daga baya ya sāke gina katangar waje na Birnin Dawuda, yamma da maɓulɓular Gihon a cikin kwari, har zuwa mashigin Ƙofar Kifi, ya kuma kewaye tudun Ofel; ya yi ta da tsayi sosai. Ya sa hafsoshin mayaƙa cikin dukan biranen katanga a Yahuda.
15 He removed the foreign gods and idol from our Father's house, with all the altars he'd built on the temple mount and in Jerusalem, and threw them out of the city. Ya fid da baƙin alloli, ya kuma fid da siffofi daga haikalin Ubangiji, haka ma dukan bagadan da ya gina a kan tudun haikali da kuma cikin Urushalima, ya zubar da su a bayan birni.
16 He rebuilt our Father's altar, sacrificed peace and thank offerings on it, and commanded Judah to serve our Father, the God of Israel. Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji ya kuma miƙa hadayun salama da kuma hadayun godiya a bagaden, ya kuma faɗa wa Yahuda su bauta wa Ubangiji, Allah na Isra’ila.
17 The people, however, still sacrificed at the high places, but only to our Father, their God. Mutane dai suka ci gaba da miƙa hadayu a masujadai kan tudu, amma wa Ubangiji Allahnsu kaɗai.
18 Manasseh's other acts, his prayer to our Father, and the seers' words to him in the name of our Father, the God of Israel, are in the records of Israel's kings. Sauran ayyukan mulkin Manasse, haɗe da addu’arsa ga Allahnsa da kuma kalmomin da mai duba ya yi masa cikin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, suna a rubuce cikin tarihin sarakunan Isra’ila.
19 His prayer, how our Father was moved by him, all his sin and unfaithfulness, and the places where he built high places, set up Asherah poles, and carved images before he humbled himself—all recorded in the seers' records. Addu’arsa da yadda Allah ya taɓu ta wurin tubansa, da kuma dukan zunubansa da rashin biyayyarsa, da wuraren da ya gina masujadan kan tudu ya kuma kafa ginshiƙan Ashera da gumaka kafin ya ƙasƙantar da kansa, duka suna a rubuce cikin tarihin mai duba.
20 Manasseh died and was buried in his palace. And his son Amon became king in his place. Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a fadansa. Sai Amon ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
21 Amon was twenty-two years old when he became king, and he reigned two years in Jerusalem. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki a Urushalima shekara biyu.
22 He did evil before our Father, as his father Manasseh had. Amon sacrificed to all the carved images Manasseh made and worshiped them. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi. Amon ya bauta ya kuma miƙa hadayu ga dukan gumakan da Manasse ya yi.
23 Unlike his father Manasseh, he did not humble himself before our Father; instead Amon multiplied his guilt. Amma ba kamar mahaifinsa Manasse ba, bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji ba; Amon ya ƙara laifinsa.
24 Amon's servants conspired against him and killed him in his palace. Fadawan Amon sukan yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a fadansa.
25 The people of the land killed all who conspired against King Amon and made his son Josiah king in his place. Sa’an nan mutanen ƙasar suka kashe dukan waɗanda suka yi wa Sarki Amon maƙarƙashiya, suka naɗa Yosiya ɗansa sarki a maimakonsa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]