Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 13 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In the eighteenth year of King Jeroboam, Abijah became king of Judah. A shekara ta sha takwas ta sarautar Yerobowam, Abiya ya zama sarkin Yahuda,
2 He reigned three years in Jerusalem; his mother was Micaiah, Uriel of Gibeah's daughter. Abijah and Jeroboam went to war. ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru uku. Sunan mahaifiyarsa Mikahiya ce, ’yar Uriyel na Gibeya. Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Abiya da Yerobowam.
3 Abijah joined battle with an army of 400,000 chosen warriors, mighty in war; Jeroboam lined up against him with 800,000 chosen, mighty warriors. Abiya ya tafi yaƙi tare da mayaƙa dubu ɗari huɗu jarumawa, Yerobowam kuwa ya ja dāgār yaƙi a kan Abiya da mayaƙa dubu ɗari takwas jarumawa.
4 Abijah stood on Mount Zemaraim in Ephraim's hill country and said, "Hear me, Jeroboam and all Israel! Abiya ya tsaya a Dutsen Zemarayim, a ƙasar tudu ta Efraim ya ce, “Yerobowam da dukan Isra’ila, ku saurare ni!
5 Don't you know our Father, the God of Israel, gave David and his sons Israel's throne forever, by a covenant of salt? Ba ku san cewa Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda da zuriyarsa har abada ta wurin alkawarin gishiri ba?
6 But Jeroboam son of Nebat—a servant of Solomon son of David—rose and rebelled against his master. Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, ma’aikacin Solomon ɗan Dawuda, ya tayar wa maigidansa,
7 Worthless men gathered around him, defying Solomon's son Rehoboam, young and timid, unable to resist them. sai ya tara wa kansa ’yan iska da mugayen mutane suka yi gāba da Rehobowam ɗan Solomon. Rehobowam lokacin kuwa ba shi da wayo, don haka bai iya tsai da su ba.
8 Now you think you can resist our Father's kingdom in David's sons' hands, since you're a huge crowd with the golden calves Jeroboam made as your gods. “Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.
9 Haven't you driven out our Father's priests, Aaron's sons and the Levites, and made your own priests like other nations? Anyone who comes with a young bull and seven rams can become a priest of things that aren't gods. Ba ku ne kuka kori firistocin Ubangiji, ’ya’yan Haruna maza, da Lawiyawa kuka kuma zaɓi firistocinku kamar yadda sauran al’ummai suke yi ba? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don yă tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.
10 But our Father is ours, and we haven't abandoned him. The priests serving him are Aaron's sons, and the Levites are at their work. “Gare mu kuwa, Ubangiji shi ne Allah, kuma ba mu yashe shi ba. Firistocin da suke bauta wa Ubangiji ’ya’yan Haruna maza ne, Lawiyawa ne kuwa suke taimakonsu.
11 Every morning and evening they burn to our Father burnt offerings and fragrant incense; they set rows of bread on the pure gold table and tend the gold lampstand, lit every evening. We keep our Father's charge, but you have abandoned him. Kowace safiya da kowace yamma sukan miƙa hadayun ƙonawa da turare mai ƙanshi ga Ubangiji. Sukan shirya burodi a tsarkaken tebur mai tsabta, sukan kuma ƙuna fitilu a alkukai kowace yamma. Muna kiyaye ƙa’idodin Ubangiji Allahnmu. Amma ku kun yashe shi.
12 Look, our Father is with us at our head, and his priests have trumpets to sound alarm against you. Israelites, do not fight our Father, the God of your ancestors, for you will not prevail." Allah yana tare da mu; shi ne shugabanmu. Firistocinsa tare da ƙahoni za su busa kirarin yaƙi a kanku. Mutanen Isra’ila, kada ku yi yaƙi da Ubangiji Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”
13 Jeroboam had sent an ambush around, to come from behind them; his forces faced Judah, the ambush behind them. To, fa, Yerobowam ya aiki mayaƙa su zagaya daga baya, domin yayinda yake a gaban Yahuda, sai ’yan kwanto su kasance a bayansu.
14 Judah turned, saw battle facing them front and back, cried to our Father; the priests blew the trumpets. Yahuda ya juya sai ya ga cewa ana yaƙe su gaba da baya. Sai suka yi kuka ga Ubangiji. Firistoci suka busa ƙahoni
15 Judah's men shouted the war cry, and as they shouted, our Father struck Jeroboam and all Israel before Abijah and Judah. mutanen Yahuda kuwa suka tā da kirarin yaƙi. Da ji kirarin yaƙi, Allah ya fatattake Yerobowam da dukan Isra’ila a gaban Abiya da Yahuda.
16 The people of Israel fled before Judah, and our Father handed them over to Judah. Isra’ilawa suka gudu a gaban Yahuda, Allah kuwa ya bashe su a hannuwansu.
17 Abijah and his army struck them a heavy blow; 500,000 chosen men of Israel fell dead. Abiya da mutanensa suka kashe su sosai, har mutum dubu ɗari biyar suka mutu a cikin jarumawan Isra’ila.
18 So Israel was humbled then, and Judah prevailed because they relied on our Father, God of their ancestors. Aka cinye mutanen Isra’ila a wannan lokaci, mutanen Yahuda kuwa suka yi nasara domin sun dogara ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
19 Abijah chased Jeroboam, capturing cities from him—Bethel and its villages, Jeshanah and its villages, Ephron and its villages. Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi.
20 Jeroboam never regained his strength during Abijah's lifetime, and our Father struck him down, and he died. Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu.
21 But Abijah grew strong. He married fourteen wives and had twenty-two sons and sixteen daughters. Amma Abiya ya ƙara ƙarfi. Ya auri mata goma sha huɗu, ya kuma kasance da ’ya’ya maza ashirin da biyu da kuma ’ya’ya mata goma sha shida.
22 The rest of Abijah's acts, his ways and sayings, are written in the prophet Iddo's commentary. Sauran ayyukan sauratar Abiya, abin da ya yi da abin da ya faɗa, a rubuce suke a cikin rubuce-rubucen annabi Iddo.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]