Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 14 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Abijah rested with his ancestors; they buried him in the City of David. His son Asa became king, and the land had peace ten years. Abiya kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki, a zamaninsa kuma ƙasar ta zauna lafiya na shekara goma.
2 Asa did what was good and right in the sight of our Father. Asa ya yi abin da yake da kyau da kuma daidai a gaban Ubangiji Allahnsa.
3 He removed the foreign altars and high places, smashed the sacred pillars, and cut down the Asherah poles. Ya kawar da baƙin bagade da masujadai bisa tudu, ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya kuma sassare ginshiƙan Ashera.
4 He commanded Judah to seek our Father, the God of their ancestors, and keep the law and commandment. Ya umarci Yahuda su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kuma yi biyayya da dokoki da kuma umarnansa.
5 He also removed the high places and incense altars from all Judah's cities, and the kingdom was at peace under him. Ya kawar da masujadan kan tudu da bagadan turare a kowane gari a Yahuda, masarautar kuwa ta zauna lafiya a ƙarƙashinsa.
6 He built fortified cities in Judah, for the land was at peace. He fought no war those years, because our Father gave him rest. Ya gina biranen katanga na Yahuda, da yake ƙasar tana zaman lafiya. Babu wanda yake yaƙi da shi a waɗannan shekaru, gama Ubangiji ya ba shi hutu.
7 He told Judah, "Let us build these cities and surround them with walls, towers, gates, and bars. The land is still ours, because we sought our Father; we sought him, and he gave us rest all around." So they built and thrived. Ya ce wa Yahuda, “Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe.” Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara.
8 Asa had an army of 300,000 from Judah with large shields and spears, and 280,000 from Benjamin with shields and bows—all mighty warriors. Asa ya kasance da mayaƙa dubu ɗari uku daga Yahuda, kintsatse da manyan garkuwoyi da māsu, da kuma mayaƙa dubu ɗari biyu da dubu tamanin daga Benyamin, riƙe da ƙananan garkuwoyi da kuma baka. Dukan waɗannan jarumawa ne ƙwarai.
9 Zerah the Cushite marched against them with a million troops and 300 chariots, advancing to Mareshah. Zera mutumin Kush ya taka ya fita don yă yaƙe su da babban runduna da kuma kekunan yaƙi ɗari uku, ya kuma zo har Maresha.
10 Asa marched out against him, and they lined up for battle in the Valley of Zephathah at Mareshah. Asa ya fita don yă ƙara da shi, suka ja dāgā yaƙi a Kwarin Zefata kusa da Maresha.
11 Then Asa cried to our Father his God: "Father, only you can help the powerless against the mighty. Help us, our God, for we rely on you, and in your name we face this vast horde. You are our God; let no mere man prevail against you." Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”
12 So our Father struck down the Cushites before Asa and before Judah, and the Cushites fled. Ubangiji fa ya bugi mutanen Kush a gaban Asa da Yahuda. Mutanen Kush suka gudu,
13 Asa and his people pursued them to Gerar, and the Cushites fell until none survived, for they were shattered before our Father and his army. Judah's men carried off great plunder. Asa kuwa da mayaƙansa suka bi su har Gerar. Mutanen Kush suka mutu a ranan nan har ba a iya ƙidaya, aka buge su a gaban Ubangiji da rundunansa. Mutanen Yahuda suka kwashi ganima sosai.
14 They struck down all the cities around Gerar, for the terror of our Father had fallen on them. They looted all the cities, since much plunder was in them. Suka hallaka dukan ƙauyukan kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka kwashi ganima na dukan ƙauyukan nan, da yake akwai ganima sosai a can.
15 They also attacked the herdsmen's tents, carried off many sheep and camels, and returned to Jerusalem. Suka kuma yaƙi sansanin makiyaya suka kwashe tumaki da awaki da raƙuma. Suka koma Urushalima.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]