Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 12 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 When Rehoboam's reign was secure and strong, he abandoned our Father's law, and all Israel with him. Bayan mulkin Rehobowam ya kahu kamar sarki ya kuma yi ƙarfi, shi da dukan Isra’ila suka yi biris da dokar Ubangiji.
2 In Rehoboam's fifth year, because they were unfaithful to our Father, Shishak king of Egypt attacked Jerusalem. Domin sun yi rashin biyayya ga Ubangiji, saboda haka Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima a shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam.
3 He came with 1,200 chariots, 60,000 horsemen, and countless troops from Egypt: Libyans, Sukkites, and Cushites. Da kekunan yaƙi dubu ɗaya da ɗari biyu da kuma mahayan dawakai dubu haɗe da mayaƙan Libiyawa, Sukkatawa da kuma Kushawa waɗanda suka wuce ƙidaya suka zo tare da shi daga Masar,
4 He captured the fortified cities of Judah and came as far as Jerusalem. ya ci biranen katanga na Yahuda har zuwa Urushalima.
5 Shemaiah the prophet came to Rehoboam and Judah's leaders, gathered in Jerusalem because of Shishak: "So says our Father: You abandoned me, so I abandon you to Shishak." Sai annabi Shemahiya ya zo wurin Rehobowam da kuma wajen shugabannin Yahuda waɗanda suka taru a Urushalima don tsoron Shishak, ya kuma faɗa musu, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Kun yi biris da ni; saboda haka, yanzu na bashe ku ga Shishak.’ ”
6 Then the leaders of Israel and the king humbled themselves and said, "Our Father is righteous." Shugabannin Isra’ila da sarki suka ƙasƙantar da kansu suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”
7 When our Father saw they had humbled themselves, our Father's word came to Shemaiah: "They've humbled themselves; I won't destroy them, but grant them a little rescue, and my anger won't pour out on Jerusalem through Shishak. Sa’ad da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai wannan maganar Ubangiji ta zo wa Shemahiya, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba.
8 But they will be Shishak's servants, to know my service and the service of earthly kingdoms." Duk da haka za su zama bayinsa, don su san bambanci tsakanin yin mini bauta da kuma yin wa sarakunan sauran ƙasashe bauta.”
9 Shishak king of Egypt attacked Jerusalem and took everything—the treasures of our Father's house, the royal palace, including the gold shields Solomon made. Da Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima, sai ya kwashi ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan sarki. Ya kwashe kome da kome, har da garkuwoyin zinariyar da Solomon ya yi.
10 Rehoboam replaced them with bronze shields, entrusted to the guard commanders watching the entrance to the king's house. Sai sarki Rehobowam ya ƙera garkuwoyin tagulla a madadin na zinariya, ya sa su a hannun shugabannin matsara na mashigin gidan sarki.
11 Whenever the king entered our Father's house, the guards carried the shields, then returned them to the guard chamber. Duk sa’ad da sarki ya tafi haikalin Ubangiji, masu tsaron sukan tafi tare da shi, suna riƙe da garkuwoyi, daga baya kuma su mai da su a ɗakin tsaro.
12 When Rehoboam humbled himself, our Father's anger turned from him, not destroying him completely; good things remained in Judah too. Gama Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, fushin Ubangiji ya bar shi, ba a kuwa hallaka shi ƙaƙaf ba. Tabbatacce an yi ’yan abubuwa masu kyau a Yahuda.
13 King Rehoboam strengthened himself in Jerusalem and reigned; forty-one when he became king, he reigned seventeen years in Jerusalem, the city our Father chose from all the tribes of Israel to place his name there. His mother was Naamah, an Ammonite. Sarki Rehobowam ya kafa kansa daram a Urushalima, ya kuma ci gaba a matsayin sarki. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila wanda zai sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama ce, ita mutuniyar Ammon ce.
14 He did evil, because he did not set his heart to seek our Father. Ya aikata mugunta domin bai sa zuciyarsa ga neman Ubangiji ba.
15 Rehoboam's deeds, first to last, appear in the records of Shemaiah the prophet and Iddo the seer, listing genealogies. Rehoboam and Jeroboam warred continually. Game da ayyukan mulkin Rehobowam, daga farko zuwa ƙarshe, ba a rubuce suke a tarihin Shemahiya annabi da Iddo mai gani wanda yake zancen zuriyoyi ba? Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam.
16 Rehoboam rested with his ancestors, buried in the City of David; his son Abijah reigned instead. Rehobowam ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Abiya ɗansa kuma ya gāje shi a matsayin sarki.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]