Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 11 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Rehoboam came to Jerusalem and assembled the house of Judah and Benjamin—180,000 chosen warriors—to fight against Israel and restore the kingdom to Rehoboam. Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam.
2 But the word of our Father came to Shemaiah, the man of our Father, saying: Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah.
3 "Say to Rehoboam son of Solomon, king of Judah, and to all Israel in Judah and Benjamin: “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin,
4 This is what our Father says: Don't go up or fight against your brothers. Go home, each of you—this came from me." So they obeyed the words of our Father and turned back from advancing against Jeroboam. ‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’ ” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam.
5 Rehoboam lived in Jerusalem and built up cities for defense in Judah. Rehobowam ya zauna a Urushalima ya kuma gina garuruwa don kāriya a cikin Yahuda.
6 He built Bethlehem, Etam, and Tekoa, Betlehem, Etam, Tekowa,
7 Beth-zur, Soco, Adullam, Bet-Zur, Soko, Adullam,
8 Gath, Mareshah, Ziph, Gat, Maresha, Zif,
9 Adoraim, Lachish, Azekah, Adorayim, Lakish, Azeka,
10 Zorah, Aijalon, and Hebron, the fortified cities in Judah and Benjamin. Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin.
11 He strengthened the fortresses and put commanders in them, along with stores of food, oil, and wine. Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi.
12 In every city he placed shields and spears, strengthening them greatly. So Judah and Benjamin remained his. Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.
13 The priests and the Levites who were throughout all Israel came to him from all their territory, Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi.
14 for the Levites left their pasturelands and property, going to Judah and Jerusalem, since Jeroboam and his sons turned them away from serving as priests of our Father. Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da ’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji.
15 He appointed his own priests for the high places, for the goat idols, and for the calf idols he had made. Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.
16 From every tribe of Israel, those who set their heart on seeking our Father, the God of Israel, followed the Levites to Jerusalem to sacrifice to our Father, the God of their ancestors. Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
17 They strengthened Judah's kingdom, supporting Rehoboam son of Solomon three years, for they walked in the way of David and Solomon three years. Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.
18 Rehoboam married Mahalath, the daughter of Jerimoth son of David and of Abihail the daughter of Eliab son of Jesse. Rehobowam ya auri Mahalat, ’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil ’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.
19 She bore him sons: Jeush, Shemariah, and Zaham. Ta haifa masa ’ya’ya maza. Yewush, Shemariya da Zaham.
20 After her, he married Maacah the daughter of Absalom, who bore him Abijah, Attai, Ziza, and Shelomith. Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.
21 Rehoboam loved Maacah daughter of Absalom more than his other wives and concubines, since he had eighteen wives, sixty concubines, twenty-eight sons, and sixty daughters. Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka ’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da ’ya’ya maza ashirin da takwas da ’ya’ya mata sittin.
22 Rehoboam made Abijah, son of Maacah, chief leader among his brothers, intending to make him king. Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin ’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki.
23 He acted wisely, spreading some of his sons through every district of Judah and Benjamin, to each fortified city, giving them abundant provisions and seeking many wives for them. Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu ’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]