Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The Pharisees and some of the scribes who had come from Jerusalem gathered around Jesus, Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu.
2 and they saw that some of his disciples were eating bread with unclean hands—that is, unwashed. Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba.
3 (For the Pharisees and all the Jews don't eat unless they wash their hands ceremonially, keeping the elders' tradition. (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce.
4 When they come from the market, they don't eat without washing. They also hold to many other traditions they've received—washing cups, pitchers, and copper vessels.). Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.)
5 Then the Pharisees and scribes asked him, "Why don't your disciples follow the elders' tradition, but eat bread with unclean hands?" Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”
6 He replied, "Isaiah prophesied truly about you hypocrites, as written: 'These people honor me with their lips, but their heart is far from me.' Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.
7 'They worship me in vain, teaching as doctrines the commandments of men.' A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’
8 You abandon the commandment of our Father and hold to the tradition of men." Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”
9 He said to them, "You do a fine job setting aside our Father's commandment to keep your own tradition!" Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku!
10 For Moses said, 'Honor your father and your mother,' and 'Whoever curses father or mother must be executed.' Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’
11 "But you say: if anyone tells his father or mother, 'Whatever you'd have gained from me is Corban' (a gift devoted to our Father), Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah),
12 then you no longer let him do anything for his father or mother. sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu.
13 So you cancel the word of our Father with your handed-down tradition. You do many things like this." Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”
14 He called the crowd again and said to them, "Listen to me, all of you, and understand: Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan.
15 Nothing outside a person entering him can make him unclean; rather, what comes out of a person is what makes him unclean." Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.”
17 When he had left the crowd and entered the house, his disciples asked him about the parable. Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali.
18 He said to them, "Are you also this dull? Don't you understand nothing entering a person from outside can make him unclean, Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi.
19 since it doesn't enter his heart but his stomach, and then goes out into the sewer?" (Saying this, he declared all foods clean.). Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, sa’an nan kuma yă fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.)
20 He said, "What comes out of a person—that makes him unclean. Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi.
21 For from within, out of the human heart, come evil thoughts—sexual sin, theft, murder, Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,
22 adultery, greed, malice, deceit, sensuality, envy, slander, pride, and foolishness. kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta.
23 All these evils come from inside and make a person unclean." Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”
24 Jesus left there for the region of Tyre. He entered a house, wanting no one to know, but couldn't stay hidden. Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba.
25 Instead, a woman whose little daughter had an unclean spirit heard about him at once, came, and fell at his feet. Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa.
26 The woman was Greek, Syrophoenician by birth. She kept asking him to drive the demon out of her daughter. Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta.
27 He told her, "Let the children eat first, for it's not right to take their bread and toss it to the dogs." Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”
28 But she replied to him, "Sir, even the dogs under the table eat the children's crumbs." Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.”
29 He said to her, "Because of this answer, go—the demon has left your daughter." Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”
30 And she went home and found the child lying on the bed, and the demon gone. Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
31 Then Jesus left the territory of Tyre, went through Sidon to the Sea of Galilee, into the region of the Decapolis. Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis.
32 They brought him a deaf man who could hardly speak, begging him to lay his hand on him. A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin.
33 Jesus took him aside privately, away from the crowd, put his fingers in the man's ears, spit, and touched his tongue. Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin.
34 Then, looking up to heaven, he sighed deeply and said to him, "Ephphatha!" (that is, "Be opened!"). Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”).
35 And immediately his ears were opened, his tongue was released, and he began to speak plainly. Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.
36 Jesus ordered them to tell no one; but the more he ordered, the more they proclaimed it. Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi.
37 They were completely amazed: "He has done everything well—he makes the deaf hear and the mute speak." Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]