Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The beginning of the gospel of Jesus Christ, the Son of our Father. Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.
2 As written in Isaiah the prophet: "Look, I send my messenger ahead of you, who will prepare your way. An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya cewa, “Zan aika da ɗan aikena yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka,”
3 A voice calling out in the wilderness: 'Prepare the way of the Lord, make his paths straight.'" “muryar mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”
4 John appeared, baptizing in the wilderness and proclaiming a baptism of repentance for the forgiveness of sins. Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.
5 All Judea and everyone in Jerusalem went out to him, and he baptized them in the Jordan River as they confessed their sins. Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun.
6 John was dressed in camel's hair, with a leather belt around his waist, eating locusts and wild honey. Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, ya kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fāri ne da kuma zumar jeji.
7 He announced: "After me comes one stronger than I; I'm not worthy to stoop and untie his sandal strap. Wannan kuwa shi ne saƙonsa, “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba.
8 I have baptized you with water, but he will baptize you with the Holy Spirit." Ina muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
9 In those days Jesus came from Nazareth of Galilee and was baptized by John in the Jordan. A lokacin, Yesu ya zo daga Nazaret na Galili, Yohanna kuwa ya yi masa baftisma a Urdun.
10 Immediately, as he came up out of the water, he saw the heavens split open and the Holy Spirit come down on him like a dove. Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya.
11 And a voice came from heaven: "You are my beloved Son; in you I delight." Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, da kai kuma nake fari ciki ƙwarai.”
12 And immediately the Holy Spirit drove him out into the wilderness. Nan da nan, sai Ruhu ya kai shi cikin hamada,
13 He was in the wilderness forty days, tempted by Satan, with the wild animals, and the angels served him. ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima.
14 Now after John was arrested, Jesus came into Galilee, proclaiming the gospel of our Father, Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah.
15 and saying, "The time is fulfilled, and our Father's kingdom is near; repent and believe the good news." Yana cewa, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”
16 Passing the Sea of Galilee, he saw Simon and his brother Andrew casting a net in the sea, for they were fishermen. Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗan’uwansa Andarawus, suna jefa abin kamun kifi a cikin tafkin, domin su masunta ne.
17 And Jesus said to them, "Follow me, and I will make you become fishers of people." Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”
18 And immediately they left their nets and followed him. Nan da nan, suka bar abin kamun kifinsu, suka bi shi.
19 Going a little farther, he saw James son of Zebedee and John his brother in their boat, mending the nets. Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga Yaƙub ɗan Zebedi, da ɗan’uwansa Yohanna a cikin jirgin ruwa, suna gyaran abin kamun kifinsu.
20 At once he called them; leaving their father Zebedee in the boat with the hired hands, they followed him. Ba da ɓata lokaci ba, ya kira su, sai suka bar mahaifinsu Zebedi a cikin jirgin ruwan, tare da ’yan haya, suka kuwa bi shi.
21 They went to Capernaum. At once, on the Sabbath, he entered the synagogue and began teaching. Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa.
22 They were amazed at his teaching, for he taught them with authority, not like the scribes. Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba.
23 And immediately there was in their synagogue a man with an unclean spirit, and he cried out. Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce,
24 Why meddle with us, Jesus of Nazareth? Have you come to destroy us? I know who you are—God's Holy One! “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!”
25 But Jesus rebuked him, saying, "Be silent, and come out of him!" Yesu ya tsawata masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!”
26 And the unclean spirit, convulsing him and crying out with a loud voice, came out of him. Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.
27 All were amazed, and they questioned each other: "What is this? A new teaching with authority - he commands even the unclean spirits, and they obey him!" Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.”
28 And at once his fame spread everywhere throughout all the surrounding region of Galilee. Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili.
29 Immediately he left the synagogue and went to Simon and Andrew's house, with James and John. Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna.
30 Now Simon's mother-in-law lay sick with a fever, and immediately they told him about her. Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita.
31 He came, took her hand, raised her up. The fever left her, and she served them. Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.
32 That evening, when the sun set, they brought him all who were sick and those oppressed by demons. A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu.
33 And the whole city was gathered together at the door. Duk garin ya taru a ƙofar gidan.
34 He healed many sick with various diseases and drove out many demons, not letting the demons speak, since they knew him. Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.
35 Long before dawn, while still dark, he got up, went out to a deserted place, and prayed there. Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a.
36 And Simon and those who were with him searched for him, Siman da abokansa suka fita nemansa.
37 and they found him and said to him, "Everyone is looking for you." Da suka same shi, sai suka ce, “Kowa yana nemanka!”
38 He said, "Let us go elsewhere, to the neighboring towns, so I can preach there too, for that is why I came." Yesu ya amsa ya ce, “Mu je wani wuri dabam, zuwa ƙauyukan da suke kusa, don in yi wa’azi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.”
39 And he went throughout all Galilee, preaching in their synagogues and casting out demons. Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu.
40 A man with leprosy came, knelt, and begged him, "If you're willing, you can make me clean." Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtacce ni.”
41 Moved with deep compassion, he stretched out his hand, touched him, and said to him, "I am willing; be clean." Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka tsabtacce!”
42 And immediately the leprosy left him, and he was made clean. Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.
43 Sternly warning him, he sent him away at once, Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi cewa,
44 and told him, "Make sure you tell no one—but go, show yourself to the priest, and offer what Moses commanded for your cleansing, as proof to the people." “Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yă zama shaida gare su.”
45 But he went out, proclaiming it freely and spreading the news, so Jesus could no longer enter a town openly, but stayed in lonely places. Yet people came to him from everywhere. A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]