Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 20 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Early on the first day of the week, while dark, Mary Magdalene came to the tomb and saw the stone taken from it. Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin.
2 So she ran and came to Simon Peter and the other disciple, the one Jesus loved, and told them, "They've taken the Lord from the tomb, and we don't know where they put him." Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”
3 So Peter and the other disciple set out and went toward the tomb. Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin.
4 Both ran together, but the other disciple ran faster than Peter, reaching the tomb first. Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin.
5 And stooping down, he saw the linen cloths lying there, but he did not go in. Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba.
6 Simon Peter, following him, arrived and entered the tomb, and saw the linen cloths lying there, Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can,
7 and the cloth that was on his head, not lying with the linen wrappings but folded separately in one place. haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin.
8 The other disciple, first to reach the tomb, then went in too; he saw and believed. A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata.
9 For they still did not understand the Scripture, that he must rise from the dead. (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.)
10 Then the disciples went back to their homes. Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama.
11 But Mary stood outside the tomb, weeping. As she wept, she bent to look into the tomb. Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin,
12 She saw two angels in white, seated where Jesus's body had lain, one at the head, one at the feet. sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.
13 They asked her, "Woman, why are you crying?" She answered, "They took my Lord, and I don't know where they put him." Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?” Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.”
14 Saying this, she turned and saw Jesus standing there, not knowing it was Jesus. Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba.
15 Jesus said to her, "Woman, why are you crying? Who are you seeking?" Taking him for the gardener, she said, "Sir, if you carried him off, tell me where you put him, and I'll take him away." Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?” Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.”
16 Jesus said to her, "Mary." She turned and said to him in Aramaic, "Rabboni!" (which means Teacher). Yesu ya ce mata, “Maryamu.” Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”).
17 Jesus said to her, "Do not cling to me, for I have not yet ascended to the Father. But go to my brothers and say to them, 'I am ascending to my Father and your Father.'" Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ”
18 Mary Magdalene went and told the disciples, "I have seen the Lord," and that he had said these things to her. Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
19 That evening, the first day of the week, with the doors locked where the disciples were, for fear of the Jewish leaders, Jesus came, stood among them, and said, "Peace be with you." Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”
20 After saying this, he showed them his hands and side. The disciples rejoiced to see the Lord. Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.
21 Jesus said to them again, "Peace to you. As the Father has sent me, so I send you." Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.”
22 After saying this, he breathed on them and said to them, "Receive the Holy Spirit. Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki.
23 If you forgive anyone's sins, they're forgiven; if you hold back forgiveness from anyone, it's held back." Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”
24 Now Thomas, one of the Twelve, called the Twin, was not with them when Jesus came. Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo.
25 The other disciples kept telling him, "We've seen the Lord!" But he told them, "Unless I see the nail marks in his hands, put my finger where they were, and put my hand in his side, I'll never believe." Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!” Amma ya ce musu, “Ina, ai, sai na ga ramin ƙusa a hannuwansa na sa yatsata a inda ƙusoshi suka kasance, na kuma sa hannuna a gefensa, in ba haka ba, ba zan gaskata ba.”
26 Eight days later, his disciples were indoors again, Thomas with them. Though the doors were locked, Jesus came, stood among them, and said, "Peace be with you." Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”
27 Then he said to Thomas, "Put your finger here, see my hands. Reach your hand out, put it in my side. Leave doubt behind—believe." Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”
28 Thomas answered him, "My Lord and my God!" Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”
29 Jesus said to him, "Have you believed because you've seen me? Blessed are those who haven't seen, yet believe." Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”
30 Jesus did many other signs before his disciples, not written in this book. Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba.
31 But these are written so you'll believe Jesus is the Christ, the Son of our Father, and by believing have life in his name. An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]