Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 15 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 "I am the true vine, and my Father is the gardener. “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin.
2 Every branch in me not bearing fruit, he removes; and every one bearing fruit, he prunes, so it bears more fruit. Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya.
3 You are already clean because of the word I have spoken to you. Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku.
4 Remain in me, and I in you. As a branch can't bear fruit alone, unless it remains in the vine, neither can you unless you remain in me. Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
5 I am the vine, you the branches. Whoever remains in me, and I in them, bears much fruit, for apart from me you can do nothing. “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.
6 Anyone not remaining in me is thrown out like a branch and withers; branches are gathered, thrown into the fire, and burned. Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone.
7 If you remain in me and my words remain in you, ask whatever you want, and it will happen for you. In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku.
8 This is how my Father is glorified: that you bear much fruit and prove to be my disciples. Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.
9 "As the Father has loved me, so I have loved you. Remain in my love. “Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata.
10 If you keep my commands, you will remain in my love, as I have kept my Father's commands and remain in his love. In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa.
11 I've told you this so my joy may be in you, and your joy be complete. Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.
12 "This is my command: love one another as I have loved you. Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.
13 No one has greater love than this: to lay down one's life for one's friends. Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.
14 You are my friends if you do what I command you. Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta.
15 I no longer call you servants—a servant doesn't know what his master does. I call you friends, since I've made known to you everything I heard from my Father. Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana.
16 You didn't choose me—I chose you and placed you to go, bear fruit that lasts, so whatever you ask the Father in my name, he'll give you. Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.
17 This is my command to you: love one another. Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.
18 "If the world hates you, know that it hated me first. “In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne.
19 If you were of the world, the world would love you as its own. But you are not of the world; instead, I chose you out of the world, so the world hates you. Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.
20 Remember what I told you: a servant isn't greater than his master. If they persecuted me, they'll persecute you too; if they kept my word, they'll keep yours too. Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.
21 But they'll do all this to you because of my name, since they don't know the one who sent me. Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba.
22 Had I not come and spoken to them, they would have no sin; now they have no excuse for their sin. Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu.
23 Whoever hates me hates my Father as well. Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma.
24 Had I not done among them the works no one else did, they would have no sin. But now they have seen and hated both me and my Father. Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana.
25 But this happened to fulfill what is written in their Law: 'They hated me without cause.' Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’
26 "When the Helper comes, whom I will send you from the Father—the Spirit of truth proceeding from the Father—he will testify about me. “Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni.
27 "And you also must testify, because you have been with me from the beginning." Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]