Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 13 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Now, before the Passover festival, Jesus knew his hour had come to leave this world to his Father. Having loved his own in the world, he loved them to the end. Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.
2 During supper, the devil had already put into Judas son of Simon Iscariot's heart the plan to betray Jesus. Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu.
3 Jesus, knowing that the Father had given everything into his hands, and that he had come from him and was returning to him, Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah;
4 rose from supper, took off his outer clothes, picked up a towel, and tied it around his waist. saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa.
5 Then he poured water into a basin and began washing the disciples' feet, drying them with the towel tied around him. Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura.
6 He came to Simon Peter, who said to him, "Lord, are you going to wash my feet?" Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, “Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?”
7 Jesus answered him, "You do not realize now what I am doing, but later you will understand." Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.”
8 "You will never wash my feet," Peter said. Jesus answered, "Unless I wash you, you share nothing with me." Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.”
9 Simon Peter said to him, "Lord, not only my feet, but also my hands and head!" Sai Siman Bitrus ya ce, “To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!”
10 Jesus told him, "One who has bathed needs only to wash his feet—he is fully clean. You are clean, but not all of you." Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yă wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.”
11 He knew who would betray him; that's why he said, "Not all of you are clean." Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba kowa ba ne yake da tsabta.”
12 After washing their feet and dressing, he reclined again and said to them, "Do you understand what I have done for you? Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, “Kun fahimci abin da na yi muku?
13 You call me Teacher and Lord, and rightly so, for that is what I am. Kuna ce da ni ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake.
14 So if I, your Lord and Teacher, washed your feet, you too must wash each other's feet. Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna.
15 For I have given you an example, that you should do as I have done for you. Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku.
16 Truly, truly, I say to you, a servant isn't greater than his master, nor a messenger greater than his sender. Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi.
17 If you know these things, you are blessed if you do them. Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su.
18 "I don't mean all of you—I know those I've chosen. But Scripture must be fulfilled: 'The one eating my bread has raised his heel against me.' “Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’
19 I tell you now, before it happens, so you'll believe, once it happens, that I AM. “Ina faɗa muku yanzu tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi.
20 Truly, truly, I tell you, whoever welcomes someone I send welcomes me, and whoever welcomes me welcomes the one who sent me." Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ”
21 After saying this, Jesus, troubled in spirit, testified, "Truly, truly, I tell you, one of you will betray me." Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
22 The disciples looked at one another, at a loss to know which of them he meant. Almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake.
23 One of his disciples, the one Jesus loved, was reclining at his side. Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi.
24 So Simon Peter motioned to him to ask which one Jesus meant. Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?”
25 Leaning back against Jesus, he asked him, "Lord, who is it?" Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?”
26 Jesus answered, "It's the one I'll give this bread to, once I've dipped it." Then he dipped the bread and gave it to Judas, son of Simon Iscariot. Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman.
27 After Judas took the bread, Satan entered into him. So Jesus told him, "Do quickly what you're doing." Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.”
28 But no one reclining at the table understood why he said this to him. Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.
29 Since Judas held the money bag, some thought Jesus meant, 'Buy what we need for the feast,' or, 'Give something to the poor.' Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu.
30 As soon as Judas had taken the bread, he went out. And it was night. Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. A lokacin kuwa dare ya yi.
31 After Judas left, Jesus said, "Now the Son of Man is glorified, and my Father is glorified in him. Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa.
32 If my Father is glorified in him, my Father will also glorify the Son in himself and glorify him immediately. In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikin Ɗan, Allah kuwa zai ɗaukaka Ɗan zuwa ga zatinsa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.
33 Dear children, I'm with you a little longer. You'll look for me, and as I told the Jewish leaders, so I tell you now: where I'm going, you can't come. “’Ya’yana, zan kasance da ku na ɗan ƙanƙani lokaci ne. Za ku neme ni. Kuma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, haka nake gaya muku yanzu. Inda zan tafi, ba za ku iya zuwa ba.
34 I give you a new command: love one another. As I have loved you, so you must love one another. “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna.
35 By this everyone will know that you are my disciples, if you love one another." Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”
36 Simon Peter said to him, "Lord, where are you going?" Jesus answered, "Where I'm going you can't follow me now, but you'll follow later." Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”
37 Peter asked, "Lord, why can't I follow you now? I'll lay down my life for you." Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.”
38 Jesus replied, "You will lay down your life for me? Truly, truly, I tell you: the rooster won't crow until you have denied me three times." Sai Yesu ya amsa ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku!
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]