Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Samuel 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 After the death of Saul, David returned from defeating the Amalekites and stayed in Ziklag two days. Bayan mutuwar Shawulu, Dawuda ya dawo daga karkashe Amalekawa. Sai ya zauna a Ziklag kwana biyu.
2 On the third day a man came from Saul's camp, clothes torn, dirt on his head. Reaching David, he fell to the ground and bowed. A rana ta uku sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Shawulu da yagaggen riga da ƙura a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi a ƙasa don yă nuna bangirma.
3 David asked him, "Where have you come from?" "I escaped from the camp of Israel," he replied. Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Daga ina ka fito?” Ya amsa ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra’ila.”
4 "What happened?" David asked. "Tell me." He said, "The people fled the battle. Many fell and died. Saul and his son Jonathan are dead too." Dawuda ya ce, “Gaya mini, me ya faru?” Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga yaƙi, aka kuma karkashe yawancin mutane. Shawulu da ɗansa Yonatan ma sun mutu.”
5 David asked the young man who brought the news, "How do you know Saul and his son Jonathan are dead?" Sai Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Yaya ka san cewa Shawulu da ɗansa Yonatan sun mutu?”
6 The young man said, "I happened onto Mount Gilboa, and there was Saul, leaning on his spear, the chariots and horsemen bearing down on him. Saurayin ya ce, “Ina kan dutsen Gilbowa a lokacin sai na ga Shawulu jingine a māshinsa. Kekunan yaƙi da mahayansu suna matsowa kusa da shi.
7 He turned around, saw me, and called to me. I said, 'Here I am.' Da ya juya ya gan ni sai ya kira ni, na kuwa ce masa, ‘Ga ni?’
8 He asked me, 'Who are you?' I told him, 'I am an Amalekite.' “Ya tambaye ni ya ce, ‘Wane ne kai?’ “Na ce, ‘Ni mutumin Amalek ne.’
9 He said to me, 'Stand over me and kill me; anguish has seized me, but I'm still alive.' “Sai ya ce mini, ‘Matso kusa ka kashe ni! Ina cikin azabar mutuwa, sai dai har yanzu ina da rai.’
10 So I stood over him and killed him, since I knew he wouldn't survive his fall. Then I took the crown from his head and the band on his arm, and brought them here to my lord." “Saboda haka na matso kusa da shi na kashe shi, domin na san cewa ba zai yi rai ba, da yake ya riga ya fāɗi. Sai na cire rawanin da yake kansa, na kuma cire warwaron hannunsa, na kuwa kawo maka su duka, ranka yă daɗe!”
11 Then David grabbed his own clothes and tore them, and so did all the men with him. Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka yayyage rigunarsu.
12 They mourned, wept, and fasted until evening for Saul, his son Jonathan, our Father's people, and the house of Israel, because they had fallen by the sword. Suka yi makoki, da kuka, da azumi har yamma saboda Shawulu da ɗansa Yonatan, da saboda sojojin Ubangiji, da kuma gidan Isra’ila, gama an karkashe su a yaƙi.
13 David asked the young man who brought the news, "Where are you from?" He said, "I'm the son of a foreigner, an Amalekite." Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Daga ina ka fito?” Ya ce, “Ni ɗan wani baƙo ne, mutumin Amalek.”
14 David said, "How were you not afraid to raise your hand to kill our Father's anointed?" Dawuda ya ce masa, “Yaya ba ka ji tsoro ɗaga hannu ka hallaka shafaffe na Ubangiji ba?”
15 David called one of his young men and said, "Go, strike him down." He struck him, and he died. Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin mutanensa ya ce, “Je ka kashe shi!” Haka kuwa ya buge shi, ya kuwa mutu.
16 David had said to him, "Your blood is on your own head, for your own mouth testified against you when you said, 'I killed our Father's anointed.'" Gama Dawuda ya riga ya ce masa, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe shafaffe na Ubangiji.’ ”
17 Then David sang this lament over Saul and his son Jonathan, Dawuda ya rera wannan makoki saboda Shawulu da ɗansa Yonatan.
18 and ordered the people of Judah taught this lament, called The Bow; it is written in the Book of Jashar: Ya umarta a koya wa mutanen Yahuda wannan waƙa mai suna Makokin Baka (tana a rubuce a Littafin Yashar),
19 "Your glory, Israel, lies slain on your heights. How the mighty have fallen! “Ya Isra’ila, an kashe darajarki a kan tuddanki. Ga shi, jarumawa sun fāɗi!
20 Don't tell it in Gath, don't proclaim it in the streets of Ashkelon, or the daughters of the Philistines will rejoice, the daughters of the uncircumcised will exult. “Kada a faɗe shi a Gat, kada a yi shelarsa a titunan Ashkelon, don kada ’yan matan Filistiyawa su yi murna don kada ’yan matan marasa kaciya su yi farin ciki.
21 Mountains of Gilboa, may you have no dew or rain, no fields yielding offerings. For there the shield of the mighty was defiled, the shield of Saul, no longer rubbed with oil. “Ya duwatsun Gilbowa, kada a sāke yin ruwa ko raɓa a kanku, balle gonakin da suke ba da hatsin hadaya su ƙara bayarwa. Gama a can ne garkuwoyin manyan sojoji suka kwanta, suka kwanta a wulaƙance. Garkuwar Shawulu kuwa, ba za a ƙara shafa mata mai ba.
22 From the blood of the slain, from the flesh of the mighty, the bow of Jonathan did not turn back, the sword of Saul did not return unsatisfied. “Daga jinin waɗanda aka kashe, daga tsokar naman jarumi, bakan Yonatan bai juye baya ba, takobin Shawulu bai komo ba tare da gamsuwa ba.
23 Saul and Jonathan, beloved and cherished in life, in death they were not parted. They were swifter than eagles, stronger than lions. Shawulu da Yonatan, a raye ƙaunatattu ne da kuma bansha’awa, a mace kuma ba su rabu ba. Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi.
24 Daughters of Israel, weep for Saul, who clothed you in scarlet and finery, who adorned your garments with ornaments of gold. “Ya ku ’yan matan Isra’ila, ku yi kuka saboda Shawulu, wanda ya suturta ku da jajjayen kayan ado, wanda ya yi wa rigunarku ado da zinariya.
25 How the mighty have fallen in the thick of battle! Jonathan lies slain on your heights. “Jarumawa sun fāɗi a yaƙi! Ga Yonatan matacce a tuddanku.
26 I grieve for you, my brother Jonathan; you were very dear to me. Your love for me was wonderful, surpassing the love of women. Na yi baƙin ciki saboda kai, Yonatan ɗan’uwana; ƙaunatacce kake a gare ni. Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce, abar al’ajabi fiye da ta mace.
27 How the mighty have fallen! The weapons of war have perished." “Jarumawa sun fāɗi! Makaman yaƙi sun hallaka!”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]