Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 17 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 His son Jehoshaphat became king in his place and strengthened himself against Israel. Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki ya kuma kahu sosai gāba da Isra’ila.
2 He stationed troops in all Judah's fortified cities and garrisons in the land of Judah and in the cities of Ephraim that his father Asa had captured. Ya kafa mayaƙa a dukan biranen katangar Yahuda, ya kuma sa runduna a Yahuda da kuma a garuruwan Efraim da mahaifinsa Asa ya ci da yaƙi.
3 Our Father was with Jehoshaphat, for he walked his father David's earlier ways, not seeking the Baals. Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat domin a shekarunsa na farko-farko ya yi tafiya a hanyoyin da kakansa Dawuda ya bi. Bai nemi shawarar Ba’al ba
4 Instead, he sought the Father his father served, obeyed his commandments, and not the practices of Israel. amma ya nemi Allah na kakansa ya kuma bi umarnansa a maimakon ayyukan da Isra’ila ke yi.
5 So our Father secured the kingdom in his hand; all Judah brought gifts to Jehoshaphat, and he had great wealth and honor. Ubangiji ya kafa mulkin a ƙarƙashin ikonsa; dukan Yahuda kuwa suka kawo kyautai wa Yehoshafat, ta haka ya yi arziki sosai da kuma girma.
6 His heart was devoted to our Father's ways; he removed the high places and Asherah poles from Judah. Zuciyarsa ta duƙufa ga hanyoyin Ubangiji, bugu da ƙari, ya kawar masujadan kan tudu da ginshiƙan Ashera daga Yahuda.
7 In his reign's third year he sent his officials Ben-hail, Obadiah, Zechariah, Nethanel, and Micaiah to teach in Judah's cities, A shekara ta uku ta mulkinsa, ya aiki ma’aikatansa Ben-Hayil, Obadiya, Zakariya, Netanel da Mikahiya su yi koyarwa a garuruwan Yahuda.
8 and the Levites with them: Shemaiah, Nethaniah, Zebadiah, Asahel, Shemiramoth, Jehonathan, Adonijah, Tobijah, Tob-adonijah; and with them the priests Elishama, Jehoram. Tare da su akwai waɗansu Lawiyawa, Shemahiya, Netaniya, Zebadiya, Asahel, Shemiramot, Yehonatan, Adoniya, Tobiya da Tob Adoniya, da kuma firistoci Elishama da Yehoram.
9 They taught throughout Judah, carrying the Book of our Father's Instruction, going to all Judah's cities, teaching the people. Suka yi koyarwa a dukan Yahuda, suna ɗauke da Littafin Dokar Ubangiji tare da su; suka tafi ko’ina a dukan garuruwan Yahuda suka koyar da mutane.
10 The dread of our Father fell on all the kingdoms around Judah, so they made no war on Jehoshaphat. Tsoron Ubangiji ya kama dukan masarautun ƙasashen da suke kewaye da Yahuda, har ba su yi yaƙi da Yehoshafat ba.
11 Some Philistines brought Jehoshaphat gifts and silver tribute; the Arabs brought flocks: 7,700 rams, 7,700 male goats. Waɗansu Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa a matsayin haraji, Larabawa kuwa suka kawo masa garkuna, raguna dubu bakwai da ɗari bakwai da kuma awaki dubu bakwai da ɗari bakwai.
12 Jehoshaphat grew more and more powerful, and he built fortresses and storage cities in Judah. Yehoshafat ya yi ta ƙaruwa a ƙarfi; ya gina katanga da biranen ajiya a Yahuda
13 He had large supplies in the cities of Judah, and mighty warriors in Jerusalem. da kuma tanade-tanade masu yawa a garuruwan Yahuda. Ya kuma ajiye gogaggu mayaƙa a Urushalima.
14 Their enrollment by ancestral house: from Judah, commanders of thousands—Adnah the commander, with him 300,000 mighty warriors; Ɗaukar da aka yi musu bisa ga iyalai yana kamar haka. Daga Yahuda, shugaban ƙungiya 1,000. Adna ne shugaba, tare da jarumawa 300,000;
15 next to him was Jehohanan the commander, and with him 280,000; biye da shi, Yehohanan shi ne shugaba, yana da sojoji 280,000;
16 next Amasiah son of Zichri, who volunteered for our Father, with him 200,000 mighty warriors. biye da shi, Amasiya ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa da yardar rai don hidimar Ubangiji, yana da sojoji 200,000.
17 From Benjamin: Eliada, a mighty warrior, and with him 200,000 armed with bow and shield; Daga Benyamin, Eliyada, jarumi soja, yana da sojoji 200,000 riƙe da baka da garkuwoyi;
18 next to him Jehozabad, and with him 180,000 equipped for war. biye da shi, Yehozabad, yana da sojoji 18,000 shiryayyu don yaƙi.
19 These men served the king, besides those he stationed in the fortified cities throughout Judah. Waɗannan su ne suka yi wa sarki hidima, ban da waɗanda aka sa a biranen katanga ko’ina a Yahuda.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]