Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 16 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In Asa's thirty-sixth year, Baasha king of Israel invaded Judah, fortifying Ramah to keep anyone from leaving or entering Asa king of Judah's territory. A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura don yă yaƙi Yahuda da Rama mai katanga, don kuma yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa sarkin Yahuda.
2 Asa took silver and gold from the storerooms of our Father's house and the royal house, and sent them to Ben-Hadad king of Aram, living in Damascus, with this message: Sai Asa ya ɗauki azurfa da zinariya daga ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma na fadansa ya aika wa Ben-Hadad sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus.
3 "Let there be a treaty between me and you, as there was between my father and your father. See, I'm sending you silver and gold. Go now and break your treaty with Baasha king of Israel, so he withdraws from me." Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.”
4 Ben-Hadad agreed with King Asa and sent his army commanders against Israel's cities. They struck down Ijon, Dan, Abel-maim, and all Naphtali's store cities. Ben-Hadad ya yarda da Sarki Asa ya kuma aika da manyan hafsoshin mayaƙansa a kan garuruwan Isra’ila. Suka ci Iyon, Dan, Abel-Mayim da kuma dukan biranen ajiya na Naftali.
5 When Baasha heard of it, he stopped fortifying Ramah and abandoned his work. Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa.
6 King Asa mustered all Judah; they carried off the stones and timber Baasha had fortified Ramah with, and with them he fortified Geba and Mizpah. Sa’an nan Sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuda, suka kuma kwashe duwatsu da katako daga Rama waɗanda Ba’asha yake amfani da su. Da su ne Asa ya gina Geba da Mizfa.
7 Then Hanani the seer came to Asa king of Judah and said to him, "Because you relied on Aram's king and not your Father, his army escaped your hand. A lokacin Hanani mai duba ya zo wurin Asa sarkin Yahuda ya ce masa, “Don ka dogara ga sarkin Aram, ba kuwa ga Ubangiji Allahnka ba ne mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka.
8 Weren't Cushites and Libyans a vast army with countless chariots and horsemen? Because you relied on your Father, he gave them to you. Ai, Kushawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da kekunan yaƙi da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, ya kuwa ba da su cikin hannunka.
9 For our Father's eyes scan the whole earth, to strengthen those whose heart is fully devoted to him. You acted foolishly in this; from now on you will have wars." Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.”
10 Asa raged at the seer for this and jailed him in the stocks, for he was furious with him about it; he also brutally oppressed some people at that time. Sai Asa ya yi fushi sosai da mai duban saboda wannan; ya yi fushi ƙwarai har ya sa aka jefa shi a kurkuku. A lokaci guda kuma Asa ya fara gwada wa mutane azaba.
11 Asa's acts, first to last, are written in the Book of the Kings of Judah and Israel. Ayyukan mulkin Asa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.
12 In his thirty-ninth year of reign, Asa's feet grew diseased, the disease severe. Yet even in his illness he did not seek our Father, but only the doctors. A shekara ta talatin da tara ta mulkinsa, Asa ya kamu da wata cuta a ƙafarsa. Ko da yake cutar ta yi tsanani, duk d haka ma a cikin ciwonsa bai nemi taimako daga Ubangiji ba, sai dai daga likitoci.
13 Then Asa rested with his fathers, dying in the forty-first year of his reign. Sa’an nan a shekara ta arba’in da ɗaya ta mulkinsa, Asa ya mutu ya kuma huta tare da kakanninsa.
14 They buried him in his own tomb, cut for himself in the City of David, laid him on a funeral bed covered with spices and various blended perfumes prepared by skilled perfumers, and lit a great fire for him. Suka binne shi a kabarin da ya fafe wa kansa a Birnin Dawuda. Suka sa shi a makara wadda aka rufe da kayan yaji da kuma turare dabam-dabam da aka niƙa, suka kuma ƙuna babbar wuta don girmama shi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]