Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Ruth 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Naomi had a relative through her husband, a prominent, wealthy man from Elimelech's clan, named Boaz. To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz.
2 Ruth the Moabite said to Naomi, "Let me glean grain behind anyone who favors me." She said, "Go, my daughter." Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je, ’yata.”
3 So she went out and gleaned behind the harvesters, and she happened to come to the field belonging to Boaz, of Elimelech's family. Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek.
4 Just then Boaz came from Bethlehem, telling the harvesters, "May our Father be with you." "Our Father bless you," they replied. Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!”
5 Then Boaz said to his foreman, "Whose young woman is this?" Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?”
6 The foreman answered, "She's the young Moabite woman who returned with Naomi from Moab's country. Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi.
7 She said, 'Please let me glean and gather among the sheaves behind the harvesters.' She came and has stayed from morning till now, resting only briefly in the shelter." Ta ce, ‘Ina roƙo a bar ni in bi bayan masu girbin in yi kala.’ Haka ta shiga cikin gonar ta kuwa yi aiki tun da safe har zuwa yanzu, sai ɗan hutun da ta yi kaɗan.”
8 Boaz said to Ruth, "Listen, my daughter. Don't glean in another field or leave here; stay close to my young women. Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da ’yan matana bayi.
9 Watch the field they harvest and follow behind them. I've told the young men not to touch you. When thirsty, drink from the jars the young men filled." Ki lura da gonar da mutanena suke girbi, ki bi su tare da ’yan matana. Na riga na faɗa wa mazan kada su taɓa ke. Kuma duk sa’ad da kika ji ƙishirwa, ki tafi ki ɗebo ruwa daga tulunan da mazan suka cika.”
10 She bowed facedown to the ground and asked him, "Why have I found favor in your eyes that you notice me, a foreigner?" Jin haka, sai ta rusuna da fuskata har ƙasa ta ce, “Me ya sa na sami irin wannan tagomashi a idanunka da har ka lura da ni, ni da nake baƙuwa?”
11 Boaz answered, "I've heard all you did for your mother-in-law since your husband died—how you left your father, mother, and homeland to come to a people you didn't know before. Bowaz ya amsa, “An faɗa mini duka game da abin kika yi domin surukarki tun mutuwar mijinki, yadda kika bar mahaifinki da mahaifiyarki da kuma ƙasarki kika zo ki yi zama da mutanen da ba ki taɓa sani ba.
12 May our Father repay your deed; may our Father, the God of Israel, under whose wings you've come for refuge, reward you fully." Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka.”
13 "May I find favor in your eyes, my lord," she said, "for you've comforted me and spoken kindly to your servant, though I'm not one of your servants." Ta ce, “Bari in ci gaba da samun tagomashi a idanunka ranka yă daɗe. Ka ta’azantar da ni ka kuma yi wa baranyarka magana mai alheri ko da yake ban kai matsayi ɗaya daga cikin bayinka ’yan mata ba.”
14 At mealtime Boaz said, "Come here, eat some bread, dip your piece in the wine vinegar." She sat beside the harvesters; he passed her roasted grain. She ate her fill and had some left. A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.
15 When she rose to glean, Boaz ordered his young men, "Let her glean even among the sheaves; don't shame her. Da ta tashi don tă yi kala, sai Bowaz ya yi umarni wa samarinsa cewa, “Ko ta tara daga cikin dammuna, kada ku wulaƙanta ta.
16 Instead, pull stalks from the bundles for her and leave them for her to pick up, and don't correct her." Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.”
17 She gleaned in the field till evening, then beat out what she'd gathered—about twenty quarts of barley. Saboda haka Rut ta yi kala a gonar har yamma. Sa’an nan ta sussuka hatsin sha’ir da ta kalata ta sami kamar efa.
18 She carried it to town; her mother-in-law saw how much she'd gleaned. She also brought out and gave her what she'd saved after eating her fill. Ta ɗauka ta koma gari sai surukarta ta ga yawan abin da ta kalato. Rut kuma ta fitar da ragowar abin da ta ci bayan ta ƙoshi ta ba ta.
19 Her mother-in-law asked, "Where did you gather today? Where did you work? Blessed be the man who noticed you!" Ruth named whose field: "The man I worked with today is Boaz." Surukarta ta tambaye ta, “Ina kika yi kala a yau? Ina kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga mutumin nan ta ya lura da ke!” Sai Rut ta faɗa wa surukarta game da wurin wanda ta yi ta aiki. Ta ce, “Sunan mutumin da na yi aiki da shi a yau Bowaz ne.”
20 Naomi told her daughter-in-law, "May our Father bless him, whose kindness hasn't left the living or the dead." She added, "He's a close relative, one of our redeemers." Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.”
21 Then Ruth the Moabite said, "He even told me, 'Stay with my workers until they finish all my harvest.'" Sa’an nan Rut mutuniyar Mowab ta ce, “Ya ma ce mini, ‘Ki riƙa bin ma’aikatana sai sun ƙare yin girbin dukan hatsina.’ ”
22 Naomi told her daughter-in-law Ruth, "Good, my daughter—go out with his young women, so you won't be harmed in another field." Na’omi ta ce wa Rut surukarta, “Zai fi miki kyau, ’yata ki riƙa tafiya da ’yan matansa, domin a gonar wani dabam mai yiwuwa a yi miki lahani.”
23 She stayed close to Boaz's young women, gleaning until the barley and wheat harvests ended, and lived with her mother-in-law. Saboda haka Rut ta tsaya kusa da bayi mata na Bowaz don tă yi kala sai da girbin sha’ir da na alkama suka ƙare. Ta kuwa zauna tare da surukarta.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]