Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 32 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The sons of Reuben and sons of Gad had vast herds of livestock. Seeing the land of Jazer and land of Gilead, they noticed it suited livestock well. Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.
2 The sons of Gad and sons of Reuben came and said to Moses, to Eleazar the priest, and to the community's leaders: Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce,
3 "Ataroth, Dibon, Jazer, Nimrah, Heshbon, Elealeh, Sebam, Nebo, and Beon, “Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon,
4 the land our Father struck down before Israel's community—is land for livestock, and your servants have livestock." ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban mutane Isra’ila, suna da kyau don dabbobi, bayinku kuma suna da dabbobi.”
5 They said, "If we have found favor in your eyes, give this land to your servants as a possession. Don't make us cross the Jordan." Suka ce, “In mun sami tagomashi daga gare ka bari a ba da wannan ƙasa ga bayinka, tă zama mallakanmu. Kada ka sa mu haye Urdun.”
6 Moses said to the sons of Gad and Reuben, "Should your brothers go to war while you sit here? Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan?
7 Why discourage Israel from crossing into the land our Father has given them? Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?
8 This is what your fathers did when I sent them from Kadesh-barnea to see the land. Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh Barneya don su dubo ƙasar.
9 They went up to the Valley of Eshcol, saw the land, then discouraged the Israelites' hearts from entering the land our Father had given them. Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.
10 And our Father's anger burned that day, and he swore an oath, saying, A ranar kuwa Ubangiji ya husata har ya yi wannan rantsuwa cewa,
11 surely the men who came up from Egypt, twenty years old and up, will not see the land I swore to give to Abraham, to Isaac, and to Jacob—because they did not fully follow me. ‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba,
12 None but Caleb son of Jephunneh the Kenizzite and Joshua son of Nun, for they fully followed our Father. ba ko ɗaya sai dai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze da Yoshuwa ɗan Nun, don su ne kaɗai suka bi Ubangiji da zuciya ɗaya.’
13 The anger of our Father burned against Israel; he made them wander the wilderness forty years until the whole generation that had done evil before our Father had died. Ubangiji ya husata da Isra’ila har ya sa suka yi ta yawo a hamada shekara arba’in, sai da dukan tsaran da suka aikata wannan mugunta a gabansa, suka mutu.
14 Now you have risen up in place of your fathers, a brood of sinners, adding still more to our Father's fierce anger against Israel! “Ga shi ku kuma, tarin masu zunubi, kuna tsaya a matsayin kakanninku, kuna sa Ubangiji yă sāke husata da Isra’ila.
15 If you turn from following him, he will leave them in the wilderness once again, and you will destroy all this people." In kun juye daga binsa, zai sāke barin dukan wannan mutane a hamada, ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakarsu.”
16 They came to him and said, "We'll build pens here for our livestock and cities for our children. Sai suka zo wurin Musa, suka ce, “Muna so mu gina katangar dutse don dabbobinmu, da kuma birane don matanmu da ’ya’yanmu a nan.
17 But we will arm ourselves, ready to go ahead of the Israelites until we bring them to their place, while our children stay in fortified cities, safe from those living in the land. Matanmu da ’ya’yanmu za su zauna a biranen da suke da katanga, don kāriya daga mazaunan ƙasar, amma mu, za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra’ilawa, har mu kai su wuraren zamansu.
18 We will not return home until every Israelite has taken his inheritance. Ba za mu koma gidajenmu ba sai kowane mutumin Isra’ila ya sami gādonsa.
19 We won't inherit with them across the Jordan and beyond, since our inheritance has come to us on this side of the Jordan, to the east." Ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayin gabashin Urdun.”
20 Moses said to them, "If you do this—if you arm yourselves before our Father for the war, Sai Musa ya ce musu, “In za ku yi haka, in za ku sha ɗamara da makamai a gaban Ubangiji, ku tafi yaƙi,
21 and every armed man among you crosses the Jordan before our Father until he drives out his enemies from before him, in kuma dukanku za ku yi ɗamara, ku ɗauki makaman yaƙi a hayin Urdun a gaban Ubangiji har lokacin da ya kori abokan gābansa daga gabansa,
22 and the land is subdued before our Father, afterward you may return and be free of obligation to him and to Israel, and this land will be your possession before our Father. to, sa’ad da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji, kwa kuɓuta daga alhakinku ga Ubangiji da kuma Isra’ila. Ƙasan nan kuwa za tă zama mallakarku a gaban Ubangiji.
23 But if you don't do this, look—you will have sinned against our Father, and know: your sin will overtake you. “Amma in ba ku yi haka ba, kun yi zunubi ke nan ga Ubangiji; kuma ku san cewa zunubinku zai tone ku.
24 Build cities for your little ones, pens for your flocks, and do what your mouth has promised." Ku gina birane domin matanku da ’ya’yanku, ku gina katanga kuma domin dabbobinku, amma fa ku cika abin da kuka yi alkawari.”
25 The sons of Gad and Reuben said to Moses, "Your servants will do as my lord commands. Mutanen Gad da mutanen Ruben, suka ce wa Musa, “Mu bayinka za mu yi yadda ranka yă daɗe ya umarta.
26 Our children, wives, flocks, and all our herds will stay there in the cities of Gilead, ’Ya’yanmu da matanmu, garkunan shanunmu da na tumakinmu, za su kasance a nan biranen Gileyad.
27 but your servants, every man armed for war, will cross before our Father to battle, as my lord says." Amma bayinka, kowane mutum a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji, zuwa yaƙi kamar yadda ranka yă daɗe ya faɗa.”
28 So Moses commanded Eleazar the priest, Joshua son of Nun, and the clan leaders of Israel's tribes about them. Sai Musa ya yi wa Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu,
29 Moses said to them, "If Gad's and Reuben's sons cross the Jordan with you, every man armed for battle before our Father, and the land is subdued before you, then give them Gilead as their possession. ya ce, “In kowane sojan mutanen Gad da na mutanen Ruben, ya ɗauki makaman yaƙi, ya haye Urdun tare da ku a gaban Ubangiji, to, sa’ad da a ci ƙasar a gabanku, ku ba da ƙasar Gileyad tă zama mallakarsu.
30 But if they won't cross over armed with you, they must take possession among you in the land of Canaan." Amma in ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo a wancan haye kamar sauran kabilun a Kan’ana.”
31 Gad's and Reuben's sons answered, "We will do as our Father told your servants. Mutanen Gad da mutanen Ruben suka amsa, suka ce, “Barorinka za su yi abin da Ubangiji ya faɗa.
32 We ourselves will cross armed before our Father into the land of Canaan, and our inherited possession will remain ours beyond the Jordan." Za mu haye a gaban Ubangiji zuwa Kan’ana, amma mallakarmu ta gādo, za tă kasance a wannan hayi na Urdun.”
33 Moses gave to them—the sons of Gad, the sons of Reuben, and the half-tribe of Manasseh son of Joseph—the kingdom of Sihon king of the Amorites and the kingdom of Og king of Bashan: the land, its cities, the territories, and the cities of the country around. Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.
34 And the sons of Gad built Dibon, Ataroth, Aroer, Mutanen Gad suka gina Dibon, Atarot, Arower,
35 Atroth-shophan, Jazer, Jogbehah, Atrot Shofan, Yazer, Yogbeha,
36 Beth-nimrah, and Beth-haran—fortified cities and pens for sheep. Bet-Nimra, da Bet-Haran a matsayin birane masu katanga, suka kuma gina katanga don dabbobinsu.
37 And the sons of Reuben built Heshbon, Elealeh, Kiriathaim, Mutanen Ruben suka sāke gina Heshbon, Eleyale, da Kiriyatayim,
38 Nebo, Baal-meon (renamed), and Sibmah—they gave the cities they rebuilt new names. haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye.
39 Sons of Machir son of Manasseh went to Gilead, captured it, and drove out the Amorites living there. Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can.
40 So Moses gave Gilead to Machir son of Manasseh, and he settled in it. Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can.
41 And Jair son of Manasseh went and captured their villages, and called them Havvoth-jair. Yayir, wani ɗan Manasse, ya ci ƙauyukansu da yaƙi, ya kuma ba su sunan Hawwot Yayir.
42 And Nobah went and captured Kenath and its villages, and called it Nobah, after his own name. Noba kuma ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya kuma ba ta suna Noba, bisa ga sunansa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]