Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 29 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 "In the seventh month, on the first day, hold a holy assembly. Do no ordinary work; it is a day for you to sound the trumpets. “ ‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni.
2 Offer a burnt offering, a pleasing aroma to our Father: one young bull, one ram, seven male lambs a year old, all without defect. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji, duka su kasance marasa lahani.
3 Their grain offering: fine flour mixed with oil—about six quarts for the bull, about four quarts for the ram, Tare da bijimin za a kuma miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;
4 and about two quarts for each of the seven lambs; kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
5 and one male goat as a sin offering, to make atonement for you. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.
6 Besides the new-moon burnt offering and its grain offering, the daily burnt offering and its grain offering, and their drink offerings, by their rule—a soothing aroma, a fire offering to our Father. Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi.
7 "On the tenth day of this seventh month, hold a sacred gathering and practice self-denial; do no work at all. “ ‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba.
8 Present a burnt offering to our Father as a pleasing aroma: one young bull, one ram, and seven male lambs a year old, all without blemish. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma ’yan raguna bakwai, ’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
9 Their grain offering: fine flour mixed with oil—about six quarts for the bull, about four quarts for the one ram, Tare da bijimin a miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai;
10 and about two quarts for each of the seven lambs; kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
11 also one male goat as a sin offering, besides the atonement sin offering, the regular burnt offering, its grain offering, and their drink offerings. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu.
12 "On the fifteenth day of the seventh month, hold a holy assembly. Do no ordinary work; celebrate a feast to our Father for seven days. “ ‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai.
13 Present a burnt offering, a fire offering, a pleasing aroma to our Father: thirteen young bulls, two rams, fourteen male lambs a year old, all without defect. A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
14 Their grain offering: fine flour mixed with oil—about six quarts for each of the thirteen bulls, about four quarts for each of the two rams, Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;
15 and about two quarts for each of the fourteen lambs; tare kuma da kowane ’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma.
16 and one male goat as a sin offering, besides the daily burnt offering, its grain offering, and its drink offering. A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha.
17 "On the second day: twelve young bulls, two rams, fourteen year-old male lambs, all without defect, “ ‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
18 with their grain and drink offerings for the bulls, the rams, and the lambs, by number, as required; Tare da bijiman, ragunan da ’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.
19 also one male goat as a sin offering, besides the regular burnt offering, its grain offering, and their drink offerings. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha.
20 "On the third day: eleven bulls, two rams, fourteen year-old male lambs, all without defect, “ ‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
21 with their grain and drink offerings for the bulls, rams, and lambs, by number, as required. Tare da bijiman, ragunan da ’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.
22 One male goat as a sin offering, besides the regular burnt offering with its grain and drink offerings. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
23 "Fourth day: ten bulls, two rams, fourteen year-old male lambs, all without defect, “ ‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
24 with grain and drink offerings for the bulls, rams, and lambs, by their number, as required; Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
25 plus one male goat as a sin offering, besides the daily burnt offering with its grain and drink offerings. A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
26 "On the fifth day: nine bulls, two rams, fourteen year-old male lambs, all without defect, “ ‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
27 with grain and drink offerings for the bulls, rams, and lambs, by number, as required. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
28 Also one male goat as a sin offering, besides the continual burnt offering, its grain offering, and its drink offering. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
29 "Sixth day: eight bulls, two rams, fourteen year-old male lambs, all without defect, “ ‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
30 with their grain offering and drink offerings for the bulls, rams, and lambs, by number, as required; Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade.
31 and one male goat as a sin offering, besides the regular burnt offering, its grain offering, and its drink offerings. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha.
32 "On the seventh day: seven bulls, two rams, fourteen year-old male lambs, all without defect, “ ‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
33 with their grain and drink offerings for the bulls, rams, and lambs, by number, as prescribed; Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade.
34 and one male goat as a sin offering, besides the daily burnt offering, its grain offering and its drink offering. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
35 "On the eighth day, hold a closing assembly; do no laborious work. “ ‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba.
36 Present a burnt offering, a fire offering, a pleasing aroma to our Father: one bull, one ram, seven male lambs a year old, all without defect, A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, a yi hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
37 with their grain and drink offerings for the bull, ram, and lambs, by number, as prescribed. Tare da bijimin, ragon da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
38 One male goat for a sin offering, besides the continual burnt offering, its grain offering and its drink offering. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
39 "Offer these to our Father at your appointed feasts, besides your vow and voluntary offerings—whether burnt, grain, drink, or peace offerings." “ ‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga Ubangiji a lokacin bukukkuwanku, hadayunku na ƙonawa, hadayu na gari, hadayu na sha da hadayu na salama.’ ”
40 Moses told the Israelites everything, just as our Father had commanded Moses. Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]