Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Our Father spoke to Moses in the Sinai wilderness, in the tent of meeting, on the first day of the second month of the second year after they left the land of Egypt. He said: Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,
2 "Count the whole community of Israel's people, by clans and fathers' houses—every male, by name, head by head. “Ka yi ƙidayan dukan al’umman Isra’ilawa bisa ga iyalansu da kabilarsu, ka rubuta kowa da sunansa bi da bi.
3 Register everyone in Israel twenty and older who can serve in the army—you and Aaron—by their divisions. Da kai da Haruna za ku lissafta dukan mazan Isra’ila bisa ga sashensu, waɗanda suka kai shekaru ashirin ko fiye, da za su iya shiga soja.
4 A man from each tribe is to be with you, each one the head of his family. Mutum ɗaya daga kowace kabila wanda yake shugaban danginsa, zai taimake ku.
5 "Names of the men who will stand with you: from Reuben, Elizur son of Shedeur. “Ga sunayen da za su taimake ku. “Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur;
6 "From Simeon, Shelumiel son of Zurishaddai; daga kabilar Simeyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai;
7 "From Judah, Nahshon son of Amminadab; daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;
8 "From Issachar, Nethanel son of Zuar; daga kabilar Issakar, Netanel ɗan Zuwar;
9 "From Zebulun, Eliab son of Helon; daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon;
10 "From the sons of Joseph: from Ephraim, Elishama son of Ammihud; from Manasseh, Gamaliel son of Pedahzur; daga kabilar ’ya’yan Yusuf, daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud; daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;
11 "From Benjamin, Abidan son of Gideoni; daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gideyoni;
12 "From Dan, Ahiezer son of Ammishaddai; daga kabilar Dan, Ahiyezer ɗan Ammishaddai;
13 "From Asher, Pagiel son of Ochran; daga kabilar Asher, Fagiyel ɗan Okran;
14 "From Gad, Eliasaph son of Deuel; daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Deyuwel;
15 "From Naphtali, Ahira son of Enan. daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan.”
16 "These were the community's called ones, leaders of their ancestral tribes, heads of Israel's clans." Waɗannan su ne mutanen da aka naɗa daga cikin jama’a, shugabannin asalin kabilu. Su ne kuma shugabannin dangogin Isra’ila.
17 So Moses and Aaron took these men who had been designated by name, Sai Musa da Haruna suka ɗauki sunayen mutanen nan da aka ba su,
18 on the first day of the second month they gathered the whole community. The people registered their ancestry by clan and family—every male twenty years old and older, listed by name, one by one, suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye,
19 as our Father had commanded Moses. So Moses counted them in the wilderness of Sinai. yadda Ubangiji ya umarci Musa. Da haka ya ƙidaya su a Hamadar Sinai.
20 From Reuben's descendants, Israel's firstborn: recorded by clan and family, name by name, every male twenty years old and up, able to serve in war. Daga zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
21 Those counted from the tribe of Reuben were 46,500. Jimillar maza daga mutanen Ruben 46,500 ne.
22 Simeon's descendants, by clans and families, counted by name, head by head: every male twenty years old and up, fit for the army. Daga zuriyar Simeyon. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
23 Those counted from the tribe of Simeon were 59,300. Jimillar maza daga mutanen Simeyon 59,300 ne.
24 From Gad's descendants: by clans, families, and names, every man twenty and older fit for military service. Daga zuriyar Gad. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
25 Those counted from the tribe of Gad were 45,650. Jimillar maza daga mutanen Gad 45,650 ne.
26 Judah's descendants, listed by clans and families, by name, every man twenty and older able to serve in the army: Daga zuriyar Yahuda. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
27 those counted from the tribe of Judah were 74,600. Jimillar maza daga mutanen Yahuda 74,600 ne.
28 Issachar's descendants, listed by clan and family, by name, every man twenty years and older fit for war: Daga zuriyar Issakar. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
29 those counted from the tribe of Issachar were 54,400. Jimillar maza daga mutanen Issakar 54,400 ne.
30 Zebulun's descendants: registered by clan and family, by name, every man twenty years old or older fit for military service. Daga zuriyar Zebulun. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
31 Those counted from the tribe of Zebulun were 57,400. Jimillar maza daga mutanen Zebulun 57,400 ne.
32 Sons of Joseph, Ephraim's line: recorded by clan and family, by name, every man twenty and older fit for military service. Daga ’ya’yan Yusuf. Daga zuriyar Efraim. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
33 Those counted from the tribe of Ephraim were 40,500. Jimillar maza daga mutanen Efraim 40,500 ne.
34 Manasseh's descendants, listed by clans and families, by name, each man twenty years or older able to serve in the army: Daga zuriyar Manasse. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
35 those counted from the tribe of Manasseh were 32,200. Jimillar maza daga mutanen Manasse 32,200 ne.
36 From Benjamin's descendants, recorded by clan and family, by name, every man twenty years old and older, fit for military service: Daga zuriyar Benyamin. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
37 those counted from the tribe of Benjamin were 35,400. Jimillar maza daga mutanen Benyamin 35,400 ne.
38 From Dan's descendants, listed by clan and family, by name, every man twenty years old and older fit for war: Daga zuriyar Dan. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
39 those counted from the tribe of Dan were 62,700. Jimillar maza daga mutanen Dan 62,700 ne.
40 Asher's descendants, listed by clan and family, by name: every man twenty years old and up, fit for military service. Daga zuriyar Asher. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
41 Those counted from the tribe of Asher were 41,500. Jimillar maza daga mutanen Asher 41,500 ne.
42 Naphtali's descendants: by clan and family, counted by name, every man twenty and older fit for war. Daga zuriyar Naftali. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
43 Those counted from the tribe of Naphtali were 53,400. Jimillar maza daga mutanen Naftali kuwa 53,400 ne.
44 Moses, Aaron, and Israel's twelve leaders counted these men, each for his family. Waɗannan su ne mazan da Musa da Haruna, tare da shugabanni goma sha biyun nan na Isra’ila suka ƙidaya, kowa a madadin iyalinsa.
45 All Israel's people were counted by families, every man twenty years old and older, fit to serve in Israel's army. Dukan Isra’ilawan da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, an ƙidaya su bisa ga iyalansu.
46 All those counted came to 603,550. Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550.
47 But the Levites were not counted among them by their ancestral tribe. Ba a dai ƙidaya zuriyar Lawi tare da saura kabilan ba.
48 For our Father had said to Moses: Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa,
49 "Do not count the tribe of Levi or list them among the Israelites. “Ka tabbatar ba ka ƙidaya mutanen Lawi ko kuma ka haɗe su tare a ƙidayan sauran Isra’ilawa ba.
50 Instead, put the Levites in charge of the tabernacle of the testimony, all its furnishings, and everything belonging to it. They must carry the tabernacle and its furnishings, care for it, and camp around it. A maimakon haka sai ka naɗa Lawiyawa su lura da tabanakul Shaida, wato, kan dukan kayayyaki da kuma kome da yake na wuri mai tsarki. Za su ɗauko tabanakul da dukan kayayyakinsa; za su lura da shi, su kasance kewaye da shi.
51 When the tabernacle sets out, Levites take it down; when it is pitched, Levites set it up. Any outsider who comes near is to be put to death. Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi.
52 Israel's people are to camp, each by his own camp, each under his own banner, by their companies. Sauran Isra’ilawa za su zauna ƙungiya-ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa daidai bisa ga ƙa’idarsa.
53 The Levites must camp around the tabernacle of the testimony, so no wrath falls on the Israelite community; the Levites are to guard the tabernacle of the testimony." Amma Lawiyawa za su kafa sansaninsu kewaye da tabanakul na Shaida. Don kada fushi yă fāɗo a kan al’ummar Isra’ilawa. Hakkin Lawiyawa ne su kula da tabanakul na Shaida.”
54 The people of Israel did everything our Father had commanded Moses; that is exactly what they did. Isra’ilawa suka yi duk waɗannan kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]