Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Matthew 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 "Do not judge, so that you may not be judged. “Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma.
2 For you'll be judged by the judgment you use, and measured by the measure you give. Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.
3 Why look at the speck in your brother's eye but miss the log in your own? “Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido?
4 Or how can you tell your brother, 'Let me remove the speck from your eye,' when a log is in yours? Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido?
5 Hypocrite, first remove the log from your own eye; then you'll see clearly to remove the speck from your brother's eye. Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.
6 "Don't give dogs what is holy, or throw your pearls before pigs—they'll trample them underfoot, then turn and tear you apart. “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo.
7 "Ask, and you'll receive it; seek, and you'll find; knock, and it'll open for you. “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.
8 For everyone who asks receives, whoever seeks finds, and whoever knocks, it will be opened. Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.
9 Or what person among you, if his son asks him for bread, will give him a stone? “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse?
10 Or if he asks for a fish, will give him a snake? Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji?
11 So if you, being evil, know how to give your children good gifts, how much more will your Father in heaven give good things to those who ask him? In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!
12 "So in everything, treat people the way you want them to treat you; for this is the Law and the Prophets. Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.
13 "Enter through the narrow gate, for the gate is wide, the road broad, leading to destruction, and many enter through it. “Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa.
14 But the gate is narrow, the road narrow, that leads to life; few find it. Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.
15 "Beware false prophets: they come to you in sheep's clothing but are ravenous wolves inside. “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne.
16 By their fruit you will recognize them. Are grapes gathered from thornbushes, or figs from thistles? Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?
17 In the same way, every good tree bears good fruit, but the bad tree bears bad fruit. Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.
18 A good tree cannot bear bad fruit, nor can a bad tree bear good fruit. Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.
19 Every tree that does not bear good fruit is cut down and thrown into the fire. Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta.
20 So then, by their fruit you will recognize them. Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”
21 "Not everyone who says to me, 'Lord, Lord,' will enter the kingdom of our Father, but the one who does the will of my Father in heaven. “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.
22 Many will say to me on that day, 'Lord, Lord, didn't we prophesy in your name, drive out demons in your name, do many miracles in your name?' Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’
23 Then I will tell them plainly: 'I never knew you; get away from me, you lawbreakers.' Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’
24 "So anyone who hears these words of mine and does them will be like a wise man whose house was built on the rock. “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.
25 Rain fell, floods came, winds blew and beat against that house, but it didn't fall, because it was founded on rock. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.
26 And everyone who hears these words of mine and doesn't do them is like a foolish man who built his house on sand. Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.
27 The rain fell, floods came, winds blew and hit that house, and it fell—and its fall was great." Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”
28 When Jesus had finished saying these words, the crowds were astonished at his teaching, Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa,
29 because he was teaching them as one who had authority, and not as their scribes. domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]