Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Matthew 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Seeing the crowds, Jesus went up the mountain; when he sat down, his disciples came to him. Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa,
2 And he opened his mouth and began to teach them, saying: sai ya fara koya musu. Yana cewa,
3 "Blessed are the poor in spirit, for theirs is the kingdom of our Father. “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.
4 Blessed are those who mourn, for they will be comforted. Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.
5 Blessed are the meek, for they will inherit the earth. Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u, gama za su gāji duniya.
6 Blessed are those who hunger and thirst for righteousness, for they will be satisfied. Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su.
7 Blessed are the merciful, for they will receive mercy. Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.
8 Blessed are the pure in heart, for they will see our Father. Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.
9 Blessed are the peacemakers, for they will be called children of our Father. Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah.
10 Blessed are those who are persecuted for righteousness' sake, for theirs is the kingdom of our Father. Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne.
11 "Blessed are you when people insult, persecute, and lie about every kind of evil against you because of me. “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.
12 Rejoice and be glad, for your reward is great in heaven, for they persecuted the prophets before you the same way. Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.
13 "You are the salt of the earth. But if salt loses its taste, how can it be salted again? It's no longer good for anything but being thrown out and trampled by people. “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
14 "You are the light of the world. A city set on a hill cannot be hidden. “Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.
15 No one lights a lamp and puts it under a basket, but sets it on a stand to light everyone in the house. Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.
16 Likewise, let your light shine before people, so they see your good works and glorify your Father in heaven. Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.
17 "Don't think I came to abolish the Law or the Prophets—I didn't come to abolish them, but to fulfill them. “Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.
18 For truly I tell you: until heaven and earth pass, not one letter, not one stroke, will pass from the Law until everything is done. Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome.
19 So whoever breaks one of these least commands and teaches others the same will be called least in the kingdom of our Father; but whoever keeps and teaches them will be called great in the kingdom of our Father. Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.
20 For I tell you, unless you are more righteous than the scribes and Pharisees, you'll never enter the kingdom of our Father. Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.
21 "You've heard that it was said to those of old, 'Do not murder; whoever murders is subject to judgment.' “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’
22 But I tell you: whoever is angry with his brother risks judgment. Whoever insults his brother risks the council, and whoever says, 'You fool!' risks fiery hell. Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.
23 "So if you're offering your gift at the altar and recall there that your brother has something against you, “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci,
24 leave your gift there before the altar, go make peace with your brother first, then come offer your gift. sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.
25 Make peace with your accuser quickly, while still on the way with him, or he may hand you over to the judge, the judge to the officer, and you may be thrown into prison. “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.
26 Truly I tell you, you will never get out until you have paid the last penny. Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.
27 "You have heard that it was said, 'You shall not commit adultery.' “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’
28 But I tell you: everyone who looks at a woman lustfully has already committed adultery with her in his heart. Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.
29 If your right eye makes you stumble, tear it out and throw it away—better to lose one part of your body than have your whole body thrown into hell. In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
30 If your right hand makes you sin, cut it off and throw it away. Better to lose one part of you than have your whole body go into hell. In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
31 "It was also said, 'Whoever divorces his wife must give her a certificate of divorce.' “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’
32 I tell you: whoever divorces his wife, except for sexual sin, makes her a victim of adultery; and whoever marries a divorced woman commits adultery. Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.
33 "Again, you've heard it was said to the ancients: 'Don't break your oath—fulfill it to our Father.' “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’
34 But I tell you, do not swear an oath at all: neither by heaven, for it is our Father's throne, Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne;
35 nor by the earth, for it's the footstool for his feet, nor by Jerusalem, for it's the city of the great King. ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne.
36 And do not swear by your head, for you cannot make a single hair white or black. Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba.
37 Let your 'Yes' be 'Yes,' and your 'No,' 'No'; anything beyond this comes from the evil one. Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
38 "You have heard that it was said, 'Eye for eye and tooth for tooth.' “Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’
39 But I tell you: don't resist an evil person. If someone slaps your right cheek, turn the other cheek to him too. Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma.
40 If anyone wants to sue you and take your tunic, let him have your cloak too. In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma.
41 And if anyone forces you to go one mile, go with him two. In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu.
42 Give to whoever asks you, and don't turn away whoever wants to borrow from you. Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.
43 "You have heard that it was said, 'You will love your neighbor and hate your enemy.' “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’
44 But I tell you, love your enemies and pray for those who persecute you, Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,
45 so you may become children of your Father in heaven, because he makes his sun rise on evil and good and sends rain on just and unjust. don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.
46 If you love those who love you, what reward is that? Don't even tax collectors do the same? In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?
47 If you greet only your brothers, what more do you do than others? Don't even the Gentiles do that? In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?
48 Be perfect, therefore, as your heavenly Father is perfect." Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]