Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Matthew 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 After Jesus was born in Bethlehem, Judea, in the days of King Herod, magi from the east arrived in Jerusalem, Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima
2 saying, "Where is the one born king of the Jews? For we saw his star in the east and have come to worship him." suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”
3 When Herod the king heard this, he was troubled, and all Jerusalem with him. Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima.
4 He gathered all the people's chief priests and scribes, asking where the Christ was to be born. Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi.
5 They told him, "In Bethlehem of Judea, for this is what was written through the prophet: Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta.
6 'Yet you, Bethlehem, in Judah's land, are certainly not the least among Judah's rulers; for from you a ruler will emerge who will shepherd Israel, my people.'" “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’”
7 Then Herod secretly summoned the magi and learned from them the exact time the star had appeared. Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, yă gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana.
8 He sent them to Bethlehem, saying, "Go, search carefully for the child. When you find him, come back and tell me, so that I too may go and worship him." Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”
9 After hearing the king, they set out; the star they had seen in the east went ahead of them until it stopped over where the child was. Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake.
10 When they saw the star, they rejoiced with overwhelming joy. Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai.
11 Entering the house, they saw the child with Mary his mother, fell down and worshiped him. They opened their treasure boxes and gave him gifts: gold, frankincense, and myrrh. Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.
12 Warned in a dream not to return to Herod, they went back to their own country by a different route. Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
13 After they left, an angel of our Father appeared to Joseph in a dream: "Get up, take the child and his mother, flee to Egypt, and stay until I tell you—Herod is about to search for the child to kill him." Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”
14 And he got up and took the child and his mother by night and left for Egypt, Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar,
15 and stayed there until Herod died, fulfilling what our Father said through the prophet: "Out of Egypt I called my son." inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.”
16 Then Herod, seeing the magi had outwitted him, grew furious and sent men to kill all boys two years old and under in Bethlehem and its whole region, matching the time he'd learned from the magi. Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.
17 This fulfilled what was spoken through Jeremiah the prophet: Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa,
18 "A voice was heard in Ramah, weeping and loud mourning, Rachel weeping for her children; she refused to be comforted, because they are no more." “An ji murya a Rama, tana kuka da makoki mai tsanani, Rahila ce take kuka domin ’ya’yanta, an kāsa ta’azantar da ita, don ba su.”
19 But when Herod died, an angel of our Father appeared in a dream to Joseph in Egypt, Bayan Hiridus ya mutu, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar,
20 saying, "Get up, take the child and his mother, go to Israel's land, for those seeking the child's life are dead." ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Isra’ila, domin waɗanda suke neman ran yaron sun mutu.”
21 So he got up, took the child and his mother, and went to Israel's land. Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Isra’ila.
22 Hearing that Archelaus was ruling Judea in place of his father Herod, he was afraid to go there. Warned in a dream, he withdrew to the region of Galilee. Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili,
23 He went and lived in a town called Nazareth, fulfilling the prophets' words: "He will be called a Nazarene." ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazare.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]