Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 11 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Nearing Jerusalem, at Bethphage and Bethany by the Mount of Olives, Jesus sent two of his disciples ahead, Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa,
2 telling them, "Go into the village ahead of you, and as soon as you enter it, you'll find a tied colt no one has ever ridden. Untie it and bring it here." ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan.
3 If anyone asks you, 'Why are you doing this?' say, 'The Lord needs it and will send it back here at once.' In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ ”
4 They went and found a colt tied at a doorway outside in the street, and untied it. Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan,
5 Some of those standing there asked them, "What are you doing, untying that colt?" sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?”
6 They answered as Jesus had told them, and the people let them go. Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su.
7 They brought the colt to Jesus and threw their cloaks over it, and he sat on it. Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa.
8 Many spread their cloaks on the road; others spread leafy branches cut from the fields. Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki.
9 Those who went ahead and those who followed were shouting, "Hosanna! Blessed is he who comes in the name of our Father! Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”
10 Blessed is the coming kingdom of our father David! Hosanna in the highest!" “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!”
11 Jesus entered Jerusalem and the temple, looked around at everything, and—since it was already late—went out to Bethany with the Twelve. Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.
12 The next day, as they were leaving Bethany, Jesus was hungry. Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.
13 Seeing a leafy fig tree in the distance, he went to see if it had anything on it. Reaching it, he found nothing but leaves, since it wasn't fig season. Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne.
14 Then he told it, "May no one ever eat fruit from you again." His disciples heard him say it. Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.
15 They arrived in Jerusalem, and Jesus entered the temple and began driving out the sellers and buyers there. He overturned the money-changers' tables and the seats of those selling doves, Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru,
16 and he would not allow anyone to carry merchandise through the temple courts. ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki.
17 And he taught them, saying, "Isn't it written: 'My house will be called a house of prayer for all the nations'? But you've made it a den of robbers." Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’”
18 The chief priests and scribes heard this and sought a way to destroy him, for they feared him, since the whole crowd was amazed at his teaching. Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
19 And when evening came, they went out of the city. Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka bar garin.
20 In the morning, as they passed by, they saw the fig tree withered from its roots. Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa.
21 Peter remembered and said to him, "Rabbi, look! The fig tree you cursed has withered." Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”
22 Jesus answered them, "Have faith in our Father. Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah.
23 Truly I tell you, whoever tells this mountain, 'Be lifted up and thrown into the sea,' without doubting in his heart but believing what he says will happen—it will be done for him. Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa.
24 So I tell you: whatever you pray and ask for, believe you've received it - it will be yours. Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
25 When you stand praying, forgive whatever you hold against anyone, so your Father in heaven may also forgive you your sins." A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”
27 They returned to Jerusalem. While Jesus walked in the temple, the chief priests, scribes, and elders came to him, Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa.
28 and asked, "By what authority are you doing this? Or who gave you this authority to do it?" Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”
29 Jesus said to them, "I'll ask you one question. Answer me, and I'll tell you by what authority I do these things. Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.
30 John's baptism—was it from heaven, or of human origin? Answer me." Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!”
31 They discussed it among themselves: "If we say, 'From heaven,' he'll ask, 'Then why didn't you believe him?' Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
32 But if we say, 'From humans'"—they feared the crowd, since all considered John a true prophet. In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.”
33 They answered Jesus, "We don't know." Jesus said, "Neither will I tell you by what authority I do these things." Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]