Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 17 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 After saying this, Jesus looked up to heaven and said: "Father, the hour has come. Glorify your Son, so the Son may glorify you, Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce, “Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka.
2 since you gave him authority over all people, to give eternal life to all you gave him. Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi.
3 This is eternal life: that they know you, the only true Father, and Jesus Christ whom you sent. Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko.
4 I glorified you on the earth, having finished the work you gave me to do. Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni.
5 Father, glorify me now with yourself, with the glory I had with you before the world existed. Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya.
6 I revealed your name to those you gave me from the world. They were yours; you gave them to me, and they have kept your word. “Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni a duniya. Su naka ne; kai ka ba ni su sun kuma yi biyayya da maganarka.
7 Now they know that everything you have given me is from you, Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito.
8 for I gave them the words you gave me; they received them, truly knew I came from you, and believed you sent me. Na ba su kalmomin da ka ba ni sun kuwa karɓa. Sun san tabbatacce daga wurinka na fito. Sun kuma gaskata kai ka aiko ni.
9 I pray for them, not for the world, but for those you gave me, since they are yours. Ina addu’a dominsu. Ba domin duniya nake addu’a ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne.
10 Everything mine is yours, and yours is mine, and I am glorified in them. Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu.
11 I'm no longer in the world, but they are in the world, and I'm coming to you. Holy Father, keep them in your name, the name you gave me, so they may be one as we are. Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya.
12 While with them, I kept them in your name you gave me. I guarded them—none was lost except the son of destruction, so Scripture would be fulfilled. Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.
13 Now I come to you, and I say these things in the world so they may have my joy completed in themselves. “Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu.
14 I've given them your word; the world hated them, since they're not of the world, just as I'm not of the world. Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne.
15 I don't ask you to remove them from the world, but to guard them from the evil one. Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan.
16 They are not of the world, just as I am not of the world. Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.
17 Make them holy by truth; your word is truth. Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.
18 As you sent me into the world, so I have sent them into the world. Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya.
19 For them I make myself holy, so they too may be made holy in truth. Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske.
20 I pray not only for these, but also for those who will believe in me through their word. “Addu’ata ba saboda masu bina kaɗai ba ne. Ina addu’a kuma saboda waɗanda za su gaskata da ni ta wurin maganarsu.
21 Father, let them all be one, as you're in me and I in you, so they're in us too, and the world believes you sent me. Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni.
22 The glory you have given me, I have given them, so they may be one as we are one. Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya.
23 I in them and you in me, so they may be made completely one, so the world may know you sent me and loved them as you loved me. Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.
24 Father, I want those you gave me to be with me where I am, to see my glory, which you gave me because you loved me before the world was made. “Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance tare da ni a inda nake, su kuma ga ɗaukakata, ɗaukakar da ka ba ni domin kana ƙaunata kafin halittar duniya.
25 Righteous Father—the world doesn't know you, but I know you, and these know you sent me. “Ya Uba Mai Adalci, ko da yake duniya ba tă san ka ba, ni na san ka, sun kuma san kai ka aiko ni.
26 I have made your name known to them, and will keep making it known, so the love you loved me with may be in them, and I in them." Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]