Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Genesis 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Then our Father told Noah, "Enter the ark with your whole household, for I've seen you righteous before me in this generation. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani.
2 Take for yourself seven pairs of every clean animal, male and female, and one pair of unclean animals, male and female, Ka ɗauki bakwai na kowace iri tsabtaccen dabba tare da kai, namiji da ta mace, da kuma biyu na kowace dabba marar tsabta, namiji da ta mace,
3 also seven pairs of sky birds, male and female, to keep offspring alive across all the earth. da kuma bakwai na kowane iri tsuntsu, namiji da ta mace, domin a bar kowane irinsu da rai a dukan duniya.
4 For in seven days I'll rain on the earth forty days and forty nights, and wipe out every living thing I made from the face of the ground." Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.”
5 Noah did everything our Father commanded him. Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi.
6 Noah was 600 years old when the floodwaters came upon the earth. Nuhu yana da shekaru 106 ne sa’ad da aka yi ambaliya ruwa a duniya.
7 He, his sons, his wife, and his sons' wives entered the ark to escape the floodwaters. Nuhu da matarsa da ’ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya.
8 Of clean animals and animals not clean, of birds and all that crawls on the ground. Biyu-biyu daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da tsuntsaye da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa,
9 Two by two, male and female, came to Noah in the ark, as our Father commanded Noah. namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu.
10 After the seven days, the floodwaters came upon the earth. Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya.
11 In Noah's six hundredth year, second month, day seventeen—that same day—all springs of the great deep burst open, and heaven's floodgates opened. A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.
12 The rain fell on the earth for forty days and forty nights. Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in.
13 That day Noah entered the ark—he, his sons Shem, Ham, Japheth, his wife, and his sons' three wives. A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi.
14 They and every wild animal by their kind, every livestock by their kind, every crawler on earth by their kind, every bird by their kind, every winged creature. Tare da su kuwa, akwai kowane naman jeji bisa ga irinsa, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinta, da kowane tsuntsun gida da na jeji bisa ga irinsa, da dukan abu mai fiffike.
15 They came to Noah, into the ark, two by two, all flesh with breath of life. Biyu-biyu na dukan halittu masu numfashi suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi.
16 Male and female of all flesh entered, as our Father commanded him; then our Father shut him in. Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya.
17 The flood lasted forty days on the earth; the waters rose, lifted the ark, floating above the earth. Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya.
18 Waters surged and rose greatly over the earth, and the ark floated on the water's surface. Ruwa ya taso, ya ƙaru ƙwarai a duniya, jirgin kuma ya yi ta yawo a bisa ruwa.
19 Waters rose higher and higher on the earth, covering all the high mountains under the whole sky. Ruwa ya ƙaru ƙwarai a duniya, ya kuma rufe dukan duwatsu masu tsawo a ƙarƙashin sammai.
20 About twenty-two feet deep the waters rose above the mountains, covering them. Ruwan ya taso ya rufe duwatsu, zurfin ruwa daga duwatsun zuwa inda jirgin yake ya fi ƙafa ashirin.
21 Everything moving on earth died: birds, livestock, wild animals, all creatures swarming the earth, and all mankind. Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane.
22 Everything on dry land that had the breath of life in its nostrils died. Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu.
23 Our Father wiped out every living thing on the ground's face—people, animals, crawling creatures, birds of the sky—and wiped them from the earth. Only Noah and those with him in the ark remained. Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.
24 And the waters prevailed over the earth 150 days. Ruwa ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]