Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Genesis 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 This is the written record of Adam's descendants. When our Father created humankind, he made them in the likeness of God. Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.
2 He created them male and female, blessed them, and named them Humankind when they were created. Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”
3 At 130, Adam fathered a son in his likeness, after his image, and named him Seth. Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.
4 After he fathered Seth, Adam lived 800 years and had other sons and daughters. Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
5 Altogether, Adam lived 930 years, and then he died. Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.
6 When Seth had lived 105 years, he fathered Enosh. Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh.
7 After he fathered Enosh, Seth lived 807 years and had other sons and daughters. Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
8 Altogether, Seth lived 912 years, and then he died. Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
9 When Enosh had lived ninety years, he fathered Kenan. Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan.
10 After he fathered Kenan, Enosh lived 815 years and had other sons and daughters. Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
11 Altogether, Enosh lived 905 years, and then he died. Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
12 When Kenan had lived seventy years, he fathered Mahalalel. Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel.
13 After he fathered Mahalalel, Kenan lived 840 years and had other sons and daughters. Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata
14 Altogether, Kenan lived 910 years, and then he died. Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.
15 When Mahalalel had lived sixty-five years, he fathered Jared. Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared.
16 After he fathered Jared, Mahalalel lived 830 years and had other sons and daughters. Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata
17 Altogether, Mahalalel lived 895 years, and then he died. Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.
18 When Jared had lived 162 years, he fathered Enoch. Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok.
19 After he fathered Enoch, Jared lived 800 years and had other sons and daughters. Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
20 Altogether, Jared lived 962 years, and then he died. Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu.
21 When Enoch had lived sixty-five years, he fathered Methuselah. Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela.
22 After fathering Methuselah, Enoch walked with our Father 300 years, and had other sons and daughters. Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
23 Altogether, Enoch lived 365 years. Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365.
24 Enoch walked faithfully with our Father; then he was gone, because our Father took him. Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
25 When Methuselah had lived 187 years, he fathered Lamech. Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek.
26 After he fathered Lamech, Methuselah lived 782 years and had other sons and daughters. Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
27 Altogether, Methuselah lived 969 years, and then he died. Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
28 When Lamech had lived 182 years, he fathered a son. Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa.
29 He named him Noah, saying, "He will comfort us in our work and painful toil of our hands, from the ground our Father cursed." Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”
30 After he fathered Noah, Lamech lived 595 years and had other sons and daughters. Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata.
31 Altogether, Lamech lived 777 years, and then he died. Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu.
32 When Noah was 500 years old, he fathered Shem, Ham, and Japheth. Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]