Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Genesis 45 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Joseph could not control himself before everyone standing by him, so he cried out, "Send everyone away from me!" No one stayed with him when Joseph made himself known to his brothers. Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, “Kowa yă tashi daga gabana!” Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga ’yan’uwansa.
2 He wept so loudly that the Egyptians heard it, and Pharaoh's household heard it. Sai ya yi kuka da ƙarfi har Masarawa suka ji, har labarin ya kai gidan Fir’auna.
3 Joseph said to his brothers, "I am Joseph! Is my father still alive?" His brothers could not answer him, for they were terrified at his presence. Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa.
4 Joseph said to his brothers, "Please, come close to me." They came close. He said, "I am your brother Joseph, whom you sold into Egypt. Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar!
5 Now don't be distressed or angry with yourselves for selling me here, since our Father sent me ahead of you to preserve life. Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka.
6 Famine has been in the land two years now; five more years remain with no plowing or harvest. Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.
7 Our Father sent me ahead of you to preserve a remnant for you on earth, and keep you alive as a great band of survivors. Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma.
8 So now, it wasn't you who sent me here, but our Father—he made me father to Pharaoh, lord of all his household, and ruler over all the land of Egypt. “Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar.
9 Hurry, go up to my father, tell him: Your son Joseph says: Our Father has made me lord of all Egypt. Come down to me; don't delay. Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta.
10 You'll live in Goshen, near me—you, your children, your children's children, your flocks, your herds, all you own. Za ka yi zama a yankin Goshen, ka kasance kusa da ni. Kai, ’ya’yanka da kuma jikokinka, garkunanka da shanunka, da kuma dukan abin da kake da shi.
11 I will provide for you there—five years of famine remain—so you, your household, and all you own don't fall into poverty. Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’
12 Your eyes see, and my brother Benjamin's eyes see, that it is my own mouth speaking to you. “Ku kanku kun gani, haka ma ɗan’uwana Benyamin, cewa tabbatacce ni ne nake magana da ku.
13 Tell my father all my honor in Egypt, and all you have seen. Hurry and bring my father down here. Faɗa wa mahaifina game da dukan girman da aka ba ni a Masar, da kuma game da kome da kuka gani. Ku kuma kawo mahaifina a nan da sauri.”
14 Then he threw his arms around his brother Benjamin and wept, and Benjamin wept on his neck." Sa’an nan ya rungume ɗan’uwansa Benyamin ya yi kuka, sai Benyamin ya rungume shi yana kuka.
15 He kissed all his brothers and wept over them. After that his brothers talked with him. Ya sumbaci dukan ’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai ’yan’uwansa suka yi masa magana.
16 News reached Pharaoh's house: "Joseph's brothers have come." It pleased Pharaoh and his officials. Sa’ad da labarin ya kai fadan Fir’auna cewa ’yan’uwan Yusuf sun zo, sai Fir’auna da dukan hafsoshin suka ji daɗi.
17 Pharaoh said to Joseph, "Say to your brothers: do this—load your animals, go, return to the land of Canaan. Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Faɗa wa ’yan’uwanka, ‘Yi wannan; ku jibge dabbobinku ku koma zuwa ƙasar Kan’ana,
18 Take your father and your households and come to me. I will give you the best of Egypt's land, and you will eat the richness of the land. Ku kawo mahaifinku da iyalanku zuwa wurina. Zan ba ku mafi kyau na ƙasar Masar, za ku kuwa ci moriyar ƙasar.’
19 You are commanded: tell them, 'Do this—take wagons from Egypt for your children and wives, bring your father, and come. “An kuma umarce ka, ka faɗa musu, ‘Ku yi wannan, ku ɗauki wagonu daga Masar domin ’ya’yanku da matanku, ku ɗauki mahaifinku ku zo.
20 Don't worry about your belongings—the best of all Egypt's land is yours.'" Kada ku damu da mallakarku, gama mafi kyau na Masar za su zama naku.’ ”
21 The sons of Israel did so; Joseph gave them wagons per Pharaoh's order, and gave them provisions for the road. Sai ’ya’yan Isra’ila maza suka yi haka. Yusuf ya ba su wagonu kamar yadda Fir’auna ya umarta, ya kuma ba su guzuri don tafiyarsu.
22 He gave each a change of clothes, but Benjamin 300 pieces of silver and five changes of clothes. Ya ba da sababbin riguna ga kowannensu amma ga Benyamin ya ba shi shekel ɗari uku na azurfa da riguna kashi biyar.
23 He sent his father ten donkeys loaded with Egypt's best, and ten female donkeys loaded with grain, bread, and food for his journey. Ga kuma abin da ya aika wa mahaifinsa, jakuna goma da aka jibge da abubuwa mafi kyau na Masar, da jakuna mata guda goma ɗauke da hatsi da burodi da waɗansu tanade-tanade don tafiyarsa.
24 He sent his brothers off; as they left, he said, "Don't quarrel on the way." Sa’an nan ya sallami ’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!”
25 So they left Egypt and came to their father Jacob in Canaan. Saboda haka suka haura, suka fita daga Masar, suka zo wurin maihaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana.
26 They told him, "Joseph is still alive—ruler over all Egypt!" But his heart went numb; he didn't believe them. Suka faɗa masa, “Yusuf yana da rai! Gaskiya, shi ne mai mulkin dukan Masar.” Gaban Yaƙub ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.
27 But when they told him all Joseph's words to them, and he saw the wagons Joseph sent to carry him, their father Jacob's spirit revived. Amma sa’ad da suka faɗa masa kome da Yusuf ya faɗa musu, da kuma sa’ad da ya ga wagonun da Yusuf ya aika don a ɗauke shi a kai da shi can, sai ya farfaɗo, ya dawo cikin hankalinsa.
28 Israel said, "Enough! Joseph my son is still alive. I will go and see him before I die." Sai Yaƙub ya ce, “Na yarda! Ɗana Yusuf yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]