Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Genesis 39 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Joseph was brought down to Egypt; Potiphar, Pharaoh's Egyptian official and captain of the guard, bought him from the Ishmaelites who had brought him down there. To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can.
2 Our Father was with Joseph; he thrived, serving in his Egyptian master's house. Ubangiji kuwa yana tare da Yusuf, Yusuf kuwa yi nasara, ya zauna a gidan mutumin Masar maigidansa.
3 His master saw our Father was with him, our Father making all he did succeed in his hand. Sa’ad da maigidansa ya ga cewa Ubangiji yana tare da Yusuf, kuma cewa Ubangiji ya ba shi nasara a kome da ya yi,
4 Joseph found favor with him and served him; his master put Joseph over his house, entrusting him with all he owned. sai Yusuf ya sami tagomashi a idanunsa, ya kuma zama mai hidimarsa. Fotifar ya sa shi yă zama shugaba a gidansa, ya kuma danƙa masa kome da yake da shi.
5 From when he put Joseph over his house and all he owned, our Father blessed the Egyptian's house for Joseph's sake; our Father's blessing was on all he had, house and field. Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji.
6 Potiphar left all he owned in Joseph's care, aware of nothing except what he ate. Joseph was well-built and handsome. Saboda haka sai ya bar kome a ƙarƙashin kulawar Yusuf, bai dame kansa a wani abu ba sai dai abincin da yake ci. To, fa, Yusuf ƙaƙƙarfa ne, kyakkyawa kuma,
7 After these things, his master's wife cast her eyes on Joseph and said, "Sleep with me." bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!”
8 He refused, telling his master's wife, "Look, with me here, my master oversees nothing in the house; all he owns he has put in my hands. Amma ya ƙi. Ya ce mata, “Ga shi kome yana a ƙarƙashina, don haka ne ma maigidana bai dami kansa da wani abu a cikin gidan nan ba; kome da ya mallaka, ya danƙa ga kulawata.
9 He is no greater in this house than I am; he's held back nothing from me except you, since you are his wife. How could I do this great evil and sin against our Father?" Babu wani da ya fi ni a wannan gida. Maigidana bai hana ni kome ba sai ke, saboda ke matarsa ce. Yaya fa, zan yi irin wannan mugun abu, in yi zunubi wa Allah?”
10 Day after day she spoke to Joseph, but he refused to listen to her, to lie beside her, to be with her. Ko da yake ta yi ta yin wa Yusuf maganar kowace rana, amma ya ƙi yă kwana da ita, ko ma yă zauna da ita.
11 One day Joseph entered the house to do his work, with no household man inside. Wata rana, ya shiga cikin gida don yă yi ayyukansa, ba wani daga cikin bayin gidan da yake ciki.
12 She caught him by his garment, saying, "Sleep with me!" He left it in her hand and fled outside. Sai ta cafke shi a riga, ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya bar rigarsa a hannunta, ya gudu ya fita daga gidan.
13 When she saw that he had left his garment in her hand and fled outside, Sa’ad da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita daga gidan,
14 she called the men of her household and said, "Look—he brought us a Hebrew man to mock us. He came in to me to sleep with me, and I screamed loudly. sai ta kira bayin gidan ta ce musu, “Duba, an kawo mana wannan mutumin Ibraniyawa don yă ci mutuncinmu! Ya zo nan don yă kwana da ni, amma na yi ihu.
15 When he heard me cry out, he left his garment beside me and fled outside. Sa’ad da ya ji na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.”
16 She kept his garment beside her until his master came home." Ta ajiye rigar kusa da ita sai da maigidansa ya dawo gida.
17 She told him the same story: "The Hebrew servant you brought us came to me to mock me. Sa’an nan ta faɗa masa wannan labari, “Mutumin Ibraniyawan, bawan da ka kawo mana, ya zo wurina don yă ci mutuncina.
18 But when I cried out, he left his garment beside me and fled outside." Amma da zarar na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.”
19 When his master heard his wife's words to him—"Your servant did these things to me"—his anger flared. Sa’ad da maigidansa ya ji labarin da matarsa ta faɗa masa cewa, “Ga yadda bawanka ya yi da ni,” sai ya husata.
20 Joseph's master took him and put him in the prison holding the king's prisoners. He stayed there in the prison. Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare ’yan kurkukun sarki. Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku,
21 But our Father was with Joseph, showing him covenant love and favor with the prison warden. Ubangiji ya kasance tare da shi; ya nuna masa alheri, ya kuma sa ya sami tagomashi a idanun mai gadin kurkukun.
22 The prison warden put Joseph in charge of all its prisoners; whatever was done there, he did. Saboda haka mai gadin ya sa Yusuf ya zama shugaban dukan waɗanda aka tsare a kurkukun, Yusuf ne kuma yake lura da dukan abin da ake yi a can.
23 The warden checked nothing in Joseph's care, since our Father was with him—whatever he did, our Father made succeed. Mai gadin ba ya sa kansa game da kome da yake ƙarƙashin kulawar Yusuf, gama Ubangiji yana tare da Yusuf, ya kuma ba shi nasara a cikin dukan abin da ya yi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]