Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Genesis 32 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Jacob went on his way, and the angels of our Father met him. Yaƙub shi ma ya kama hanyarsa, sai mala’ikun Allah suka sadu da shi.
2 Jacob saw them and said, "This is our Father's camp!" He named that place Mahanaim. Sa’ad da Yaƙub ya gan su sai ya ce, “Wannan sansanin Allah ne!” Saboda haka ya kira wannan wuri Mahanayim.
3 Jacob sent messengers ahead of him to Esau his brother in the land of Seir, the territory of Edom. Sai Yaƙub ya aiki manzanni su sha gabansa zuwa wurin ɗan’uwansa Isuwa a ƙasar Seyir, a ƙauyen Edom.
4 He ordered them, "Tell my lord Esau: your servant Jacob says, I've lived with Laban and stayed until now. Ya umarce su, “Ga abin da za ku faɗa wa maigidana Isuwa, ‘Bawanka Yaƙub ya ce, na yi zama tare da Laban na kuwa kasance a can sai yanzu.
5 I own oxen, donkeys, flocks, and servants—male and female. I've sent to inform my lord, to find favor in your eyes." Ina da shanu da jakuna, tumaki da awaki, bayi maza da mata. Yanzu ina aika da wannan saƙo zuwa ga ranka yă daɗe, don in sami tagomashi a idanunka.’ ”
6 The messengers returned to Jacob: "We went to your brother Esau—he's coming to meet you, 400 men with him." Sa’ad da manzannin suka komo wurin Yaƙub, suka ce, “Mun tafi wurin ɗan’uwanka Isuwa, yanzu kuwa yana zuwa ya sadu da kai, da kuma mutum ɗari huɗu tare da shi.”
7 Jacob was very afraid and distressed. He split the people with him, and the flocks, herds, and camels, into two camps, Da tsoro mai yawa da kuma damuwa, Yaƙub ya rarraba mutanen da suke tare da shi ƙungiyoyi biyu, haka ma garkunan tumaki da awaki, da garkunan shanu da raƙuma.
8 thinking, "If Esau reaches one camp and attacks it, the remaining camp will escape." Ya yi tunani, “In Isuwa ya zo ya fāɗa wa ƙungiya ɗaya, sai ƙungiya ɗayan da ta ragu ta tsira.”
9 Then Jacob said, "God of my father Abraham and God of my father Isaac, my Father, who said to me, 'Return to your land and family, so I may treat you well,' Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’
10 I am too small for the least of all the covenant love and faithfulness you have shown your servant, for I crossed this Jordan with only my staff, and now I have become two camps. Ban cancanci dukan alheri da amincin da ka nuna wa bawanka ba. Da sanda kaɗai nake sa’ad da na ƙetare wannan Urdun, amma ga shi yanzu na zama ƙungiyoyi biyu.
11 Rescue me, please, from my brother's hand, from Esau's hand—I fear him: he may come and strike me down, mothers with children. Ka cece ni, ina roƙonka daga hannun ɗan’uwana Isuwa, gama ina tsoro zai zo yă fāɗa mini, yă karkashe mu duka, ’ya’ya da iyaye.
12 But you said, 'I will surely be good to you and make your descendants like the sand of the sea, too many to count.'" Amma ka riga ka faɗa, ‘Tabbatacce zan sa ka yi albarka. Zan kuma sa zuriyarka su zama kamar yashin teku da ba a iya ƙirgawa.’ ”
13 He stayed there that night, then took a gift for his brother Esau from what he had: Ya kwana a can, daga cikin abin da yake tare da shi kuwa, ya zaɓi kyauta domin ɗan’uwansa Isuwa,
14 200 female goats and twenty male goats, 200 ewes and twenty rams, awaki ɗari biyu da bunsurai ashirin, tumaki ɗari biyu da raguna ashirin,
15 thirty nursing camels with their young, forty cows, ten bulls, twenty female donkeys, ten male donkeys. raƙuma mata talatin tare da ƙananansu, shanu arba’in da bijimai goma, jakuna mata ashirin da kuma jakuna maza goma.
16 He gave them to his servants, drove by drove, separately, and told his servants, "Pass ahead of me, and leave space between drove and drove." Ya sa su a ƙarƙashin kulawar bayinsa, kowane kashin garke ya kasance a ware. Ya ce wa bayinsa, “Ku sha gabana, ku kuma ba da rata tsakanin garke da garke.”
17 He ordered the first, "When Esau my brother meets you and asks you, 'Whose are you? Where are you going? Whose are these ahead of you?' Ya umarci wanda yake jagorar ya ce, “Sa’ad da ɗan’uwana Isuwa ya sadu da ku ya kuma yi tambaya, ‘Ku na wane ne, ina za ku, kuma wane ne mai dukan dabbobin nan da suke gabanku?’
18 then say, 'They're your servant Jacob's, a gift sent to my lord Esau. Look, he himself is behind us.'" Sai ku ce, ‘Na bawanka Yaƙub ne. Kyauta ce wa maigidana Isuwa, yana kuma tafe a bayanmu.’ ”
19 He also commanded the second, the third, and all who followed the herds, "Say the same to Esau when you find him, Yaƙub ya kuma umarci na biyu da na uku da kuma dukan waɗansu da suka bi garkunan, “Sai ku faɗa irin abu guda ga Isuwa sa’ad da kuka sadu da shi.
20 and you will say, 'Also, your servant Jacob is behind us.'" For he thought, "I will appease him with the gift ahead of me, then see his face; perhaps he'll accept me." Ku kuma tabbata kun ce, ‘Bawanka Yaƙub yana tafe a bayanmu.’ ” Gama Yaƙub ya yi tunani cewa, “Zan kwantar da ran Isuwa da waɗannan kyautai, kafin mu sadu fuska da fuska, wataƙila yă karɓe shi.”
21 So the gift passed on ahead of him, and he himself stayed that night in the camp. Saboda haka kyautai Yaƙub suka sha gabansa, amma shi kansa ya kwana a sansani.
22 That night he got up, took his two wives, two female servants, and eleven sons, and crossed the Jabbok ford. A wannan dare Yaƙub ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansa goma sha ɗaya ya haye rafin Yabbok.
23 He took them and sent them across the stream, and likewise sent across everything he had. Bayan ya sa suka haye rafin, haka ma ya tura dukan mallakarsa zuwa hayen.
24 And Jacob was left alone. And a man wrestled with him until the breaking of the day. Saboda haka sai aka bar Yaƙub shi kaɗai. Sai ga wani mutum ya zo ya yi kokawa da shi har wayewar gari.
25 Seeing he could not defeat Jacob, the man touched his hip socket, and Jacob's hip was wrenched as they wrestled. Da mutumin ya ga cewa bai fi ƙarfin Yaƙub ba, sai ya bugi kwarin ƙashin cinyar Yaƙub, sai gaɓar ƙashin cinyarsa ya goce, a sa’ad da yake kokawa da mutumin.
26 He said, "Let me go; dawn is breaking." But Jacob said, "I won't let you go unless you bless me." Sa’an nan mutumin ya ce, “Bar ni in tafi, gama gari ya waye.” Amma Yaƙub ya amsa ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”
27 And he said to him, "What is your name?" And he said, "Jacob." Mutumin ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Yaƙub.”
28 He said, "You will no longer be named Jacob, but Israel, for you have struggled with our Father and with men, and won." Sai mutumin ya ce, “Sunanka ba zai ƙara zama Yaƙub ba, amma Isra’ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”
29 Jacob asked him, "Please tell me your name." He said, "Why do you ask my name?" And he blessed him there. Yaƙub ya ce, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.” Amma mutumin ya amsa ya ce, “Me ya sa kake tambayata sunana?” Sa’an nan ya albarkace shi.
30 So Jacob named the place Peniel: "For I have seen our Father face to face, yet my life was saved." Saboda haka Yaƙub ya kira wurin Feniyel, yana cewa, “Domin na ga Allah fuska da fuska, duk da haka aka bar ni da rai.”
31 The sun rose upon him as he passed Penuel, limping because of his hip. Rana ta yi sama a sa’ad da ya wuce Fenuwel yana kuma ɗingishi saboda ƙashin cinyarsa.
32 This is why, even now, the Israelites won't eat the thigh muscle on the hip socket—because he struck Jacob's hip socket there, at the thigh muscle. Wannan ya sa har wa yau Isra’ilawa ba sa cin jijiyar ƙashin cinya wadda take a kwarin ƙashin cinya, domin an taɓa kwarin ƙashin cinyar Yaƙub kusa da jijiyar.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]