Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In Jehoiakim king of Judah's third year, Nebuchadnezzar king of Babylon marched on Jerusalem and besieged it. A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya.
2 The Sovereign Father handed Jehoiakim king of Judah over to him, with some items from our Father's house; he took them to Shinar, to his god's house, and the items into his god's treasury. Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon cikin ma’ajin gidan allahnsa.
3 The king ordered Ashpenaz, his chief official, to bring some Israelites from the royal family and nobility. Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane.
4 Young men without defect, good-looking, skilled in all wisdom, well-informed, quick to understand, fit to stand in the king's palace—and to teach them Babylonian writing and language. Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu.
5 The king assigned them a daily portion of his food and wine, three years' training, then service before him. Sarki kuma ya sa a ba su abinci da ruwan inabi kowace rana daga cikin abincin sarki. Za a koyar da su har shekaru uku, bayan haka kuma su shiga yin wa sarki hidima.
6 Among them were Daniel, Hananiah, Mishael, and Azariah, from the sons of Judah. Daga cikin waɗannan da aka zaɓa akwai waɗansu daga Yahuda, Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya.
7 The chief official renamed them: Daniel, Belteshazzar; Hananiah, Shadrach; Mishael, Meshach; Azariah, Abednego. Sai sarkin fada ya raɗa musu sababbin sunaye, ga Daniyel ya raɗa masa Belteshazar; ga Hananiya ya raɗa masa Shadrak; ga Mishayel ya raɗa masa Meshak; ga Azariya kuma ya raɗa masa Abednego.
8 Daniel resolved not to make himself unclean with the king's food or wine, so he asked the chief official's permission not to make himself unclean. Amma Daniyel ya ƙudura a zuciyarsa ba zai ƙazantar da kansa da abinci da ruwan inabin sarki ba, sai ya tambayi sarkin fada don a ba shi izinin kada yă ƙazantar da kansa ta wannan hanya.
9 Now our Father gave Daniel favor and compassion in the eyes of the chief official. Sai Allah ya sa sarkin fada ya nuna masa tagomashi ya kuma ƙaunaci Daniyel,
10 The chief official told Daniel, "I fear my lord the king, who set your food and drink. Why should he see your faces worse than boys your age? You'd forfeit my head to the king." amma sai sarkin fada ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoron ranka yă daɗe, sarkina wanda ya sa a ba ku abinci da ruwan inabi. Me zai sa yă ga kuna ramewa fiye da sauran samari, tsaranku? Sarki zai sa a fille mini kai saboda ku.”
11 Then Daniel said to the steward the chief official had appointed over Daniel, Hananiah, Mishael, and Azariah, Sai Daniyel ya ce wa mai gadi wanda sarkin fada ya sa yă kula da Daniyel, Hananiya, Mishayel da Azariya,
12 "Please test your servants for ten days. Give us only vegetables to eat and water to drink. “Ina roƙonka ka gwada bayinka kwana goma. Kada ka ba mu kome sai kayan lambu mu ci da kuma baƙin ruwa mu sha.
13 Then compare our appearance with the youths eating the king's food; do with your servants as you see." Sa’an nan sai ka dubi fuskokinmu da na sauran samarin da suke ci daga abincin sarki; sa’an nan ka yi da bayinka bisa ga abin da ka gani.”
14 So he agreed to this and tested them for ten days. Sai ya amince da haka ya kuma gwada su har kwana goma.
15 After ten days they looked healthier and better fed than all the young men eating the royal food. A ƙarshen kwana goma sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki.
16 So the steward took away their assigned food and the wine they were to drink, and gave them vegetables instead. Sai mai gadinsu ya janye abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu.
17 To these four boys our Father gave knowledge and insight in all writing and wisdom; Daniel understood all visions and dreams. Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.
18 When the king's set days for bringing them in ended, the chief official brought them before Nebuchadnezzar. A ƙarshen lokacin da sarki ya sa da za a kawo su ciki, sai sarkin fada ya gabatar da su ga Nebukadnezzar.
19 The king spoke with them, and none matched Daniel, Hananiah, Mishael, and Azariah; so they served the king. Sarki kuwa ya yi magana da su, sai ya gano cewa babu wani kamar Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya; don haka sai suka shiga yi wa sarki hidima.
20 Whenever the king questioned them on wisdom and understanding, he found them ten times better than all magicians and enchanters in his whole kingdom. A dukan al’amuran hikima da na fahimta wanda sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa sau goma.
21 And Daniel remained there until the first year of King Cyrus. Daniyel kuwa ya kasance a nan har shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]