Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Acts 17 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 After traveling through Amphipolis and Apollonia, they came to Thessalonica, where there was a Jewish synagogue. Da suka bi ta Amfifolis da Afolloniya, sai suka isa Tessalonika, inda akwai majami’ar Yahudawa.
2 Paul, as usual, went in to them and reasoned with them from the Scriptures on three Sabbaths. Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majami’ar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi,
3 Opening and explaining the Scriptures that the Christ must suffer and rise from the dead, he said, "This Jesus I proclaim to you is the Christ." yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesu da nake sanar muku shi ne Kiristi.”
4 Some of them were persuaded and joined Paul and Silas, along with a great many devout Greeks and quite a few leading women. Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Hellenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba.
5 But the Jews grew jealous, gathered evil men from the marketplace, formed a mob, and threw the city into chaos. They stormed Jason's house, seeking to bring them out to the crowd. Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ’yan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka tā da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron.
6 Not finding them, they dragged Jason and some brothers before the city officials, shouting, "These men who have turned the world upside down have come here too, Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ’yan’uwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa, “Waɗannan mutanen da suke tā da fitina ko’ina a duniya sun iso nan,
7 Jason welcomed them. They all defy Caesar's decrees, claiming there is another king—Jesus. Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.”
8 And they stirred up the crowd and the city authorities who heard these things." Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi.
9 And when they had taken bail from Jason and the rest, they let them go. Sai suka sa Yason da sauran su biya kuɗin saki sa’an nan suka sallame su.
10 The brothers at once sent Paul and Silas off by night to Berea; on arrival they went to the Jewish synagogue. Da dare ya yi, sai ’yan’uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Bereya. Da suka isa can, sai suka shiga majami’ar Yahudawa.
11 These Jews were more open-minded than those in Thessalonica, receiving the word eagerly and examining Scripture daily to see if these things were true. Bereyawa kuwa sun fi Tessalonikawa hankali, gama sun karɓi saƙon da marmari ƙwarai, suka kuma yi ta yin bincike Nassosi kowace rana su ga ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne.
12 So many of them believed, along with many prominent Greek women and men. Yahudawa da yawa suka gaskata, haka ma waɗansu manyan matan Hellenawa da kuma mazan Hellenawa da yawa.
13 When Jews from Thessalonica learned Paul proclaimed the word of our Father in Berea too, they went there also, agitating and stirring up the crowds. Da Yahudawan da suke a Tessalonika suka ji cewa Bulus yana wa’azin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma tā da hankalinsu.
14 The brothers immediately sent Paul off to the sea, but Silas and Timothy stayed there. Nan da nan ’yan’uwa suka sa Bulus yă tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya.
15 Paul's escorts brought him to Athens, then left with orders for Silas and Timothy to join him as soon as possible. Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens sa’an nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa.
16 While Paul waited for them in Athens, his spirit was provoked within him, seeing the city full of idols. Yayinda Bulus yake jiransu a Atens, ya damu ƙwarai da ya ga birnin cike da gumaka.
17 So he debated in the synagogue with Jews and worshipers of God, and daily in the marketplace with whoever was there. Saboda haka ya yi ta muhawwara a majami’a da Yahudawa da kuma Hellenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.
18 Some of the Epicurean and Stoic philosophers also debated with him. Some asked, "What's this babbler trying to say?" Others said, "He seems to promote foreign gods"—since he preached the good news of Jesus and the resurrection. Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.
19 They took him and brought him to the Areopagus, asking, "Can we know what this new teaching you're presenting is? Sai suka ɗauke shi suka kawo shi wurin taron Areyofagus, inda suka ce masa, “Ko za mu san mene ne sabon koyarwan nan ya ƙunsa da kake yi?
20 For you bring strange things to our ears, so we want to know what they mean." Kana kawo mana ra’ayoyin da suke baƙo a gare mu, kuma muna so mu san mene ne suke nufi.”
21 Now all the Athenians and foreigners living there spent their time on nothing but telling or hearing something new. (Duk Atenawa da baƙin da suke zama a can suna zaman kashe wando ne kawai kuma ba abin da suke yi sai dai taɗi da kuma jin sababbin ra’ayoyi.)
22 Paul stood in the middle of the Areopagus and said, "Athenians, I see that you are extremely religious in every way. Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce, “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai.
23 For as I passed through and examined your sacred objects, I found an altar inscribed: 'To an unknown god.' What you worship without knowing it, I now proclaim to you. Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu, Ga Allahn da ba a sani ba. To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.
24 Our Father, who made the world and everything in it, being Sovereign of heaven and earth, doesn't live in temples made by hands, “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa.
25 nor served by human hands, as if he needed anything—he himself gives everyone life, breath, and everything. Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome.
26 From one man he made every nation of mankind live across the whole earth, fixing their set times and the boundaries of their homelands, Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance.
27 so they might seek our Father, perhaps reach for him and find him—though he is not far from each of us, Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu.
28 for 'In him we live and move and have our being'; as even some of your own poets have said, 'We too are his descendants.' ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’
29 So as our Father's children, we shouldn't think the divine is like gold, silver, or stone—an image shaped by human skill and imagination. “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa.
30 The times of ignorance our Father overlooked, but now he commands all people everywhere to repent. A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba.
31 He set a day to judge the world justly, through a man he appointed—proving it to all by raising him from the dead." Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.”
32 Hearing of the resurrection of the dead, some mocked; others said, "We'll hear you on this again." Sa’ad da suka ji maganar tashin matattu, waɗansunsu suka yi tsaki, amma waɗansu suka ce, “Muna so mu ƙara jin ka a kan wannan batu.”
33 So Paul left them. Da wannan, Bulus ya bar Majalisar.
34 But some men joined him and believed, including Dionysius the Areopagite, a woman named Damaris, and others. Waɗansu mutane kima suka zama mabiyan Bulus suka kuwa gaskata. A cikinsu kuwa akwai Diyonasiyus ɗan Majalisar Areyofagus, haka kuma wata mace mai suna Damaris, da waɗansu dai haka.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]