Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Samuel 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The war between Saul's house and the house of David dragged on a long time. David grew steadily stronger, while Saul's house grew weaker and weaker. Aka daɗe ana yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda. Dawuda kuwa ya yi ta ƙara ƙarfi, yayinda gidan Shawulu ya yi ta raguwa a ƙarfi.
2 Sons were born to David in Hebron. His firstborn was Amnon, whose mother was Ahinoam of Jezreel; An haifa wa Dawuda ’ya’ya maza a Hebron. Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;
3 his second, Chileab, by Abigail, Nabal of Carmel's widow; the third, Absalom, son of Maacah, daughter of Talmai king of Geshur; na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur;
4 the fourth, Adonijah son of Haggith; the fifth, Shephatiah son of Abital; na huɗu shi ne Adoniya, ɗan Haggit; na biyar shi ne Shefatiya, ɗan Abital;
5 and the sixth, Ithream, by David's wife Eglah. These were David's sons born in Hebron. na shida kuma shi ne Itireyam, ɗan Egla matar Dawuda. An haifi waɗannan wa Dawuda a Hebron.
6 During the war between the house of Saul and the house of David, Abner kept strengthening his position in Saul's house. Sa’ad da ake yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda, sai Abner ya yi ta ƙarfafa matsayinsa a gidan Shawulu.
7 Saul had a concubine named Rizpah, daughter of Aiah. Ish-bosheth said to Abner, "Why did you sleep with my father's concubine?" To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa, ’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?”
8 Abner, very angry at Ish-bosheth's words, said, "Am I a dog's head loyal to Judah? Today I keep showing loyalty to your father Saul's house, his brothers and friends, and haven't handed you to David. Yet now you charge me over this woman! Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina?
9 May our Father do the same to Abner, and more, if I do not do for David what our Father swore to him, Allah yă yi wa Abner hukunci mai tsanani, in ban goyi bayan Dawuda ya sami abin da Ubangiji ya yi masa alkawari da rantsuwa ba.
10 to transfer the kingdom from Saul's house and set up David's throne over Israel and over Judah, from Dan to Beersheba." Zan kuma mayar wa Dawuda sarautar gidan Shawulu, in kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila, da kan Yahuda tun daga Dan har zuwa Beyersheba.”
11 And Ish-bosheth could not say another word to Abner, because he was afraid of him. Ish-Boshet bai ƙara yin karambanin ce wa Abner kome ba, gama yana tsoronsa.
12 Abner sent messengers to David on his behalf: "Whose is the land? Make your covenant with me, and my hand will be with you to bring all Israel over to you." Sai Abner ya aiki manzanni a madadinsa wurin Dawuda su ce masa, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi yarjejjeniya da ni, zan kuwa taimake ka, in juye dukan Isra’ila zuwa ɓangarenka.”
13 David said, "Good; I'll make a covenant with you. But I require one thing: you won't see my face unless you first bring Michal, Saul's daughter, when you come." Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”
14 David sent messengers to Ish-bosheth, Saul's son: "Give me my wife Michal, whom I betrothed to me for one hundred Philistine foreskins." Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”
15 So Ish-bosheth sent and took her from her husband, Paltiel son of Laish. Sai Ish-Boshet ya ba da umarni, aka kuwa ɗauke ta daga gidan mijinta Faltiyel ɗan Layish.
16 Her husband went with her, weeping as he followed her to Bahurim. Then Abner told him, "Go back." So he returned. Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma.
17 Abner spoke with Israel's elders: "You've long wanted David as king over you. Abner ya tattauna da dattawan Isra’ila ya ce, “An daɗe kuna nema ku naɗa Dawuda sarkinku.
18 Now act, for our Father promised David: 'By my servant David's hand I will save my people Israel from the Philistines and all their enemies.'" To, yanzu sai ku yi haka! Gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta wurin bawana Dawuda zan ceci mutanena Isra’ila daga hannun Filistiyawa, da kuma hannun dukan abokan gābansu.’ ”
19 Abner also spoke to Benjamin, then went to Hebron to tell David all that Israel and the whole house of Benjamin had agreed to do. Abner kuma ya yi magana da mutane Benyamin da kansa. Sa’an nan ya tafi Hebron yă gaya wa Dawuda ko mene ne Isra’ila da kuma dukan gidan Benyamin suke so su yi.
20 When Abner came to David at Hebron with twenty men, David held a feast for Abner and his men. Sa’ad da Abner wanda yake tare da mutane ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda ya shirya masa liyafa tare da mutanensa.
21 Abner told David, "Let me go gather all Israel to my lord the king, so they make a covenant with you and you reign over all your heart desires." So David sent Abner off, and he left in peace. Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Bari in tafi nan da nan in tattara dukan Isra’ila wa ranka yă daɗe, sarki, saboda su yi alkawari da kai, ka kuma ka yi mulki bisa dukansu yadda ranka yake so.” Saboda haka Dawuda ya sallami Abner, ya kuwa tafi lafiya.
22 Just then David's servants and Joab returned from a raid with much plunder. But Abner was not with David at Hebron, for David had sent him away, and he had gone in peace. Ba a jima ba sai mutanen Dawuda da Yowab suka dawo daga hari. Suka kawo ganima da yawa tare da su. Abner kuwa ya riga ya bar Dawuda a Hebron, domin Dawuda ya sallame shi, shi kuma ya tafi lafiya.
23 When Joab and all his army arrived, he was told, "Abner son of Ner came to the king, who sent him off, and he left in peace." Sa’ad da Yowab da dukan sojoji suka dawo, aka gaya masa cewa Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya sallame shi, ya kuma tafi lafiya.
24 So Joab went to the king: "What have you done? Abner came to you—why did you send him off, and now he's gone? Sai Yowab ya je wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka. Don me ka ƙyale shi yă tafi? Ga shi kuwa ya tafi!
25 You know Abner son of Ner came to deceive you, to learn your movements and everything you're doing." Ka san Abner ɗan Ner ya zo ne yă ruɗe ka, yă ga fitarka da shigarka, yă kuma binciki kome da kake yi.”
26 When Joab left David, he sent messengers after Abner, who brought him back from the well of Sirah. But David knew nothing. Yowab ya tashi daga gaban Dawuda ya tafi ya aika manzanni su bi Abner. Suka same shi a rijiyar Sira suka komo da shi, Dawuda kuwa bai sani ba.
27 When Abner returned to Hebron, Joab pulled him aside inside the gate as if to speak privately, and there stabbed him in the stomach. He died—for the blood of Joab's brother Asahel. To, da Abner ya komo Hebron, Yowab ya ratse da shi zuwa hanyar shigar gari kamar zai gana da shi a kaɗaice. Amma a can ya soki Abner a ciki, ya kashe shi don yă rama mutuwar ɗan’uwansa Asahel.
28 Later, when David heard, he said, "I and my kingdom are forever innocent before our Father of the blood of Abner son of Ner. Daga baya, Dawuda ya ji labarin sai ya ce, “Ni da masarautata har abada ba mu da laifi a gaban Ubangiji game da jinin Abner ɗan Ner.
29 May it fall on Joab's head and all his father's house! May Joab's house never lack someone with a discharge or skin disease, who leans on a crutch, falls by the sword, or lacks food." Alhakin jininsa yă kasance a kan Yowab da kuma a kan dukan iyalin mahaifinsa! Kada gidan Yowab yă rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko mai jingina ga sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko kuma wanda ba shi da abinci.”
30 So Joab and his brother Abishai killed Abner for killing their brother Asahel in the battle at Gibeon. (Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner don yă kashe ɗan’uwansu Asahel a yaƙin Gibeyon.)
31 David told Joab and all the people with him, "Tear your clothes, put on sackcloth, and mourn before Abner." King David walked behind the bier. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya.
32 They buried Abner in Hebron, and the king wept aloud at his grave, and all the people wept. Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner.
33 The king sang this lament for Abner: "Should Abner have died as a fool dies? Sarki ya kuma yi wannan waƙar makoki domin Abner ya ce, “Daidai ne Abner yă mutu, kamar yadda marasa bin doka suke mutuwa?
34 Your hands were not bound, your feet not set in chains. You fell as one falls before the wicked." And all the people wept over him again. Hannuwanka ba a daure suke ba, ƙafafunka ba a tabaibaye suke ba. Ka mutu kamar waɗanda suke mutuwa a hannun mugaye.” Sai dukan mutane suka sāke fashe da kuka saboda shi.
35 Then all the people came to urge David to eat something while it was still day, but David swore: "May our Father do so to me, and worse, if I taste bread or anything else before sunset!" Sa’an nan duk suka zo suka roƙi Dawuda yă ci wani abu tun rana ba tă fāɗi ba; amma Dawuda ya rantse ya ce, “Bari Allah yă hukunta ni, in na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta fāɗi!”
36 All the people noticed and were pleased; everything the king did pleased all the people. Dukan mutane suka lura suka kuma ji daɗi ƙwarai, tabbatacce kome da sarki ya yi, ya gamshe su.
37 So that day all the people and all Israel knew the king had not willed the death of Abner son of Ner. Saboda haka a ranar dukan mutane da dukan Isra’ila suka gane sarki ba shi da hannu a kisan Abner ɗan Ner.
38 The king told his servants, "Don't you know a prince and a great man has fallen today in Israel? Sa’an nan sarki ya ce wa mutanensa, “Ba ku gane cewa ɗan sarki kuma babban mutum ya mutu a ƙasar Isra’ila a yau ba?
39 Today, though the anointed king, I am weak, and these men, Zeruiah's sons, are too hard for me. May our Father repay the one who does evil for his evil." A yau, ko da yake ni naɗaɗɗen sarki ne, duk da haka na raunana, kuma waɗannan ’ya’yan Zeruhiya sun fi ƙarfina. Ubangiji yă sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata!”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]