Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 35 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Josiah kept Passover to our Father in Jerusalem; they slaughtered the Passover lamb on the fourteenth day of the first month. Yosiya ya yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima, aka kuma yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a ranar goma sha huɗu ga wata na farko.
2 He assigned priests their duties and encouraged them in service of our Father's house. Ya zaɓi firistoci su yi aikinsu, sai ya ƙarfafa su su yi aikin da kyau a hidimar haikalin Ubangiji.
3 He told the Levites who taught all Israel and were holy to our Father: "Put the holy ark in the house Solomon son of David, king of Israel, built. You need no longer carry it on your shoulders. Now serve your Father and his people Israel. Ya ce wa Lawiyawa waɗanda suke koyar da dukan Isra’ila da kuma waɗanda aka tsarkake wa Ubangiji. “Ku sa akwatin alkawari mai tsarki a cikin haikalin da Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila ya gina. Ba za a riƙa ɗaukansa a kafaɗa ba. Yanzu ku bauta wa Ubangiji Allahnku da kuma mutanensa Isra’ila.
4 Prepare yourselves by your fathers' houses, by your divisions, by David king of Israel's written instructions, and his son Solomon's instructions. Ku shirya kanku iyali-iyali a sassanku, bisa ga umarnan da Dawuda sarkin Isra’ila da kuma ɗansa Solomon suka rubuta.
5 Stand in the holy place by family groups of your lay brothers, one Levite division per group. “Ku tsaya a tsattsarkan wuri, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin ’yan’uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa.
6 Slaughter the Passover lamb, dedicate yourselves, and prepare for your brothers, following the word of our Father through Moses." Ku yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku kuma shirya raguna domin ’yan’uwanku, kuna yin abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.”
7 Josiah gave the lay people 30,000 lambs and young goats, 3,000 bulls, for Passover offerings—for everyone present, from his own possessions. Yosiya ya tanada wa dukan mutanen da ba firistoci ba ne waɗanda suke a wurin, tumaki da awaki dubu talatin don a yanka saboda hadayun Bikin Ƙetarewa, ya kuma ba su shanu dubu uku. Dukan dabbobin kuwa daga garken sarki ne.
8 His officials also gave willingly to the people, priests, and Levites. Hilkiah, Zechariah, and Jehiel, chief officers of our Father's house, gave the priests 2,600 Passover offerings and 300 bulls. Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku.
9 Conaniah, with his brothers Shemaiah and Nethanel, and Hashabiah, Jeiel, and Jozabad, Levite leaders, gave the Levites 5,000 Passover offerings and 500 bulls. Haka kuma Konaniya tare da Shemahiya da Netanel, ɗan’uwansa, da Hashabiya, Yehiyel da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, suka tanadar da hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyar da kuma bijimai ɗari biyar domin Lawiyawa.
10 The service was set; priests stood at their posts, Levites by their divisions, as the king commanded. Sa’ad da aka shirya kome don Bikin Ƙetarewar, sai Firistoci tare da Lawiyawa suka tsaya wurin tsayawarsu bisa ga umarnin sarki.
11 They slaughtered the Passover lambs; priests sprinkled the blood passed to them, and Levites skinned them. Aka yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, firistoci kuma suka yayyafa jinin da aka ba su, yayinda Lawiyawa suna fiɗan dabbobi.
12 They set aside the burnt offerings, distributing them by family division among the common people, to offer to our Father as written in the book of Moses; likewise with the bulls. Suka keɓe hadayun ƙonawa don su ba da su ga ƙungiyoyin iyalan mutane don su miƙa ga Ubangiji, yadda yake a rubuce a Littafin Musa. Suka yi haka da shanun.
13 They roasted the Passover lamb in fire as required, boiled the holy offerings in pots, kettles, and pans, and quickly brought them to all the common people. Suka gasa dabbobin Bikin Ƙetarewa a bisa wuta yadda aka tsara, suka dafa hadayu masu tsarki a tukwane, da manyan tukwane, da kuma kwanoni, suka raba su nan da nan ga dukan mutane.
14 Afterward they prepared for themselves and the priests, since the priests, Aaron's sons, were busy offering burnt offerings and fat portions until night; so the Levites prepared for themselves and the priests, Aaron's sons. Bayan wannan, suka shirya wa kansu da kuma wa firistoci, saboda firistoci, zuriyar Haruna, suna miƙa hadayun ƙonawa da sashen kitse daga safe har dare. Saboda haka Lawiyawa suka shirya wa kansu da kuma wa firistocin daga zuriyar Haruna.
15 The singers, Asaph's sons, stood at their posts as David, Asaph, Heman, and Jeduthun the king's seer had commanded. The gatekeepers stayed at each gate; they had no need to leave their duty, for their fellow Levites prepared for them. Mawaƙa zuriyar Asaf, suna a wuraren da Dawuda, Asaf, Heman da Yedutun mai duba na sarki suka tsara. Bai zama lalle matsaran ƙofofi a kowace ƙofa su bar wuraren aikinsu ba, domin ’yan’uwansu Lawiyawa sun yi shiri dominsu.
16 So all the service of our Father was arranged that day: to keep Passover and offer burnt offerings on the altar of our Father, by King Josiah's command. Ta haka fa aka yi dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Bikin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda sarki Yosiya ya umarta.
17 The Israelites present kept Passover then, and the Feast of Unleavened Bread seven days. Isra’ilawan da suka kasance a can suka yi Bikin Ƙetarewa a wannan rana, suka kuma kiyaye Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai.
18 No Passover like it had been kept in Israel since Samuel the prophet's days; none of Israel's kings kept a Passover like Josiah's, with the priests, Levites, all Judah and Israel present, and Jerusalem's residents. Ba a taɓa yin Bikin Ƙetarewa haka ba tun zamanin annabi Sama’ila; kuma babu sarkin Isra’ilan da ya taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya yi, tare da firistoci, Lawiyawa da kuma dukan Yahuda da Isra’ila, waɗanda suke can tare da mutanen Urushalima.
19 This Passover was kept in the eighteenth year of Josiah's reign. An yi wannan Bikin Ƙetarewa a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya.
20 After all this, once Josiah had prepared the temple, Egypt's king Neco marched up to fight at Carchemish on the Euphrates, and Josiah went out to meet him. Bayan wannan duka, sa’ad da Yosiya ya shirya haikali, Neko sarkin Masar ya haura don yă yi yaƙi a Karkemish a Yuferites, sai Yosiya ya fita don yă fafata da shi a yaƙi.
21 But Neco sent messengers to him, saying, "What do we have to do with each other, king of Judah? I'm not coming against you today, but against the house I'm at war with. God told me to hurry—stop opposing God, who is with me, or he'll destroy you." Amma Neko ya aiki ’yan saƙo ga Yosiya, yana cewa, “Me ya gama ni da kai, ya Sarkin Yahuda? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da gidan da yake gāba da ni! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada yă hallaka ka.”
22 Josiah did not turn away from him, but disguised himself to fight him. He ignored Neco's words from the mouth of our Father, and went to fight in the plain of Megiddo. Yosiya fa, bai juya daga gare shi ba, amma ya ɓad da kama don yă yi yaƙin. Bai saurari abin da Neko ya faɗa bisa ga umarnin Allah ba, amma ya tafi ya yaƙe shi a filin Megiddo.
23 Archers shot King Josiah; he told his servants, "Get me out—I'm badly wounded." Maharba suka harbi Yosiya, sai ya ce wa hafsoshinsa, “Ku ɗauke ni ku fita da ni daga nan; gama an yi mini mummunan rauni.”
24 His servants moved him from the chariot to his second chariot and brought him to Jerusalem, where he died and was buried in his fathers' tombs. All Judah and Jerusalem mourned Josiah. Saboda haka suka ɗauke shi a keken yaƙin, suka fitar da shi, suka sa shi a wata keken yaƙin da yake da shi, suka kawo shi Urushalima, inda ya mutu. Aka binne shi a makabartar kakanninsa, sai dukan Yahuda da Urushalima suka yi makoki dominsa.
25 Jeremiah composed laments for Josiah, and to this day all the singers, men and women, sing laments for Josiah. This became a custom in Israel, and it is written in the Laments. Annabin Irmiya ya tsara waƙoƙin makoki domin Yosiya, wanda har wa yau mawaƙa maza da mata suke rera game da Yosiya. Suka sa waɗannan su zama al’ada a Isra’ila, suna kuma a rubuce cikin Littafin Makoki.
26 The rest of Josiah's acts, and his faithful deeds in keeping with what is written in our Father's law. Sauran ayyukan mulkin Yosiya da kuma kyawawan abubuwan da ya yi, bisa ga abin da aka rubuta a Dokar Ubangiji,
27 His acts, first to last, are written in the Book of the Kings of Israel and Judah. dukan ayyukan, daga farko har zuwa ƙarshe, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]